Shekara 30 Atiku na neman kujerar shugaban kasa

Abubuwan da suka faru da Atiku wanda ya fito neman takarar shugaban kasa a karo na shida

Shekara 30 Atiku na neman kujerar shugaban kasa

Zaben 2023 shi ne karo na shida da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, yake fitowa neman kujerar shugaban kasa, wanda tun a shekarar 1993 yake ta hankoro.

A ranar Laraba Atiku ya yanki tikitin namen takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2023 da ke kara matsowa.

Takararsa tasa a zaben 2023 na zuwa ne shekara 30, tun bayan shigarsa harkar siyasa a 1993.

Ga abubuwan da suka faru da shi a tsawon lokacin da ya dauka ya neman kujerar shugaban kasa:

Zaben 1993

A karon farko, Atiku Abubakar ya fito takarar shugaban kasa ne a karkashin jam’iyyar SDP gabanin babban zaben 1993.

Amma bai kai labari ba, inda ya sha kaye zaben fid da dan takara, wanda Cif MKO Abiola da mataimakinsa, Alhaji Babagana Kingibe suka samu nasara.

Sai dai kuma daga baya gwamantin soji ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta soke zaben na 1993, wanda Abiola da Kingibe suka samu kuri’a 8,341,309 (58.36%).

Zaben 2007

Atiku ya kasance mataimakin shugaban kasar Najeriya na tsawon shekara takwas (1999 zuwa 2007).

A lokacin, wasu gwamnoni sun nemi ya fito takarar shugaban kasa a babban zaben 2003, amma ya ce a bari sai Obasanjo ya kammala wa’adinsa na biyu a 2007, wanda kafin nan suka raba gari.

A 2007 Atiku ya sauya sheka daga jam’iyar PDP mai mulki zuwa sabuwar AC, inda ya samu tikitin takarar shugaban kasa.

A wanna karon ma ya sha kaye a hannun dan takarar shugaban kasar jam’iyyar  PDP, Umaru Musa Yar’Adua, wanda ya lashe zaben mai cike da rudani.

Dan takarar jam’iyyar ANPP Muhammadu Buhari, ne ya zo na biyu, Atiku kuma ya zo na uku, a zaben da masu sanya ido na Tarayyar Turai suka ce ba su taba ganin mummunan zabe irinsa ba.

Zaben 2011

Daga baya ya sake komawa PDP, ya nemi takarar shugaban kasa, amma shugaban kasa na lokacin, Goodluck Jonathan ya kayar da shi a zaben fid dan takarar jam’iyyar.

Zaben 2015

A 2014, Atiku ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa, amma Muhammadu Buhari ya kayar da shi da sauran ’yan takara a zaben fid da dan gwani.

Zaben 2019

Zuwa shekararar 2017 ya bar APC ya koma PDP, inda ya zama dan takarara shugaban kasa, amma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kayar da shi.

Zaben 2023

A yayin da ake shirye-shiryen babban zaben 2023 kuma, Atiku ya kara yankar tikitin takarar zaben shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Zaben 2023, shi ne karo na shida da Atiku ke hankoron zama shugaban kasar Najeirya.

Tuni dai ya bayyana wasu bangarori biyar da idan har ya kai labari a 2023 gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kansu.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna