Shekara 18 aikin Asibitin Sabuwar Kaduna na tafiyar hawainiya

Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu kamarsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara.

Shekara 18 aikin Asibitin Sabuwar Kaduna na tafiyar hawainiya

Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba.

Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara.

Sau hudu gwamnonin jihar daban-daban suna sa wa’adin kammalawa da kaddamar da wannan katafaren asibiti, ba tare da haka ba ta cimma uwa ba.

A shekarar 2007 tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Namadi Sambo tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci na Duniya suka assasa aikin ginin asibitin da wa’adin kammala shi a cikin shekara biyar, wato 2012.

An yi fatan zai kasance Asibitin Koyarwa ga daliban da ke karatun aikin likitanci a Jami’ar Jihar Kaduna. Ga mazauna yankin Sabuwar Kaduna da ke Karamar Hukumar Chikun da kewaye kuwa, suna ganin kayansu ya tsinke a gindin kaba, ba sai sun yi tafiyar kilomitoci akalla biyar zuwa Asibitin Unguwar Rimi ko Barau Dikko ba, ballantna su shafe kimanin kilomita 10 zuwa Asibitin Yusuf Dan Tsoho.

Bayan shekara uku da fara aikin, a shekarar 2010 Gwamna Namadi Sambo ya zama Mataimakin Shugaban Kasa, shekara biyu kafin wa’adin kammala aikin. Amma yanzu shekara 15 ke nan, gwamnatocin da suka biyo bayansa ba su iya kammalawa ba, sai ma tafiyar hawauniya da aikin ke yi.

Gwamnoni biyar sun kasa ne?

Daga lokacin da Gwamna Namadi ya zama mataimakin shugaban kasa zuwa yanzu an yi gwamnonin hudu a Jihar Kaduna, cikinsu har da mataimakinsa, Marigayi Patrick Ibrahim Yakowa da Mukhtar Ramalan Yero da Nasiru El-Rufai sai gwamna mai ci a yanzu, Sanata Uba Sani, amma har yanzu aikin asibitin bai kammala ba.

Shekara 18 da aka shafe ana wanan katafaren asibitin wanda shi ne irinsa na farko mallakin gwamnatin jihar, ya sa burinta na amfani da shi a matsayin asibitin koyarwa ya zama kawalwalniya.

Hakan ne ya sa a shekarun baya daliban da ke karatun aikin likitanci a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) suka kasa kammala karatunsu a jami’ar, sai kasar waje gwamnatin ta tura wasunsu ’yan asalin jihar ta yi domin su kammala karatun nasu, da zummar za ta kammala aikin cikin dan lokaci domin magance matsalar.

Amma duk da haka, haka ba ta cimma ruwa ba, a karshe sai kwaskwarima aka yi wa Asibitin Barau Dikko, daya daga cikin manyan asibitocin gwamantin jihar, aka daga darajarsa ya zama asibitin koyarwa ga daliban likitanci na jami’ar KASU.

Ga al’ummar yankin Sabuwar Kaduna kuwa, duk da cewa sun kosa su gani a kasa, don haka, har yanzu ba su cire tsammani ba, sun zura wa sarautar Allah ido su ga lokacin da wannan asibiti mai gadade 300 zai tabbata, su fara cin gajiyarsa.

A zamanin gwamnatin da ta gabata ta Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarta kan aikin, inda ta bayyana cewa an kammala ginin, saura vangaren da za a shigar da na’urorin da za a yi amfani da su, kafin a kammala vangaren, domin ko an gina, idan aka tashi shigar da kayan sai an sake fasawa.

A lokacin, gwamnatin ta bayyana cewa kayayyakin sun kusa isowa; amma ko a lokacin ana ci gaba da aikin ginin da gyare-gyare, kusan savanin bayanin gwamnatin. Ita ma har wa’adinta ya kare asibitin bai tabbata ba.

