Shekara 50 da kisan Martin Luther King Jr
A shekaraniya Laraba 4 ga Afrilu aka yi bikin tunawa da kisan dan rajin kare hakkin jama’a bakar fatar Amurka, Rabaran Martin Luther King Junior shekaru 50 da suka gabata, inda wani dan wariyar launin fata a Amurka, James Earl Ray ya bindige shi a 1968. Shekara 50 da aukuwar wannan lamari, kalaman Martin Luther […]

A shekaraniya Laraba 4 ga Afrilu aka yi bikin tunawa da kisan dan rajin kare hakkin jama’a bakar fatar Amurka, Rabaran Martin Luther King Junior shekaru 50 da suka gabata, inda wani dan wariyar launin fata a Amurka, James Earl Ray ya bindige shi a 1968.
Shekara 50 da aukuwar wannan lamari, kalaman Martin Luther King suna ci gaba da zama ababen da ke burge mutane da yawa, musanman jawabinsa a kan karfafa ’yancin bakar fata wanda ya sa ya shiga kundin tarihi. A jawabin Martin Luther ya rika cewa “I habe a dream” inda yake cewa, “Ina fata ’ya’yana hudu za su girma a wata kasa da za a dubi halinsu a yanke hukunci amma ba launin fatar jikinsu ba.”
Da wadannan kalaman da Martin Luther King ya yi a gaban wani gangami na fiye da mutum dubu 250 ciki har da fararen fata a birnin Washington a ranar 23 ga watan Agustan 1963, ya shiga kundin tarihi. A kullum burinsa shi ne karfafa ’yancin bakar fata dangane da matsalolinsu na yau da kullum da yadda suke fuskantar matsala wajen neman aikin yi.
An haife shi a ranar 15 ga Janairun 1929 a birnin Atlanta na Jihar Georgia da sunan Michael King Jr. Mahaifinsa fasto ne mahaifiyarsa kuma malamar makaranta. Tun yana karami ya fuskanci wariyar launin fata, amma duk da haka bai karaya ba, ya yi karatu har ya kammala jami’a a fannin ilimin halayyar zaman jama’a da na addinin Kirista. Sai dai mahaifinsa ya canja masa suna bayan ziyarar da ya kai birnin Berlin a 1934 lokacin da ya hadu da dan rajin sauyin addinin Kiristan nan Martin Luther.
Haka kuma yana sha’awar yin koyi da wadansu fitattun mutane irinsu Aristoteles da Mahatma Ghandi musamman game da gwagwarmaya cikin lumana. A 1953 ya auri Coretta Scott Williams suka samu ’ya’ya hudu da ita. dan kwatar ’yancin ya yi bakin jini ba kawai a wajen wadansu daga cikin fararen fatar Amurka masu akidar wariya ba, ya sha yin dauki-ba-dadi da hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka FBI wadda ta zarge shi da yada akidar gurguzu. A ranar 4 ga Afrilun 1968 wani mai aikata laifi farar fata dan wariyar launin fata, James Earl Ray ya bindige Martin Luther King Jr., a gaban wani otel da ke birnin Memphis na Jihar Tennessee. Ya mutu yana da shekara 39 a duniya.