Shekara daya da rasuwar M.D.Yusufu: Ban kwana da kundin tarihi mai rai
Makabartar dan takum da ke birnin Katsina ta samo asali ne daga wani malami masani addini musulunci kuma Waliyyi, mai suna Muhammad ibn Ahmad At Tazakhat.A nan ne aka rufe M.D. Yusufu.A gefen kabarinsa daga hannun dama kabarin mahaifiyarsa ne Hajiya Hadiza,wadda ta rasu shekaru goma da suka wuce.Daga hagu kuma kabarin yayarsa ce Hajiya […]
Makabartar dan takum da ke birnin Katsina ta samo asali ne daga wani malami masani addini musulunci kuma Waliyyi, mai suna Muhammad ibn Ahmad At Tazakhat.A nan ne aka rufe M.D. Yusufu.
A gefen kabarinsa daga hannun dama kabarin mahaifiyarsa ne Hajiya Hadiza,wadda ta rasu shekaru goma da suka wuce.Daga hagu kuma kabarin yayarsa ce Hajiya Akila.
Shi ya zabi wajen da aka rufe shekaru sha biyar da suka wuce.Kuma an ce wani lokaci ya kan kai ziyara wajen,yana kuma sawa a je ziyara wurin, wanda ya kira da sunan gidansa na karshe a duniya.
Daga bakin kabarin ta gabas za ka iya hango dakinsa da ke gidansa na Katsina,amma wani dogon bene da aka yi ya kare shi. Daga nan zuwa gidansa tafiya ce ‘yan mintuna a kasa.
Gidansa.yana unguwar da ake kira Yaranci, wadda Sarki Dikko ya kafa ta. Titin da gidansa yake, sunan kakansa ne aka sanya masa, watau Muhammad Dikko Road. Lamba na 49. Daga nan ana iya hangen gidan Mahaifinsa. Magajin gari Yusufu.
Gidan M.D Yusufu na Katsina an gina shi da konannen bulo (Red bricks). Duk Katsina shi ne aka fara ginawa da irin wannan bulo.Ginin bene ne hawa daya. A kasan benen, bangare daya dakin karatu ne.wanda littafan da ke ciki sun fi na babbar laburaren jahar Katsina. Wani dakin kuma jaridu ne iri-iri na tsawon shekaru,wadanda aka hada su littafi-littafi, su ma sun cika dakin.Sai dan wajen da yake ganawa da mutane,wanda bai iya daukar mutum goma lokaci guda.
A gidansa na Legas,littafai da jaridu da muhimman takardu ne suka canye kashi biyu cikin uku na gidansa. Tirela-tirela aka rika cikawa ana kai wa Cibiyar Yusufu Bala Usman da ke Zariya, a lokacin da zai baro Legas da zama.
A gidansa na Abuja ma tun daga falonsa, Litattafai da jaridu ne kewaye da shi.daya daga cikin ‘ya‘yansa rasa daki ya yi, sai dai ya rika rabawa a dakin karatu yana kwana.
Duk wani littafi da ya zo masa sai ya karanta shi. Idan kuma ya ji labarinsa zai sa a nemo masa ya karanta.Babu wani littafi da aka rubuta wanda ya shafi Najeriya ko Afirka da bai da shi, sai dai idan marubucin in wani dan dagaji ne. Idan littafi ya fito ya karanta za ka ji yana sharhin cewa, abin da marubucin ya fada haka ne ko kuwa da kuskure.Wani lokaci ya kan buga wa marubucin waya ya ce na ga littafi kaza, amma abu kaza da kaza a cikin littafin ba haka ba ne.
Duk wadansu muhimman abubuwan da suka faru a tarihin Najeriya a gabansa aka yi, yana da cikakkiyar masaniyar yadda aka yi. Idan kana magana da shi zai ba ka misalai na shekaru hamsin, ya rika gangarowa har zamanin da kuke,sai ya yi sharhi ya kuma fitar da mafita.
Manyan shaihunan ilmi tarihi a kasar nan sun sallama cewa shi wani tushe ne wanda za ka san gaskiyar me ya faru a tarihin siyasa da mulkin Najeriya. Shaihunan malamai irinsu. Farfesa Abdullahi Mahdi, shugaban jami’ar jahar Gombe da Farfesa Alkasum Abba, shugaban jami’ar jahar Adamawa da Dakta Abubakar Saddik na jami ar ABU Zariya da Dakta Patric Wilmot, kadan ne daga cikin shaihunnan malaman da suka sallama masa.