Sau hudu ana dage wa’adin kammalawa

Da farko an yi tsara kammala aikin ne a shekarar 2012, lokacin mulkin Marigayi Patrick Yakowa, amma aka dage shi zuwa 2014 a lokacin mulkin Mukhtar Ramalan Yero, saboda abin da gwamnatin jihar ta bayyana a matsayin tsaiko wajen karvar wasu daga cikin kayayyakin zamani da ake bukata.

Rashin cika alkawuran gwanatocin da suka biyo bayan Namadi ya kawo tsaikon wajen kammala aikin da sama da shekaru 10.

Ko a zamanin Malam Nasir El-Rufai ya sha alwashin kammala aikin a shekarar 2017 amma bisani ya dage wa’adin zuwa shekarar 2019, wanda shi ma bai tabbata ba, har wa’adin mulkinsa ya kare.

Al’ummar jihar sun yi tsammanin Gwamnatin El-Rufai ce za ta kammala aikin, saboda yawan ziyarar da tsohon gwamnan ya kai wurin, tare da ba da tabbacin kammalawa kafin karewar wa’adin mulkinsa na shekaru takwas a 2019, amma haka ba ta cim ma ruwa ba.

Yanzu haka gwamnatin mai ci ta Uba Sani ta bayyana cewa nan da karshen watan Maris take sa ran kammala aikin. To shin hakan zai tabbata?

Aikin na ci gaba

Amma binciken Aminiya ya gano cewa a duk da cewa ba a kammala aikin ba, amma an ci karfinsa, har an yi fenti tare da sanya sauran kayayyakin da ake bukata, karashen aikin ake yi domin a bude shi saboda amfanin al’ummar jihar dama na makwabta.

Wakilin Aminiya da ya ziyarci asibitin a makon da ya gabata ya ruwaito cewa ana ci gaba da aiki a harabar asibitin, inda aka kammala fenti aka shimfida kwalta a harabar, an kuma sanya tagogi da kofofi na zamani.

Amma duk da haka ma’aikata na ci gaba da aiki a cikin ginin wanda bisa dukkan alamu an ci karfin aikin.

‘Muna yaba wa aya zaki’

Wata matar aure a yankin, Misis Ana Dominic ta ce suna wahala wajen zuwa asibiti musamman mata, don haka ta roki gwamnatin jihar ta kokarta ta gaggauta kammala aikin wanda an ci karfinsa.

“A taimaka mana domin mu talakawa muna walaha saboda rashin asibiti a unguwar nan. Idan har aka kammala za mu ji dadi matuka,” in ji ta.

Wani dattijo, Mista Philarge Bardom mazaunin kauyen Unguwar Ma’aji da ke a kusa da asibitin ya ce suna matukar wahala tare da iyalanmu saboda rashin asibiti.

“Gaskiya ba mu ji dadin rashin kammala asibitin nan ba kusan shekaru sama da goma da fara shi. Idan an gama aikin aka bude za mu ji dadi saboda zai rage mana wahala da muke sha wajen zuwa asibiti,” inji shi.

Ya roki gwamnatin ta taimaka ta kammala aikin domin inganta rayuwar mutanen yankin dama na jihar baki daya.

Wata mata mai suna Maman Phiriti ta ce, “mata da yara na wahala wajen zuwa asibiti a Unguwar Rimi da sauran unguwannin da ke kusa, saboda haka idan aka bude wannan sabon asibiti za mu samu matukar sauki.”

Ta ce idan aka bude shi, baya ga masu zuwa neman magani, za su iya samun aiki a asibitin ko da aikin shara ne, idan kuma bai samu ba, za su yi kasuwanci da masu zuwa asibitin.

Kammala shi zai rage mana wahalhalu —Mazauna

Wasu mazauna yankin da Aminiya ta zanta da su sun nuna farin cikinsu bisa yadda suka ga aikin na tafiya, amma sun yi fatan gwamnatin jihar ta yunkura wajen kammala shi.

Wani magidanci, Aminu CNN ya ce gwamnatin Namadi ta aiwatar da kusan kaso 35 na aikin kafin, amma kasancewar Marigayi Yakowa da Ramalam Yero ba su dade a mulki ba aka yi watsi da aikin.

