Shekara 40 ina kasuwancin karafa – Alhaji Munkaila
Wani dattijo da ke harkar kasuwancin tsofaffi da sababbin karafa a Kasuwar Gombe Alhaji Munkaila Muhammad, ya ce ya samu rufin asiri cikin shekara 40 da fara wannan kasuwanci. Alhaji Munka’ila Muhammad, ya ce ya fara harkar ce tun yana Jos a Jihar Filato shekara 40 da suka gabata amma dawowarsa Gombe yanzu shekara 35 […]
Wani dattijo da ke harkar kasuwancin tsofaffi da sababbin karafa a Kasuwar Gombe Alhaji Munkaila Muhammad, ya ce ya samu rufin asiri cikin shekara 40 da fara wannan kasuwanci.
Alhaji Munka’ila Muhammad, ya ce ya fara harkar ce tun yana Jos a Jihar Filato shekara 40 da suka gabata amma dawowarsa Gombe yanzu shekara 35 ke nan kuma ya koyawa yara tun yana Jos din, wadansu kuma ya taho da su Gombe kafin ya yaye su.
Ya ce ya fara kasuwancin ne tun bai da jari wanda sai ya fita da kansa ya nemi karafan ya sayar har ta kai ya fara samun kudin da yake saye daga mutane yana sayarwa.
Dattijon ya ce da ya fara ne da harkar gorar ruwa wato aluminiyum ya koma bola jari har ya koma hadawa da sababbi.
Alhaji Munka’ila ya kara da cewa wannan harka ta kasuwancin karafa rufin asirin da ke cikinta ya kai domin duk wata bukata idan ta taso daidai gwargwado za ka iya biya wa kanka ba sai ka nemi wani ya yi maka ba.
Alhaji Munkai’la, ya ce a dalilin saye da sayar da karafan nan babu wanda bai san labarinsa ba a Arewa maso Gabas.
Yace da za a samar da kamfanin da zai sarrafa karafa a nan kusa a kasar nan kasuwancinsu zai kara habaka, kuma jama’a da dama za su kara samun aikin yi.
Sai ya yi kira ga masu kasuwancin karafa irin nasu su rika yin harkar da gaskiya don su ci gaba, “Muddin mutum ba ya kasuwa da gaskiya ba zai ga alheri ba,” inji shi.
Ya ce duk wanda yake harka da gaskiya ko ba kudi a hannunsa zai ci gaba muddin yana da adalci jama’a za su rika ba shi kaya yana kasawa ya sayar ya ba su kudinsu.