Shekara 4 da kisan Sheikh Albani: Lallai Malam bai mutu ba!

Yau shekara hudu ke nan cur da kisan Sheikh Muhammad Auwal Albani Zariya. Don haka a yau GIZAGO (08065576011) ya waiwaya baya ya rubuta wannan tsokaci, a matsayin tunawa ko karin ta’aziyya ga wannan bawan Allah da ya yi wa addinin Allah hidima a tsawon rayuwarsa: “Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma.”  […]

Shekara 4 da kisan Sheikh Albani: Lallai Malam bai mutu ba!

Marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani Zariya

Yau shekara hudu ke nan cur da kisan Sheikh Muhammad Auwal Albani Zariya. Don haka a yau GIZAGO (08065576011) ya waiwaya baya ya rubuta wannan tsokaci, a matsayin tunawa ko karin ta’aziyya ga wannan bawan Allah da ya yi wa addinin Allah hidima a tsawon rayuwarsa:

Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma.”  Wanda duk ya mutu, ba sauri ya yi ba, wanda kuma yake raye, bai yi jinkiri ba; domin kuwa kowa da lokacinsa. Babban dalilin bude wannan tsokaci da wannan gabatarwa shi ne, saboda ta’aziyyar rashin jan gwarzo, masoyin Allah, muzakkarin yada Sunnar Manzon Allah (SAW), Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zariya; wanda a ranar 1 ga Fabrairun 2014 aka samu wadansu tantirai suka bindige shi, tare da matarsa da dansa daya.

Wane ne Sheikh Albani? Babu wai babu inke, marigayi Sheikh Albani, duniya ta gama shaida cewa shi malami ne na kwarai, mai tsattsauran ra’ayin riko da Sunnar Ma’aiki Muhammadu (SAW). An tabbatar da cewa Allah Ya yi masa baiwar ilimin addinin Musulunci, kamar  yadda yake masani kan ilimin zamani kuma mai kishin ilimin.

Mutum ne da Allah Ya yi wa fikira da kaifin basira da iya tsara zance. Idan yana zance, wato wa’azi ko koyarwa komai dakikancin mutum zai iya fahimta. Malamin ya kasance mai fada da karya, mai yaki da zalunci, marar tsoro idan dai a fagen tsage gaskiya ne.

A duk lokacin da ya samu labarin wani al’amari marar dadi ko ya bankado wata munakisa da za a yi wa al’umma, malamin ba ya yin kasa a gwiwa, yakan shiga da fita har sai ya fallasa al’amarin, ya sanar da al’umma. Irin haka ne ya sanya lokacin da Boko Haram suka fara dasa mummunar akidarsu, malamin ya daura damara, ya shiga fallasa su, yana kira ga al’umma su shiga taitayinsu.

A duk lokacin da ya ankara da cewa gwamnati azzaluma ce, malamin yakan jajirce ya fada mata gaskiya, sannan ya barranta da ita. Saboda wannan hali nasa, gwamnatin Goodluck Jonathan ta saka masa kahon zuka. Akwai ma lokacin da aka laka masa sharri, aka ce wai yana da hannu wajen tada bama-bamai a Jihar Kaduna. Da yake Allah ba azzalumin kowa ba ne, aka yi ta doka shari’a, inda daga karshe ya yi nasara, makiyansa kuma makiyan al’umma suka sha kunya.

Marigayi Albani ba ya sassautawa wajen nuna wa masu mulki hanyar kwarai, domin shi ba makwadaici ba ne, ba mai bambadanbci ba ne. A shekarar 2011, ’yan jarida sun taba tattaunawa da shi, inda karara ya nuna wa masu mulki akidarsa ta kaunar talakawa. Ya nuna irin yadda ya kamata masu mulki su rika yi ga malaman addini.

Ga abin da yake cewa:

“Zamanin da gwamnati za ta tuntubi malaman addini domin kawai tana son a yi mata addu’a ya wuce. Ya kamata gwamnati ta ji tsoron Allah, ta zama mai gaskiya a yayin dangantakarta da malaman addini. Ma’ana, ba ina nufin wai a rika saya wa malaman addini motocin shiga ba, ba ina nufin a rika gina musu gidaje ba. Haka kuma ba na nufin wai gwamnati ta rika gina masallatai da makarantu ko ta rika kawo mana littattafai masu dauke da tambarin gwamnati ba, ba na nufin wai gwamnati ta rika ciyar da mutane a lokacin azumin Ramadan. Sam-sam, ba haka nake nufi ba.

