Shekara 20 da Rasuwar Shata: Waiwaye kan tasirin tauhidi da mu’amula a rayuwarsa (1)
A ranar 18 ga Yuni, 2019, Dokta Mamman Shata Katsina ya cika kwanaki 7,300 da rasuwa, wanda ya zo daidai da shekara 20 cif. Tun daga ranar da zakin mawakan ya rasu na yi tunanin cewa idan Allah Ya raya ni na kai shekara 20 bayan rasuwarsa, zan duba in yi tambihi a kan matsayinsa […]
A ranar 18 ga Yuni, 2019, Dokta Mamman Shata Katsina ya cika kwanaki 7,300 da rasuwa, wanda ya zo daidai da shekara 20 cif.
Tun daga ranar da zakin mawakan ya rasu na yi tunanin cewa idan Allah Ya raya ni na kai shekara 20 bayan rasuwarsa, zan duba in yi tambihi a kan matsayinsa a lokacin. Babban abin da za a duba a yau a game da Shata, shi ne yadda mu’amalarsa da mutanensa da tauhidinsa ga Allah suka yi aiki ga rayuwarsa, lokacin yana raye, da ma bayan babu shi. Iyayen gidansa wadanda ya yi wa wakoki sun tallafe shi cikin mutunci, sun nuna masa gata na musamman. Wannan shi ne dalilin da ya sanya a farko da tsakiyar zamaninsa bai ji kunya ba, bai ji kunyar makada da mawaka abokan hamayyarsa ba. Wato na game da cika baki ya furzas da ya rika yi a wakokinsa da dama, na ratar da Allah Ya hukunta ya ba sauran mawaka. Kalmomin da ke nuna cika baki ya furzas sun hada da: “…zaki mai banka mai ban kashi, Mamman…” da kuma: “ruwa ya bace sai kwarawan asali, kauce yaro kada kadannu su kashe ka…” Yakan kuma ce: “…yanda yai man, bai yi ma maroka ba, ko makadi, ko wani mai waka, ko wane ne…”
Wadannan kalmomi suna matukar dugunzuma watare da hasala mawaka, don dai babu yadda za su yi da shi. Amma yana shan zagi a wajensu kamar kurar bara.
Komai na musamman aka yi ko aka nuna masa, na gata daidai gwargwadon baiwa da daukakar da Allah Ya yi masa da kuma fifikon da Ya yi masa a kan sauran mawaka.
A cikin shekara 20 da rasuwar Shata, a yau kamar makadin yana raye, tunda ga wakokinsa nan barkatai ana ta jin su kullum. Ba ma jin su kadai ake yi ba, a yanzu har da rubuta su ake yi, ana karantawa. An yi bincike masu yawa da rubuce-rubuce da tarurruka masu yawa a kan mawakin.
A cikin kwanaki 7,300 da rabuwar Shata da duniya an rubuta littattafai akalla 3 ko 4 a kan rayuwarsa kuma a ciki an zubo wasu daga cikin baitoci na wakokinsa jefi-jefi. Bayan wannan ma Farfesa Sa’idu Gusau ya wallafa littafi na Diwanin Shatan da ke dauke da wakokinsa kawai ba tare da tarihinsa ba. Sannan Hukumar Tarihi ta Jihar Katsina ta wallafa wasu littattafai biyu su ma a kan Diwani ko rubutattun wakokin makadin. Wannan ya nuna maza-maza yadda hukumomi da masana suke yunkurin adana wakokinsa ta sigogi daban-daban, saboda tasirinsu da sakonnin da suke dauke da su. Sannan ga dalibai nan masu karatun digiri daga na daya zuwa na uku a jami’o’inmu suna bincike a fannoni daban-daban a kan rayuwa da mu’amala da kuma sigogin wakokin makadin. Saura ga su nan iri-iri a manyan makarantu da har ana yawan turo wadansu zuwa gare ni ina duba musu ina ba su duk bayanan da suka kamata.