Ba ya tarayya da kowa sai wanda ya san ciwon kansa ko ya san abin da yake yi ko mai wani kyakykyawan guri da alkibla. Duk wasu masana da manazarta a kasar nan sun san da zamansa. Idan kuma ya dauke ka domin ku yi tafiya tare,ba ya nuna bambanci,ya kan ce ka koyi mu’amala da manya don wata rana ba sa nan, kai ke nan.
Na taba samun kaina muna mitin a waje guda lokaci guda a shekarar 2002, ga marigayi Dakta Yusufu Bala Usman ga marigayi Farfesa Sam Aluko ga Malam Sani Zoro ga dakta Abubakar Saddik. Na kalliteburin, na kalli kaina, na kalli wanda ya tara mu marigayi M.D.Yusufu. Da jikina ya yi tsami sai na dauko biro da takarda na rubuta dan wake, kamar haka:
In an tambaye ki ina ina?
Fada masu ina a cikin giwaye
Fada masu ina tsakiyar zakoki,
Fada masu ina gaban dakaru
Fada masu na zama jinjiri ana mani tatata.
Fada masu ina a wani zama na tarihi.
A gabana marigayi Uche Chukumeiriji a lokacin yana Sanata, ya zo aka tsara yadda za a wargaza shirin da wasu ke yi na kawo tazarcen Obasanjo a Majalisar dattawa. Idan aka tattauna sai a dawo wajen M.D.Yusufu, wani lokaci ya soke duk tsarin da aka yi ya sake sabo,wani lokaci kuma ya canza masa fasali. Sai na sake wani rubutun kamar haka:
Tarihi yana aukuwa ne da mutane.
Tarihi yana faruwa ne da bigire,
Tarihi yana aukuwa ne da lokaci.
Tarihi yana da ‘yan taka rawa da kuma ‘yan kallo.
A inda nike tarihi ne zai faru.
A wurin ina kallo,ina taka rawa da bayar da rowan sha da kuma gurzo takarda. Ina daukar darasin da babu wani aji da za a iya samunsa.
M.D. Yusufu mutum ne mai karfafa gwaiwar adana tarihi da bincike,wannan ya sanya ya sha daukar nauyin assasa wajen adana kayan tarihi da bayanan tarihi. Ya yi tsaye wajen ganin an gina Cibiyar Yusufu Bala Usman da ke Hanwa Zariya.
Idan ya ba ka littafi zai tambaye ka me ka fahimta. Idan ka kawo masa littafi zai tabbatar ya karanta, idan akwai abin gyara a ciki ya gyara.
Ya taba ba ni aron littafi,bayan wani lokaci ya bukaci abinsa. Ina Katsina ya sanya na hau jirgi na kai masa a Legas. Ya ce hau jirgi ka koma gida. Na ce masa yallabai littafin fa Naira uku aka saye shi,sai ya ce idan za ka samo mun shi a kasuwa zan saya Naira dubu 500.Ya ce, ai babu inda za ka sameshi ko nawa ne. Ya ce, kana lissafin kudin jirgi ne da tasin da ka hau,ni kuma ina lissafin idan ya sallwanta ina zan samo shi? domin wanda ya rubuta shi ya mutu, kamfani kuma babu shi. Ko a lokaci kwafi dari biyar kacal aka buga.
A shekarar 2013 da na ce masa za mu kafa cibiya mai suna: M.D.Yusufu Research and Documentation Centre.sai ya kura mani idanu, sannan ya ce idan kun ga ya dace to Allah Ya ba da sa’a, taku ce. Don ni tawa ita ce Yusufu Bala Usman Centre da ke Zariya.
Ganina na karshe da shi, shi ne lokacin da na je gidan ya ce in dauki wata mujjala mai suna The Atlantic, ya ce, ‘je ka karanta da safe mu tattauna a kan labarin da suka kawo.’
M.D.Yusufu ya tafi ya bar tarihi jibge a cikin dimbin littafai da kuma tarin takardun da ya bari.Amma tarihin da ya tafi da shi a kwakwalwarsa yana da yawan gaske. Allah Ya jikansa.
danjuma Katsina Marubuci kuma danjarida. 08035904408. email mdanjumakatsina@gmail .com