Shekara 75 A Duniya: Taya murna ga dan kishin kasa Dokta Bukar Usman, OON
A yau GIZAGO (08065576011) ya karkata akalarsa kacokan ne ga taya daya daga cikin mashahuran ’yan kishin kasa da ke raye a wannan lokaci. Rayuwar marubuci, manazarci, mai yi wa al’umma hidima, Dokta Bukar Usman, abin nazari ce ga al’umma musamman masu tasowa su yi koyi da ita: A jibi Lahadi (10-12-2017), fitaccen marubuci, […]
A yau GIZAGO (08065576011) ya karkata akalarsa kacokan ne ga taya daya daga cikin mashahuran ’yan kishin kasa da ke raye a wannan lokaci. Rayuwar marubuci, manazarci, mai yi wa al’umma hidima, Dokta Bukar Usman, abin nazari ce ga al’umma musamman masu tasowa su yi koyi da ita:
A jibi Lahadi (10-12-2017), fitaccen marubuci, dan kishin kasa kuma mai tallafa wa al’umma, Dokta Bukar Usman, OON yake cika shekara 75 a duniya, kasancewar ya zo duniyar nan ce a ranar 10 ga watan Disamba, 1942. Rana ce mai muhimmanci, musamman ba a kansa da iyalansa kadai ba, a’a rana ce mai muhimmanci ga daukacin al’umma, musamman idan aka yi la’akari da yadda wannan dan taliki, rayuwar tasa ta zama mai amfani ga al’umma ta fannoni da dama.
Shi al’amarin rayuwar duniya, ba yawan shekaru ne abin dubawa ba, shin me wannan lokaci ya kasance a rayuwar mai shi da kuma sauran al’umma? Ke nan idan za mu tambayi kanmu, tsawon shekarun Dokta Bukar 75 a duniya, shin wane tasiri rayuwarsa ta yi ko take kan yi ga al’umma? Abin da za mu duba ke nan, a yau.
Kamar yadda tarihinsa ya nuna, musamman kamar yadda ya zo a littafin tarihin rayuwarsa mai taken ‘Hatching Hopes’ (Cikar Buri), an haife shi ne a ranar 10 ga watan Disamba, 1942 a garin Biu, inda kuma a nan ne ya fara dandana madarar ilimi. Ya yi makarantar firamre a Biu, kamar kuma yadda ya fara makarantar sakandare a Biu. Daga karshe ya kammala karatunsa na sakandare a shahararriyar kwalejin King’s College da ke Legas. Haka ya ci gaba da neman ilimi, inda ya samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Ya kammala a shekarar 1969, inda ya samu digiri a Fannin Tafiyar da Mulki da Hulda da kasashen Waje. Bai tsaya nan ba, domin kuwa ya ci gaba da neman ilimi, inda ya yi digiri na biyu da na uku (Digirin-Digirgir), duk dai a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Idan muka duba gwagwarmayar rayuwarsa ta bangaren ilimi, Dokta Bukar ya zama abin misali. Yadda ya jajirce ya yi karatu, tun daga firamare har zuwa Digirin Digirgir, ya zama mai nuna ishara ga muhimmancin ilimi. Ga duk mai son ya samu nasara, irin tasa, to kamata ya yi ya zama mai koyi da shit a fuskar neman ilimi. Da ilimi ne ake samun fahimta, ake samun wayewa, ake samun arziki. Zaman kashe wanda ko zaman maula, mummunar ta’ada ce da ke kassara mutuncin mutum. Ke nan ba za ka zama mai amfani ga kanka ba, ba za ka zama mai amfanar jama’a ba sai ka kasance mai dogaro da jibinka. Ba za ka zama mai dogaro da jibinka ba sai ka kasance mai sana’a ko kuma ma’aikaci. Bisa haka, Dokta Bukar ya fara aiki a matsayin karamin jami’i a Gwamnatin Tarayya. Sannu a hankali ya yi ta samun karin girma har ya kai kololuwar girman da duk wani ma’aikacin ofis ke kaiwa. A shekarar 1999 ce ya yi ritaya daga aiki a Ofishin Shugaban kasa da mukamin Babban Sakatare (Permanent Secretary).
Kamar yadda masu iya magana suka ce, idan ka ji wane ba banza ba, kamar yadda suka ce, kowa ya ci zomo sai ya ci gudu. Rayuwar Dokta ta fannin neman halal, abin misali ce kuma abin koyi ce ga al’umma, musamman ma matasa. Abin da yake nuna mana shi ne, idan kana son nasara, to ka kama aiki ko sana’a kuma kada ka raina matakin da ka fara da shi. Shi ya fara daga karamin ma’aikaci amma saboda himma da kwazo da maida hankali, bai samu nakasu ba har sai da ya kai kololuwa.
