Shekara 40 a gadon mulki: Jonathan ya jinjina wa Sarkin Lafiya

Shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan ya jinjina wa Mai martaba Sarkin Lafiya kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Nasarawa, Alhaji Isa Mustapha Agwai na daya kan kokarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a jawabinsa wajen bikin cika shekara 40 a karagar mulki da Sarkin […]

Shekara 40 a gadon mulki: Jonathan ya jinjina wa Sarkin Lafiya
Shekara 40 a gadon mulki: Jonathan ya jinjina wa Sarkin Lafiya

Shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan ya jinjina wa Mai martaba Sarkin Lafiya kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Nasarawa, Alhaji Isa Mustapha Agwai na daya kan kokarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a jawabinsa wajen bikin cika shekara 40 a karagar mulki da Sarkin ya yi a karshen makon da ya gabata.
Shugaba Jonathan wanda Ministan Ayyuka na Musamman Alhaji Kabiru Turaki ya wakilta ya ce lallai an samu dimbin nasarori a karkashin jagorancin Sarkin na Lafiya, inda ya yi fatan Allah Ya ja zamaninsa Ya kuma kara masa lafiya.
Da yake jawabi Gwamnan Jihar, Umaru Tanko Al-Makura ya ce shekara 40 da Sarkin Lafiya Alhaji Isah Mustapha Agwai ya shafe a karagar mulki sun kasance masu dimbin tarihi. Ya kuma yaba wa Sarkin dangane da dimbin nasarori da ya samu a cikin wadannan shekara 40 inda, ya ce sai fa Sarki mai sadaukarwa ne kawai zai iya cimma wadannan nasarori.
Gwamnan ya yaba irin gudunmawa da Sarkin yake bayarwa wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da ci gaban al’ummar jihar. Daga ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen yaki da munanan ayyuka a jihar, inda ya yi kira ga al’ummar jihar su tabbatar da dorewar zaman lafiya don ba gwamnatinsa damar ci gaba da samar musu da ribar dimokuradiya.
An kawo karshen bikin da nada Janar T.Y. danjuma (mai ritaya) a sarautar Barde Babba na Lafiya, inda aka nada matarsa Deisy danjuma sarautar Aminiyar Lafiya.
A jawabin Janar danjuma ya yaba wa sadaukarwar Sarkin da yadda yake shawo kan batuttuwa wajen raya birnin Lafiya da kewaye da kasa baki daya, kuma ya gode masa dangane da wannan karamci.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin akwai tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da Babban Hafsan Tsaro Iya Mashal Aled Bade da tsofofin gwamnonin jihar Sanata Abdullahi Adamu da Alhaji Aliyu Agwai Doma da ministoci da sarakunan gargajiya daga ciki da wajen jihar. Sarkin Lafiya Alhaji Isah Agwai an haife shi ne a 1935, kuma ya zama sarkin Lafiya na 16 ne a 1974. Kuma a zamaninsa masarautar ta samu gagarumar bunkasa inda garin Lafiya ya zama hedkwatar Jihar Nasarawa a 1996.