Shekara 52 da kisan su Sardauna (III)

Ranar 15 ga watan kowane Janairu, da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware don tunawa da ‘yan mazan jiya, ba ta dace ba. Kodayake lallai sojoji sun taka rawa wajen hana Najeriya rabewa, to kuma in za mu tuna, sun taka mummunar rawa wajen haddasa yakin basasa. Ke nan, ba laifin ‘yan siyasa ba ne kadai. […]

Shekara 52 da kisan su Sardauna (III)

Ranar 15 ga watan kowane Janairu, da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware don tunawa da ‘yan mazan jiya, ba ta dace ba. Kodayake lallai sojoji sun taka rawa wajen hana Najeriya rabewa, to kuma in za mu tuna, sun taka mummunar rawa wajen haddasa yakin basasa. Ke nan, ba laifin ‘yan siyasa ba ne kadai. Za mu yi abin nan da bahaushe ke cewa “in bera da sata daddawa ma wari”. Ka da mu manta wadanda suka dauki bindiga suka kashe su Sardauna, su Tafawa  balewa, su Yakubu Pam, su Akintola da sauran su, ba ‘yan siyasa ba ne. Sojoji ne wadanda shugabannin farko suka tura su makarantu, sannan suka dauki dawainiyarsu, wasu ma har Ingila aka je aka horar da su, amma da suka dawo, suka juya bakin bindiga suka  ci amana. Ka dauki wanda ya kashe Sardauna, mutum ne wanda ya shaku da Sardauna, wata ruwayar ma na cewa, Manjo Chukwumeka Nzeogwu Kaduna na daya daga cikin mutanen da Sardauna ya taimaka,  amma saboda rashin mutunci shi ne ya sanya bindiga ya harbe Sardauna da uwargidansa, tare da kona gidan. Amma saboda rashin mutuncin na mahunkuntan Najeriya, har jana’izar ban-girma aka yi wa Nzeogwu, inda aka binne gawarsa a makabarta da ake rufe sojojin Najeriya da suka yi shahada a filin daga. Kuma wai ma a Kaduna aka binne shi! Saboda haka, ko mun ki, ko mun so, sojoji sun taka rawa babba wajen haddasa fitinar yakin basasa a Najeriya. 

Dalilin da suka sa  aka kashe shugaban mulkin soja, wanda ya hau bayan hambarar da su Tafawa balewa, wato J.T.U. Aguyi Ironsi shi ne , daga ciki akwai batun  kememe da ya yi na kin hukunta sojojin da suka aiwatar da juyin mulkin 15 ga Janairu, 1966. 

Idan kuma dalilin da ya sa aka zabi ranar 15 ga watan Janairu a matsayin ranar tunawa da tsofaffin sojoji cewa saboda ko ita ce  gwamnatin tarayyar Najeriya ta zaba a hukumance a matsayin ranar da aka kawo karshen yakin basasa, to wannan ba gaskiya ba ne, domin ra’ayi ma ya bambanta a kan hakikanin lokacin da za a ce an kawo karshen yakin. Amma in dai ba wata boyayyiyar manufa, to kamata ya yi a ce sojojin Najeriya su mayar da ranar 12 ga watan Janairu, a matsayin ranar tunatarwar, domin  madugun tawayen Biyafara, Kanar Ojuku ya arce ya bar Najeriya zuwa kasar Ibory Coast, inda aka ba shi mafaka tun ranar 10 ga Janairun 1970. Kana kuma, Kwamandan yaki na bangaren ‘yan tawaye, ya yi sanarwar a je makamai ranar 12 ga   watan Janairu ba ranar 15 ba. Ranar da ‘yan tawaye suka yi suranda (mika wuya), ita ce ranar da aka kawo karshen yakin basasar Najeriya , domin ai bangare daya ba ya yaki.

To amma ci gaba da martaba ranar tunawa da tsofaffin sojoji, tare da kawar da kai game da mummunar ta’asar da suka tafka ranar 15 ga Janairun 1966, inda suka wuntsilar da kundin tsarin mulkin kasar, tare da bi gida-gida suna kashe muhimman mutanen da sune suka jagoranci kasar wajen sama mata ‘yancin mulkin kai, ba karamin zalinci ba ne, kuma rashin adalci ne, wanda ya kamata a duba. Fassarar wannan, bai wuce kokarin da wasu ke yi na mantar da mu daga wani muhimmin bangaren tarihin kasar nan ba.

Boye gaskiya da kokarin sauya tarihin kasar nan, da aka fara tun bayan 15 ga watan Janairu, 1966, shi ne yasa har yanzu wasu al’ummar  kasarnan kamar kungiyar IPOB ke ci gaba da tada rigima a kasar nan.

Mu dawo batun masu zagin Sardauna. Ko makiya sun ki sai mun ci gaba da tunawa da Gamji dankwarai bisa kyakkyawan shugabanci da ya kawo a Arewa. Wani marubucin tarihi Sardauna mai suna Buhari Daure a cikin littafinsa mai suna Tsayayyen Namiji, ya zakulo kadan daga cikin dimbin ayyukan da Gamji dan Ibrahim ya yi a lokacin mulkinsu. 