“Ya kamata gwamnati ta rika tuntubar malaman addini domin ta san irin matsalolin da al’ummar karkara ke fuskanta. Shi addinin Musulunci, an saukar da shi ne domin magance matsalolin al’umma da biya musu bukatunsu na rayuwa. A nan, ba daidai ba ne a ce za a rika saya wa malaman addini manya-manyan motocin shiga na jif-jif. Haka kuma ba daidai ba ne a rika gina musu gidaje, domin ba shi ne maganin matsalolin da suke faruwa a yanzu ba. Idan gwamnati ta ce za ta rika yi wa malamai haka, to al’umma za su kara tsanar su, su zama abokan gaba a gare su.

“Mun ga duk abin da ya faru a watan Afrilu, inda mutane suka kona motoci da gidajen wadansu malaman addini. Wadansu malaman ma har kashe su aka yi saboda an yi zargin cewa wakilan gwamnati ne.

“Ya kamata gwamnati ta shiga harkar tafiyar da addini a kasar nan. Daga karshe, kamata ya yi gwamnati ta rika tuntubar malaman addini, ba kamar yadda take daukarsu a matsayin masu tsattsauran ra’ayi ba. A nan, ba ina nufin gwamnati ta rika amfani da jami’an tsaro na SSS suna uzura musu ba. Kamata ya yi su rika gwamutsarsu, domin su fahimci irin akidojinsu. Duk gwamnatin da ta kulla gaba ko yaki da a’ummarta ko kuma wadansu daga cikin al’ummarta ba za ta iya kawo ci gaba ba.”

Wannan shi ne bayanin muzakkarin malami, wanda ke kishin ci gaban al’umma.

Wani abu da ya kamata mutane su fahimta game da Albani shi ne, ba shi ne malamin addini na farko da aka taba hallakawa ba. A shekarar 2007, an hallaka Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, a lokacin da yake gabatar da Sallar Asuba, a masallacin da yake jagoranta da ke Kano. Yana cikin sujada, azzalumai suka yi masa ruwan harsasai kuma maganar ke nan har zuwa yau. Bayan Malam Ja’afar, an hallaka Malam Danmaishiyya a Sakkwato, wanda shi ma shahararren malami ne da ke adawa da zalunci. Ga shi kuma an hallaka Malam Albani, wanda kowa ya shaida shahararsa wajen yaki da zalunci da azzalumai.

Abin tambaya a nan shi ne, shin bayan kisan Sheikh Albani sai kuma wa? Idan ba mu manta ba, a can baya, tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa gwamnatin Goodluck Jonathan da ta shude, ta taba tanadar wasu gungun makasa, wadanda za su rika bin mutanen kirki suna kashewa da bindiga. Irin mutanen da za su rika hallakawa sun hada da malaman addini da masu tsage gaskiya da sauran masu adawa da zaluncin gwamnati. Ga shi a daidai wancan lokacin ne aka bindige Albani, sai kuma wa?

Wani abu da ya kamata wadanda suka hallaka Albani su sani shi ne, sun yi asara duniya da Lahira, a yayin da shi kuwa mun tabbata a yanzu yana cikin farin ciki a kushewarsa; domin kuwa dukan nauyinsa ya koma kansu. Na tabbata makasansa a yanzu suna cikin bakin ciki da kuncin rayuwa, musamman saboda mummunar addu’ar da miliyoyin mutane ke yi musu, kuma za a ci gaba da yi musu ita har ranar tashin Kiyama, inda za su hadu da wani babban bakin cikin da narkon azaba har abada.

Mu kuma da muke alhinin rashin wannan jarumi, kamata ya yi a kullum mu rika yi masa addu’a. Mu jajirce wajen bibiyar darussan da ya dade yana koya wa al’umma. Mu kasance masu gaskiya da son gaskiya. Mu kasance masu nazari da neman ilimi kuma da aiki da shi. Allah Ya jikan Malam Albani, Allah Ya sa ya huta. Allah Ya dayyaba ilimin da ya bari da iyalin da ya bari da daliban da ya bari. Allah Ya tada magajinsa, Ya ba shi fikira da kaifin azamar ci gaba daga inda ya tsaya. Amin!