Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 6

A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka: Ci baya aka samu – Abubakar Kilgori […]

Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 6
Shekara 14 na dimokuradiyya a Najeriya: Nasara ko asara? 6

A makon da ya gabata ne aka yi bikin cikar Najeriya shekara 14 da tafiyar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin nasara aka samu ko kuwa akasinta? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban kuma sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:

Ci baya aka samu – Abubakar Kilgori

Abubakar Usman Kilgori: “A gaskiya ci baya kawai aka samu a duk shekarun da aka kwashe ana siyasa a kasar nan, bayan duk abin da aka yi alkawari ba a samar da shi ba sai kawai aka kwace wanda aka same mu da shi. Idan ka dubi fannin lafiya, duk kwararrun ma’aikatan da muke da su kafin siyasa sun bar kasar nan kuma ba kwararri a yanzu, ilmi a kullum tabarbarewa yake, musamman a nan Sakkwato, ruwan sha babu ingantacce; sabanin inda aka fito. Kai komai ka bi ta bangarensa sai ka samu ci baya.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50