Shekara 30 sun sanya mun bunkasa – Manajan Daraktan Bankin Abbey

Manajan Daraktan bayar da jingina na Bankin Abbey Mortgage Bank, Madu Hamman

Shekara 30 sun sanya mun bunkasa – Manajan Daraktan Bankin Abbey

Manajan Daraktan bayar da jingina na Bankin Abbey Mortgage Bank, Madu Hamman

A wannanna tattaunawar da Manajan Daraktan bayar da jingina na Bankin Abbey Mortgage Bank, Madu Hamman. Ya yi tsokaci sosai kan shekaru talatin da Bankin Abbey ya yi a bangaren jingina da sauran cigaba. Ga yadda hirar ta kasance:

A yanzu ana bikin cikar bankin Abbey shekaru 30 na masana’antar bankin. Ta yaya masana’antar ta fara, kuma me ya sa kuka zabin bankin bayar da jingina?

Wata babbar dama ce ga duk wani kamfani ya yi murnar samun babbar nasara. Mu a Bankin Abbey mun samu nasara a bangaren harkar jingina mu yi bikin cikarmu shekaru talatin saboda na yi imanin muna daya daga cikin bankunan bayar da jingina da suke da juriya da har yanzu suke aiki tun lokacin da aka bashi lasisi na farko na gudanar da bankin bayar da jingina. Abu ne mai mutukar kalubale amma mun cigaba da kasancewa har bayan shekaru talatin yayin da sauran ba su samu nasarar da muka samu ba.

Bangaren bayar da jingina ko kuma bangaren harkar bankin bayar da jingina, ya samu sakamakon dokar shekarar alif dari tara da tamanin da tara wacce ta baiwa masu zaman kansu damar shiga kasuwa. Kafin nan, Bankin bayar da jingina na Gwamnatin Tarayya shi kadai ne a bangaren bankin jingina. Saboda haka, sai Gwamnatin Tarayya ta ga ya dace ta bayar da dama a bangaren ta hanyar baiwa bangaren masu zaman kansu su shigo cikin harkar. Hakan ya sanya an samu kashi na farko na bankunan bayar da jingina da aka baiwa lasisi a shekarar alif dari tara da casa’in da daya.

A shekarar alif dari tara da casa’in da bakwai Babban Bankin Najeriya na CBN ya zama shi ne babban mai sanya ido a bangaren ta hanyar tabbatar da sanya ka’idoji da dokoki na yadda bankunan za su gudana wanda hakan ya sanya bangaren ya cigaba kuma ya bunkasa.

Yaya gasar ta kasance lokacin da kuka shigo masana’antar? Kuma yaya gasar take bayan shekaru talatin?

Gasar a shekaru talatin da suka gabata ta kasance mai tsauri saboda yawan masu ruwa da tsaki a kasuwar. Muna kasuwar yayin da akwai bankuna hudu zuwa biyar amma ba kasafai ake samun sabbin shiga ba, inda hakan ya janyo rashin yarda. To yayin da bankunan da suka kasa suka bar kasuwar sai gasar ta cigaba yayin da manyan bankunan kasuwanci suke gasa da bankunan bayar da jingina kan alfanun jingina.

Amma idan ka kasance a masana’anta a tsawon shekaru talatin kuma za mu iya cewa mun kai gaci kuma mun fahimci yadda juyawar kasuwa take kuma muna tafiya da kasuwa.

Yaya sanya ido yake a shekaru talatin da suka wuce kuma yaya sanya idon yake a yanzu?

Shekaru talatin da suka gabata Bankin Bayar da Jingina na FMBN shi ke kula da bankunan bayar da jingina masu zaman kansu amma sai Babban Bankin CBN ya karba bayar da aka samu matsala ta farko tare da renon da kuma tallafawa bankunan bayar da jinginan masu zaman kansu da kulawa da ka’idoji da suka daidaita kasuwar.

Tun wannan lokaci, Hukumar Kare Dukiyar Masu Ajiya ta NDIC ta shigo domin kare dukiyar da aka ajiye a bankunan bayar da jingina masu zaman kansu wanda hakan ya baiwa abokan huldarmu suka samu nutsuwa a bangaren kare kudinsu. Hakan ya bunkasa kasuwar. Bankin CBN ya cigaba da tallafawa bangaren daya daga ciki shi ne kafa Kamfanin Jinginar Kudi na NMRC. Sai aka samu karin sanya ido da tallafi da shawarwari da kare masana’antar a shekarun.