Karatu da rubutu wasu abubuwa ne guda biyu da babu kamarsu wajen tallafa wa dan Adam a dukkan rayuwarsa. Idan kana son fahimtar rayuwa kowace iri ce, sai ka yi karatu. To me za ka karanta? Ba za ka zama mai karatu ba sai mai rubutu ya samar da abin karantawa. Sai da karatu ne za ka fahimci addininka da yadda za ka bauta wa Allah. Sai da karatu ne za ka fahimci al’ummarka da yadda za ka zauna cikinta cikin lumana da karuwar juna. Sai da karatu ne za ka fahimci sana’arka ko kuma aikinka.
A rayuwar Dokta Bukar Usman ta shekara 75 a yau, ya kasance wanda Allah Ya hore masa wadannan baiwa biyu. Ya kasance mai yawan karatu da neman ilimi, kamar kuma yadda ya kasance marubuci. Marubuci ne ba na wasa ba, ba na sha’awa kadai ba. Marubuci ne da ya kasance mai amfanar jama’a da iliminsa a kowane fanni kuma a kowane lokaci.
A rayuwarsa, Dokta Bukar ya rubuta littattafai masu tarin yawa sama da guda 30 kuma yana ma kan ci gaba da rubutawa. Wasu daga cikin littattafansa sun hada da 1-The Interface of the Muse & Gobernment Protocol (Literature/Criticism), (Klamidas 1998). 2-Press, Policy & Responsibility (Media), (Klamidas 1998). 3-Democracy, Human Rights and National Stability (Political/Debelopment), (Klamidas 1999). 4-boices in a Choir: Issues in Democratisation and National Stability in Nigeria (Klamidas 1999). 5-Hatching Hopes, (Klamidas 2006). 6-Dreams and Realities, Issues in Nigeria’s Golden Jubilee Independence Annibersary (Klamidas 2010). 7-Bride Without Scars and Other Stories (Klamidas 2005). 8-The Stick of Fortune (Klamidas 2006). 9-Girls in Search of Husband and Other Stories (Klamidas 2006). 10-Taskar Tatsuniyoyi). Game da wannan batu, ga abin da Farfesa Ashraf El-Azzazi na Cibiyar Nazari Da Bincike-Bincike A Kan Afrika, Sashen Harsunan Afrika, bangaren Harshen Hausa, Jami’ar Alkahira, Masar da Malam Abdulrahman Ado na Sashen harsunan Najeriya, Tsangayar Nazarin Halayyar dan Adam, Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa, Katsina-Najeriya suka ce game da shi:
“Ba shakka, a duk lokacin da mutum ya buga littafi kuma ya watsa shi cikin duniya, to, ba zai san iyakar inda littafin nan zai je ba. Malam Bukar Usman na daya daga cikin mujahidai masu amfani da karfinsu da dukiyarsu a wajen neman watsa ilimi da adana shi cikin rubutu. To, amma kila zai yi mamakin cewar littattafansa, ana nan ana yin amfani da su wajen koyo da koyar da ilimin Hausa, a kasashen Larabawa, ba ma kamar a Misira.” (Daga littafin: Salon kwarewa A Cikin Harshen Hausa, shafi na di). Haka shi ma wani marubuci, manazarci kuma malamin makaranta, Khalid Imam ya bayyana cewa:
“A yau, ba batun kambamawa ba, Dokta Usman, dan asalin Biu, ya tabbatar wa duniya cewa shi kadai ne kogin marmaron da ke shayarwa da magance kishirwar da Adabin Hausa ke ciki. Abin mamaki, a matsayinsa na jigon Adabi, dinbin littattafansa sun samu amsuwa daga manyan malamai da dalibai a nan gida Najeriya da kasashen waje, wadanda suka samar da muhimman rubuce-rubucen ilimi daga gare su.”
Kamar yadda ni GIZAGO na san shi, Dokta Bukar Usman, ba bangaren ilimi kadai hidimarsa ga al’umma ta tsaya ba. Domin hidimta wa al’umma, na kusa da na nesa, wadanda ya sani da wadanda ma bai taba gani ba a rayuwarsa, ya kafa Gidauniyar Bukar Usman, wacce ta hanyarta yake tallafa wa al’umma da dukiyarsa. Wasu sun amfana ta hanyar biya masu kudin magani, wasu ta hanyar daukar dawainiyarsu ta karatu, wasu ta hanyar ba su jarin sana’a da sauran hanyoyin tallafi daban-daban. Mutum ne shi mai saukin kai, mai tawali’u da dogaro da kai. Mutum ne da ya samu shaidar zama da kowa lafiya. Ya samu shaida daga hukumomi da kungiyoyi daban-daban. A shekarar 2000, ya samu Lambar Yabo ta kasa OON. A shekarar 2014, Jami’ar Ahmadu Bello ta karrama shi da Digirin Girmamawa (Dr. Litt).
A yayin da a lokacin nan Allah Ya sanya ya cika shekara 75 a duniya, muna yi masa addu’ar Allah Ya kara masa lafiya da wadatar arziki. Ya albarkaci zuri’arsa, Ya kara masa azama da kwarin gwiwar ci gaba da tallafa wa al’umma.