Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 5
A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka: An samu gagarumin ci gaba -Farfesa Yakasai […]
A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
An samu gagarumin ci gaba -Farfesa Yakasai
Farfesa Salisu Ahmad Yakasai: “Ni a ra’ayina, an samu gagarumin ci gaba, don ana gane ci gaba ne ga yadda aka auna ma’unin jagora ga mika walwalar jama’a ta hanyar fadin ra’ayinsu. Mutane na fadin albarkacin bakinsu a gwamnatin siyasa, sabanin ta soja, wannan ci gaba ne. Mutane sun cika hanzari, shi ne ya sa wasu idanunsu suka rufe. Wannan abu ne mai sauki, in kana son ka gane an samu ci gaba ka auna sauran kasashe ire-irenmu, wadadanda muke da arziki guda da su ka gani, ba wai ka rika kwatanta mu da Amurka da Ingila ba, wadanda sun shiga halin da muke ciki kafin su zama yadda suke yanzu. Garaje ne ya yi mana yawa, ci gaba kadan-kadan ne yake zuwa. Ba abin da muka samu dari bisa dari, tun daga ilmi, siyasa, tattalin arziki da kayan more rayuwa, gwargwadodai an samu.