Ta yaya Bankin Abbey ya bayar da tallafi a masana’antar baki daya?

Gudunmawar da Abbey ya bayar da masana’antar tana da yawa a cikin shekaru talatin da suka wuce. Muna daga cikin membobin Kungiyar Bankin Jingina na Bankuna Najeriya da ake kira da MBAN.

An kafa ta ne don ta rika kare ra’ayin bankunan jingina a tsakanin masana’antar bankuna. Ta haka ne muka bullo da tsare-tsare da za mu rika aiki da masu sanya ido da gwamnati a bangarorin da ake bukatar tallafi da samar da ’yanci ga bangaren don ya bunkasa.

A matsayinsa na memban harkokin kudi a shekaru ashirin da biyar da suka gabata. Mun dauki nauyin gina rukunin gidaje da masu bunkasa kadarori, mun baiwa abokan huldarmu kudi wadanda suke bukatar sayen wasu kadarori.

Abokan huldarmu da dama sun samu alfanun alakar da suke da ita da bankin Abbey na samun gidaje. Abokan huldarmu sun hada da makarantu masu zaman kansu tun farkon shekarar alif dari tara da casa’in sun samu alfanun bunkasawa da daukan nauyin gina makarantunsu.

Ta wace hanya abokan huldar Bankin Abbey suke cin moriyar ayyukan bankin?

Cikin shekarun Bankin Abbey ya cigaba da bunkasa ayyukansa ga abokan huldarsa ta fannin biyan bukatunsu da kuma samar musu da kudi da harkokin jingina. Abokan huldarmu za su tabbatar da hakan ga dogaranmu.

Don bunkasa biyan bukatun abokan huldarmu, mun sanya jarin fasahar zamani a shekaru da suka gabata don bunkasawa da saukaka mu’amala a asusunsu da ke tare da mu. Kwanannan, mun kaddamar da tsarin bankin kudin kasashen waje da tsarin bankin yanar gizo kwanannan mun kaddamar manhajarmu ta tafi-da-gidanka mai suna Abbeymobile.

Duk wadannan an kaddamar da su ne don bunkasa biyan bukatun abokan huldarmu da kara cika burin abokan hulda.

A bangaren bunkasar haja, ta yaya za ka kwatanta hajarku idan aka kwatanta da gasa?

Na fada cewa gasa a bankin jingtina iri daya ce, bambancin kawai shi ne bayanin abin da za ka sanya da kuma abin da kake sa ran samu daga hajar. Mai yawan hajar da muke da alaka da su za su amfana ka samu kadara idan kana da sha’awa.

Ba kawai ka ba mu kudinka ba amma muna son mu karfafa mutane su tara kudi don mallakar gidajensu kuma za ka iya yin haka idan ka tarbiyyanci kanka kuma za ka iya ware wasu kudi daga bisani za ka yi amfani da su.

Wadanne kalubale kuke fuskanta?

Muna fuskantar kalubale da yawa. Kowa ya san abin da muke da shi dangane da dokar yin amfani da fili da kuma irin yadda yake da wahalar samun sauyawa a harkar jingina. Wani tsawon lokaci ne kuma kasuwanci mai tsadar gaske wanda shi ne daya daga cikin kalubalen da ke kawo cikas ga ci gaban bangaren.

Ana ta kokarin rokon gwamnati ta yi wa dokar mallakar fili gyaran fuska don bayar da damar samar da saukin mu’amala ga filaye. Inda dole ka samu amincewar gwamnati na duk wata mu’amala wanda muke fuskantar kalubale da tsada. Yana kawo tsaikon mu’amala kuma yana da tsada ga abokin hulda.

Sauran kalubalen sun hada da yanayin farashin kasuwar da kuma wahalar da bankuna ke sha wajen tabbatar da sanya jari da kuma ribar da za su ci, ta haka abokin hulda ke amfani ya biya abin da ya kasa.

Sauran sun hada da samun kudin da ya dace. Kamar yadda na ce a baya mafiyawan kudin jingina da muke da shi yana da gajeran lokaci. Haka zalika bankunan jingina na sa ran su bayar da bashin shekaru goma zuwa shabiyar ga abokin hulda amma mafi yawan kudin da za a ajiye da za ka iya samu a littafinka shi ne na shekara daya.