Yanzu ma abin ya ci gaba, abin ya dauki sabon salo, kowanne dalibi sai ya dauki wani fanni na daban a kan rayuwa da wakokin makadin. Wadansu sukan yi bincike a kan wakokin sarakuna, wadansu a kan wakokin mata, wadansu a kan wakokin zambo da sauransu. Ko kuma a wakokin sarakunan ma (duk da yake an dade ana rubutu a kan wakokin fada ko na iko, amma dai Shata shi ya dada fadada wakokin fada tunda al’amarinsa yana da fadi) ko na mata, wadansu sukan tsuke abin su takaita kurum a kan binciken wakar sarki daya ko ta mace daya da makadin ya wake. Malam Hamza Usman Kankara na Kwalejin Ilimi Mai Zurfi ta Katsina ya yi nazarin digirinsa na biyu a kan wakokin Shata na ta’aziyya. Bashir Dankaura ya rubuta kundin digiri na farko a kan wakokin Gagarabadau ta Shata da ta Mammalo yaron Shatan. Misalai biyu ke nan. A kuma fannin tarurruka don kara wa juna ilimi a manyan makarantu, nan ma al’amarin Shatan ya dauki sabon salo. Manazarta ko masana kan dauki wani bagire daya tilo su yi batu a kansa. Wannan ya nuna cewa an ma samu sabon fage a nazarin adabi. An samu mawaka na zamani masu tasowa wadanda ke amsa sunan Shatan, ko da kuwa mutum (wasu kade-kade yake daban) ba kwaikwayon Shatan yake ba, kurum saboda kwarjininsa. Shi kansa Shatan bai san cewa za a raja’a a yi ayyuka a kansa kamar yadda ake yi a yanzu ba kafin ya rasu. Yau ga shi shekarunsa 20 a kasa amma ga Shatattaki nan ko’ina a Arewacin Najeriya da ma wajenta suna fadada adabi da sunansa.
Akwai abubuwan lura ga Shata a nan. Koda ake ce masa ‘Mahadi mai dogon zamani’ ana nufin duk tashen mawaki, duk kwarjinin mawaki, duk ficensa ba ya wuce shekara 10 zuwa 30, dole zai kwanta ko tauraruwarsa ta dushe, ko wane ne shi. Kai ko da kuwa Ibrahim Narambada Tubali ne ko Musa Dankwairo Maradun. Tun da mun binciki mawakan Hausa masu yin ‘kuriga’ Narambada na a cikinsu. Narambada na hawan gwaji ko ‘kuriga’ kafin ya gabatar da waka, akalla na mako biyu. Sai dai ko bayan shekara 30 a canja ma wakar wani sabon salo, ko yara su zaburo su amsa, kai ubangida kana a gefe guda a matsayin jagora kurum. Shi ko Shata ya shekara 63 yana waka, yana yin abu daya. Wannan shi ne sababin wannan kalma ko inkiya.
A sha’anin tashe, na san ba mawaki ba, ko budurwar kauye tana iya yin sa, wato ta yi zamani kafin ta yi aure. Wadansu mawakan ma kafin su cira sun kwanta. Irin wadannan, zamaninsu ba ya wuce shekara 5 zuwa 10, kamar su: Aura, Turai Rimaye, Ayashe mai kidan duma, Fanteka, Aliyu Disco Baby Argungu, Ahmadu Monkey, Murtala Kaura, Sa’idu Ziti, Sani Dan Indo, Sani Sabulun Sunlight Kanoma, Ali Makaho mai gurmi, da sauransu.
Gaba daya idan ka tattara zancen za ka iya daure shi da tsumma daya, na cewa babban abin fata ga rayuwa shi ne mutum ya roki Allah idan karshensa ya zo, ya zo da kyau, Allah Ya kawo mataimaki wanda za ya tallabe shi.
Da Allah bai kawo wa Shata dauki da Jarman Kano Muhammadu Adamu Dankabo ba, da ya samu nakasu da wulakanci daga maroka a shekara 10 na karshen rayuwarsa. Da sun yi masa dariya, na yadda karshensa zai kasance. Ma’ana, da Allah bai kawo masa Kabo ba, da bai samu yadda yake so ba, su kuma da sun samu yadda suke so.
Shata ya yi ta fama da maroka; munafukai kuma mahassadansa. A gabansa su nuna su masoyansa ne, amma ba su kaunarsa a boye. Abin nan da Hausawa ke cewa ‘ka ga mutum a fuska Annabi Musa amma a zucci Fir’auna.’ Tauhidi da yawan nuna ikon Allah da yarda da Allah su suka ceci Shata daga hannun makiyansa maroka.
Tun daga farkon zamaninsa, da maroka suka lura da irin baiwar da Allah Ya yi masa ta musamman ce, suka shiga yi masa asirrai da sammace-sammace don kada ya yi tashin gwauron zabon da ya yi. Daga karshen rayuwa kuma abokan gaba da Shatan ya faskare su suka zura idanu su ga yaya rayuwarsa za ta kare. Shin zai mutu cikin halin wulakanci koko cikin rufin asiri? To sai ga shi Allah Ya ba su kunya, ba su samu yadda suke so ba.
Za a ci gaba
Dokta Kankara, Malami ne Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma
Za a iya samunsa ta imel: [email protected] ko tarho: (07030797630)