Shekara 54 Baya: Tunawa da kisan gillar Gamji Sardauna
A ranar Larabar makon jiya (15-1-2020), Firimiyan Tsohuwar Jihar Arewa na farko kuma na karshe, Alhaji Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato ya cika shekara 54 da barin duniya. Ya rasa rai ne a wani kazamin juyin mulkin soja na farko a kasar nan, bayan samun ’yancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya (1-10-1960). Manjo Chukwuma […]
A ranar Larabar makon jiya (15-1-2020), Firimiyan Tsohuwar Jihar Arewa na farko kuma na karshe, Alhaji Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato ya cika shekara 54 da barin duniya. Ya rasa rai ne a wani kazamin juyin mulkin soja na farko a kasar nan, bayan samun ’yancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya (1-10-1960).
Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu, dan kabilar Ibo ne ya jagoranci juyin mulkin, wanda bayan Sardauna aka kashe wadansu jiga-jigan Arewa, irin su Sa Abubakar Tafawa Balewa Firayi Ministan Najeriya na farko kuma na karshe da Birgediya Janar Maimalari da dsauransu. Kai har ma da Firimiyan tsohuwar Jihar Yamma, Cif Samuel Akintola. Amma daga Tsohuwar Jihar Gabas, ba wani babba daga cikin ’yan kabilar Ibo da aka kashe. Dadin-dadawa, wadanda suka shugabanci juyin mulkin, suka kuma dora Manjo Janar J.T.U Aguiyi Ironsi, dan kabilar Ibo a kan karagar mulki; a zaman sabon Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan kasar nan.
Babban hanzarin da Manjo Nzeogu ya bayar a wancan lokaci, shi ya zama hanzarin da sojoji suka rika bayarwa duk lokacin da suka yi kutse suka kwace mulki, walau daga hannun soja dan uwansu ko daga hannun zababbiyar gwamnatin farar hula, lokacin da sojojin suke yayin kwace mulki a kasar nan. Wato shi ne batun zargin gwamnatin da ke kan karagar mulki da cin hanci da rashawa da kasa iya tafiyar da mulki da mayar da mutanen wani bangaren kasar saniyar ware. Da Allah Ya yi wa Manjo Nzeogwu tsawon kwana da ban san abin da zai ce ba a kan irin yadda kasar nan ta dulmuye cikin kogin cin hanci da rashawa da nuna bambancin addini da na kabila da ma na jinsi da suka mamaye dukkan fadin kasar nan a yau, al’amarin da ya samu asali daga mulkin soja.
Wancan juyin mulki na farko da wanda aka yi na biyu, wata shida bayansa, inda aka kashe Shugaban Kasa Janar Aguiyi Ironsi a Ibadan, juyin mulkin da aka zargi hafsoshin soja ’yan Arewa da jagorantarsa a zaman ramuwar gayyar na farko da dora Laftana Kanar Yakubu Gowon dan Arewa a karagar mulki; shi ya haddasa ’yan kabilar Ibo a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Gabas, Laftana Kanar Odumegwu Ojukwu ballewa daga Tarayyar Najeriya, ya kuma kafa kasarsu ta Biyafara.
Hakan ya jefa kasar nan a cikin Yakin Basasa na tsawon wata 30. Yakin da ba a kawo karshensa ba sai a ranar 15 ga Janairun 1970, yau shekara 50.
Abin da ya biyo bayan wannan juyin mulki, za a iya cewa shi ne babban tushen kallon hadarin kajin da yanzu da manya da kananan kabilun kasar nan suka samu kansu ciki, ta yadda kowa ya yi magana ba kasafai ake ganin muhimmancinta ba, sai an fassara ta da addini ko kabila ko jinshin da mutum ya fito. Haka labarin yake a jihohi da kananan hukumomi, duk kuwa da a yau an raba wadancan jihohi uku (Arewa da Yamma da Kudu maso Gabas), zuwa jihohi 36 da kananan hukumomi 774, baya ga Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Bari in dawo kan dan talikin da nake son tunawa da shi a yau, wanda ya jagoranci Arewa da kasa baki daya (kasancewar jam`iyyarsa ta NPC, ita take mulki a Gwamnatin Tsakiya), wato Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. Mutumin da sauran mukarraban gwamnatinsa suka jajirce iyakacin jajircewa wajen dorawa bisa ga kamanta gaskiya da adalci daga inda Turawan Mulkin Mallaka suka tsaya. Ya tsaya kan samar da duk wani abu na ci gaba da Arewa da kasa ke alfahari da shi, kusan har zuwa wannan lokaci.
Alal misali, Gwamnatin Jihar Arewa ta jajirce a kan lallai sai ’yan Arewa sun yi karatun boko, duk da kyamar da wadansu suke yi masa, cewa karatun Nasara ne. Don samun nasara a kan fannin ilimi, ya sanya gwamnatin ci gaba da rarraba tsarin karatun koyon aikin koyarwa da na koyon sana’a, ilimin da a yau kamar yadda muke gani kowane da irin muhimmancinsa. Kafin Gwamnatin Arewa ta kai ga kafa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1962, duk wani dalibi dan Arewa da ya cancanci shiga jami’a, gwamnatin na daukar nauyinsa ko dai zuwa Kwajejin Jami’ar Ibadan ko kuma zuwa kasashen waje, musamman kasar Birtaniya.
Hakazalika a kan tattalin arziki, Gwamnatin Sardauna ita ta kafa Bankin Arewa da gwamnonin jihohin Arewa suka yi wa rikon sakainar kashi, har ya zama mallakar wadansu mutanen Kudu. Yayin da Hukumar Bunkasa Arewa (NNDC) ta dade a some, haka labarin yake a kan Kamfanin Buga Jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da ke Kaduna, shi ma tuni ya durkushe kuma gwamnonin sun kasa farfado da shi.
Ta fannin ayyukan noma da kiwo, Gwamnatin Sa Ahmadu Bello ce ta inganta tare da karfafa wannan babbar sana’a, ta hanyar kafa Hukumar Sayen Amfanin Gona ta Arewa (NSMB). Samuwar haka, manoman Arewa suka rika noma gyada da auduga da samar da fatu da kiraga da kasar nan ta rika samun kudaden shiga daga kasashen waje, wadanda da su aka gano danyen man fetur da a yau kasar take alfahari da shi. Danyen man da mutanen Kudu ke mana gori, cewa mun zama cima-zaune a kan tattalin arzikin kasar nan. Hatta sufurin jirgin kasa yana cikin hanyoyin sufuri da Gwamnatin Sardauna ta tabbatar da dorewarsa a zamaninta.
Hatta siyasar da suka yi ta fi ta wannan zamanin tsabta da kana’a da girmama abokan hamayya da ’yan kasa baki daya, duk kuwa da irin kuntatawa da ake zargin talakawa masu ra’ayin da ya sha bamban da na Jam’iyyar NPC.
Sai dai mu ce Allah Ya jikan Gamji dan kwarai da sauran mukarrabansa. Kamar yadda shahararren mawakin kasar Hausar nan ya fadi a wakasar ta ta’aziyyar Sardauna. “Gaba ta wuce baya adda saura. Yanzu ku meno wani kama tai.” Shekara 54, sai fadi da baka amma ba aiki ba kamantawa irin ta Sa Ahmadu Bello.