“Amma tsohon Gwamna El-Rrufai ya gudanar da kusan kaso 85 kafin ya bar mulki. A yanzu Gwamna Uba Sani yake aiwatar da kusan kaso 95 kuma idan aka daure za a iya kammalawa cikin sauri.

“Idan aka bude shi ko shakka babu zai taimaka wa mutanen Jihar Kaduna, ba wai kawai mazauna Sabuwar Kaduna kadai ba, domin za a rage cinkoso a Asibitin Barau Dikko da sauran asibitocin jihar” in ji shi, yana mai cewa sun kosa a kammala aikin asibitin da kwashe shekaru ana yi.

Na nasa vangaren, Malam Abdurasheed Rabiu, kira ya yi ga Gwamna Uba Sani da ya gaggauta kammala aikin domin shekaru sama da goma ana aiki ba wasa ba ne. Ya ce, “Kammala wannan aikin asibiti ko shakka babu zai taimaka wa mutanen yankin nan saboda mun dade muna jiran ranar da za a bude asibitin.”

Ya ce a yanzu mutane na wahala wajen zuwa asibiti a wasu unguwannin, amma idan aka samar masu da asibiti a kusa da su zai taimaka masu.

Babu kamarsa a Afirka ta Yamma — Kwamishina

Aminiya ta fahimci cewa baya ga amfanin da mazauna yankin da jihar za su samu idan aka bude asibitin, zai rage zuwa neman magani kasashen waje.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an tsara asibitin ne domin ya rage yawan fita zuwa kasasgeb waje neman magani, domin za a samar da duk kayan aikin da ake bukata irin wadanda manyan asibitocin duniya ke da su.

Kwamishinar Lafiya a jihar, Hajiya Umma Ahmed wacce ta tabbatar da hakan ta ce suna sa ran bude asibitin a cikin rubu’in farko a shekarar nan. Ta jaddada cewa babu asibitin da ya kai shi a fadin Afirka ta Yamma don haka suke bukatar wadanda za su kula da shi su zama kwararru.

Saura kiris

Ta kara da cewa karashen aikin asibitin ne ya rage kuma an riga an kawo duk kayayyakin da ake bukata, saka su kawai ya rage a yi.

“Sannan akwai wasu kayayyakin da ba a son saka su sai inda babu kura, saboda ba sa son kura. Sai an kammala sauran ayyukan tukunna daga karshe a saka su. Sashen tiyata ke da irin wadannan kayayyakin.

“Amma idan ka lura har wutar lantarki an jawo kai-tsaye daga babban laying wutar lantarki wato (national grid). Aikin ya yi nisa fiye da yadda ake tunani.

“Muna fatan a watanni ukun farko na shekarar nan a kammala aikin, domin ko su Bankin Raya Musulunci na Duniya wadanda suna cikin masu daukar nauyin ginin asibitin sun yaba da aikin da aka yi a lokacin da suka zo ziyara.

“Ba ma son aikin ya kai karshen shekara ba a kammala ba saboda Gwamna na matukar son ganin ya kammalu. Shi ya sa tun da na hau kujerar nan na matsa domin ganin an kammala aikin, wanda an fara shi ne tun lokacin mulkin Namadi Sambo,” in ji ta.

Ta ce a wannan gwamnatin kowa ya da gaske ake son kammala aikin, domin kusan duk a ranar Alhamis sai an zauna taro da masu aikin domin saboda burinta da na gwamnatin jihar shi ne a kammala aikin asibitin a bana.

Kwamishinar ta kara da cewa duk wani kalubalen da ake fuskanta, tun da wannan gwamnatin ta kama aiki ta kawar da su domin kammala aikin.

Ta kuma bayyana cewa a yanzu suna kokarin ganin sun mayar da janaratocin daga masu amfani da man fetur zuwa masu amfani da iskar gas (CNG) saboda samun sauki.