Shekara 44 da yakin basasa, ba a biya sojojin Najeriya hakkokinsu ba
Tsofaffin sojojin sun yi zanga-zanga, saboda ana biyan sojojin Biafra da suka yaki Najeriya
Tsofaffin sojojin Najeriya sa suka yi yakin basasa domin kare kasar sun yi zanga-zanga kan rashin biyan su kudaden su na fansho har tsawon shekara 44 bayan yakin.
A ranar Laraba ne sojojin sa-kan da ake kira ‘Buhari Boys’, wadanda suka ajiye aiki bayan yakin, suka bayyana haka a lokacin zanga-zangar da suka gudanar a Ibadan, baban birnin Jihar Oyo.
- Dalibai sun kashe matashiya a Sakkwato saboda zargin batanci ga Annabi
- Zargin batanci: Kotu ta umarci ‘Legal Aid’ ta ba Abduljabbar lauyoyi
Tsoffin sojojin daga Arewaci da Kudancin Najeriya sun daga kwalaye dauke da rubutu ciki har da, “Muna mutuwa saboda rashin biyan mu hakkokinmu shekara 44 bayan mun yi yaki don kare martabar kasarmu.”
Kakakinsu, Pa Babawande Philips, ya ce gwamnati ta yi watsi da su bayan rawar da suka taka a fagen fama don hada kan Najeriya, ga shi yawancinsu girma ya kama su baya ga halin talauci da ya kassara su, wasu kuma sun mutu.
A cewarsa, sun dauki wannan matakin ne don Shugaba Buhari ya san da su a biya su kudaden fanshonsu.
Philips ya bayyana mamakin dalilin da bayan duk wahalar da suka sha, amma bayan shekara 44 bayan yakin aka ki biyan su.
Ya ce duk da cewa an san sun yi yaki don dorewar Najeriya, amma an ki biyan su, alhali sojojin Biafra da suka yaki Najeriya an biya su kudadensu na sallama da fansho.
Ya ce, “Suna amfani da dokar soja ta 102 don hana mu hakkokinmu, amma bai kamata su yi amfani da ita a kanmu ba, tunda ba su yi amfani da ita kan sojojin Biafra ba.”
A cewarsa tun shekara 2002 suke fafutikar ganin an biya su hakkokin nasu, amma har yanzu babu wani kwakkwaran abu da suka gani daga gwamnati.
Ya kara da cewa “Suna riya cewa duk wanda bai shekara 15 a bakin aikin soja ba bai cancanta a biya shi fansho ba.
“Sun manta akwai sanarwar da aka fitar a 1977 cewa duk sojan da ya bar aiki bayan shekara 10 amma kasa da shekara 15 bakin aiki ba, yana da hakkin a biya shi kashi 40 na kudaden fansho da garatuti.
“Ban sani ba ko ba su san da sanarwar ba, idan ba su san da ita ba to su je su bincika, domin duk wadannan takardun muna da su.
“Muna kuma da takardun tantancewar da aka yi a 2005 da 2007 a tare da mu.
“Ba mu san dalilin da suke ci gaba da wahalar da mu ba, ga shi yawancinmu na fama da talauci, wadansu ma sun rasu.”