“ Ya ceto Arewacin Kamaru, inda bayan kada kuri’ar mutanen yankin, suka zabi su ci gaba da zama a Najeriya. Wannan na da nasaba da cewa Sardauna ya fito daga tsatson shugabannin daular Sakkwato, don haka mayaki ne, wanda yasan darajar kasa, bai yi sakaci Najeriya ta yi asarar koda taki daya ne na kasar mu ba. Sabanin yanzu inda sakacin shugabanninmu ya sa Bakassi ta koma hannun Kamaru. Najeriya ta yi dimbin asarar kasa da albarkar kasa ga kuma uwa uba rashin zaman lafiya a wannan yankin.

Ta bangaren ilimin zamani, har yau ba a samu wani gwamna ya taka matsayin da Sardauna ya taka cikin kankanen lokaci wajen harkar bunkasa ilimi. Sardauna yasan tarihi, ya fahimci cewa sai da Turawan Mishan wadanda sune suka kawo boko a Najeriya suka shekara tamanin a Kudu kafin abin ya iso Arewa. Don haka akwai ratar shekaru tamanin tsakaninmu da Kudu. Amma kasa da shekaru goma, sai da Arewa ta fara zama barazana ga Kudu ta bangaren ilimi.Lokacin da Isa kaita ke Ministan Ilimi a Gwamnatin Sardauna, an gina  sama da makarantu 50 a wurare daban-daban na Arewacin Najeriya. Wasu daliban an tura su kasashen ketare ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba. Da yawan shugabannin yanzu masu korar malamai, sun ci albakarcin tsare-tsaren ilimi ne na gwamnatin Arewa karkashin Sardauna, kamar yadda marubucin littafin Sardauna, Buhari Daure ya ruwaito cewa a shekarar 1959 ne Majalisar Arewa ta amince da gina jami’ar da ta zama Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. A jawabinsa lokacin bude jami’ar, Sardauna ya fadi makasudin kafa ABU:

 “Domin ilimantar da matasanmu maza da mata ba tare da nuna wani bambanci ba.Wannan ce hanyar da kawai za ta taimake mu wajen shawo kan kalubalenmu”.

Yau ba ma a Najeriya ba, a duniya ana maganar ABU, ita ce ta yaye ‘yan bokon farko na Arewa kuma shi ya sa muke ji da ita. Duk wanda ba ya son A.B.U. to ba ya son ‘yan Arewa ne kawai.

A cikin dan kankanen lokacin sai ga Arewa ta mallaki hamshakan kamfanonin NNDC da kamfanonin masaku, na matse mai sun fallatsa ko’ina a Arewa. Lokacin da muka samu kamfanin dab’i na NNPC, jaridar Gaskiya Tafi Kwabo,jaridar Turanci ta New Nigeria.

Lokacin muka samu hukumar samar da gidaje ta NNHC. Wannan hukuma ta samu nasarar gina gidaje masu saukin kudi a garuruwan Gusau, Zariya da Kaduna.

Ta bangaren bunkasa addinin Musulunci, an gina Masallatai, an musuluntar da masu sha’awar shiga Musulunci, taimakon mabukata da kyauta ba a yi kamar Sardauna ba. Wannan ya sa wani mawaki ke cewa “ ka dubi yawan mutanen da sun ka taru Kaduna, gidan Sardauna, kuma kullum sai ya ba kowa.”

Duk da son addini da rikon addini da kyawawan al’adun Arewa da Sardauna ke da shi, bai sa shi ya kuntata wa Kiristoci da wadanda ba Musulmi ba. Kai kamar yadda shugabannin Kiristocin ke fada, har yanzu ba a sake shugaban da suka ji dadi kamar Sardauna ba.

Gaskiya ba lokaci idan na ce zan rubuta komai game da Sardauna, kai wani abin ma, idan na rubuta jahilai na iya kkaryata mutum, to amma gaskiya tun da aka kashe Sardauna, har yanzu Arewa ba mu kara samun kamar sa ba. Ga son addini, ga rike kyawawan al’adu misali taron daba da ake shiryawa, karfafa mawakan gargajiya da kyauta da fara’a da zumunci da tausayi da jarumta kai siffofin Sa Ahmadu Bello Sardauna kyawawa yawa ne gare su. Ga juriya, da iya zama da wadanda ba su hada addini daya ko kabila ba. To amma kamar yadda Sardaunan da kansa ya ce: “ Duk irin kokarinka, sai mutane sun ce ba haka ba; in kai mai arziki ne su ce kai mai arziki ne, in kai talaka ne, sai sun yi magana, idan kai abin kirki za su yi magana. Haka in kai na banza ne. Maslaha ita ce ka yi iyakar bakin kokarinka. Allah ya jikan Gamji, dankwarai.

Kwamared Bishir Dauda ya rubuto makalarsa daga Sabuwar Unguwa Katsina,kuma shi ne  Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka ta kasa 08165270879 Nura