Shekara 70 ina sana’ar niƙa amma ban taɓa shiga wannan hali ba
Wani mai sana’ar niƙa tun zamanin zuwan Sarauniyar Ingila Najeriya ya ce bai taɓa shiga irin wannan halin wahalar rayuwa da ake fama da ita a yanzu ba. Malama Abdullahi, wanda ake wa laƙabi da Baturen Niƙa, ya bayyana haka ne a lokacin da ya koka a kan matsalar rashin wutar lantarki. Ya ce tun […]
Wani mai sana’ar niƙa tun zamanin zuwan Sarauniyar Ingila Najeriya ya ce bai taɓa shiga irin wannan halin wahalar rayuwa da ake fama da ita a yanzu ba.
Malama Abdullahi, wanda ake wa laƙabi da Baturen Niƙa, ya bayyana haka ne a lokacin da ya koka a kan matsalar rashin wutar lantarki.
Ya ce tun zamanin mulkin Firimiyan Arewa, Marigayi Sardaunan Sakkwato, Ahmadu Bello, ya fara aiki niƙa da inji amma bai taɓa shiga halin da ya shiga yanzu ba.
Ya ce, “kuma ga shi har yanzu su masu kawo takardar biyan kuɗin wutan suna bin mu wai mu biya kuɗi.
“Gaskiya a matsayina na mai wannan shekarun ina iya cewa kasarmu Najeriya kullum komawa baya ake yi maimakon ci-gaba da aka ce wai ana samu.
“A ƙarshe ina shawarar shuwagabannin da su sake tunani.”