Shekara daya na mulkin Shugaba Trump

Shugaban Amurka na yanzu Donald JohnTrump ya kama mulkin Amurka ne a cikin shekarar da ta gabata, bayan nasarar bazatar da ya yi na buge abokiyar karawarsa ta jamiyyar Democrat wato Hillary Clinton a zaben da ya bai wa ba Amurkawa duniya mamaki. Trump sanannen dan kasuwa ne, ba a cikin Amurka ba, har da […]

Shekara daya na mulkin Shugaba Trump

Shugaban Amurka na yanzu Donald JohnTrump ya kama mulkin Amurka ne a cikin shekarar da ta gabata, bayan nasarar bazatar da ya yi na buge abokiyar karawarsa ta jamiyyar Democrat wato Hillary Clinton a zaben da ya bai wa ba Amurkawa duniya mamaki.

Trump sanannen dan kasuwa ne, ba a cikin Amurka ba, har da wasu kasashen  duniya. Kuma fitaccen mai gabatar da shirin talabijin ne.

Sai dai idan ka cire harkan  kasuwanci, Trump ko kansila bai taba  rikewa ba balle ace magajin gari ko  kuma gwamna. Wannan takarar shugaban kasar ita ce takara ta farko a harkan zabe. Kila wannan ya sa yace aikin shugaban kasar zai iya canza  tunanensa da wasu abubuwa da ke da nasaba da tunanensa  a harkan shugabanci.

Ya ce gwamnatin da zai jagoranta, gwamnati ce ta canji tare da ganin harkokin mulki sun tafi ba tare da matsala ba.

  Akwai lokacin yakin neman zabe, shugaba Trump ya ce Amurka ba za ta yi shugaba kamarsa ba idan aka cire shugaba marigayi Abraham Lincoln.

Ya yi alkawurra da dama kafin ya kama mulKi, kama daga batun gina katanga tsakanin Amurka da Medico zuwa shigowar bakin haure da  batun wasu kasashen Musulmai da yake musu kallon su ne matsalar tsaro a  Amurka da ma sauran sassan duniya. Sai  kuma batun  samar da  kiwon lafiya mai rahusa da shugaba Obama ya yi dama wasu da bai bayyana ba.

Da farkon fara mulkinsa, sai ya fidda sanarwar hana wasu ‘yan kasashe  6  wadanda  yawanci  na musulmi ne, amma kafin kace me  jama’ar kasar suka yo  ca a kansa, wanda  har wasu alkalai da lauyoyi suka maka shi a kotu , wannan ya sa wannan dokar ba ta yi tasiri ba.

Ana gama wannan kuma, sai ga batun sallamar shugaban Hukumar FBI, James Comey, nan ma ya sha suka, amma ya doge a kan wannan.

An gama batun korar Comey ke nan,  sai  kuma ya jaddada batun rushe tsarin kiwon lafiya wanda aka samar lokacin Shugaba Obama, wanda hatta ‘yan jam’iyyarsa ba su amince da rusa tsarin ba. Haka kuma batun gina Katanga tsakanin Amurka da Medico da suke da iyaka,  nan ma bai ji da dadi ba, domin an jefa wannan batun cikin kwandon shara, sai kuma gyara dangantakar Amurka  da Cuba wanda Tsohon Shugaba Obama ya yi, inda yanzu haka gwamnatin ta Trump  ta janye wasu ma’aikatar ofishin jakadancin Amurka da ke Cuba.

Sai batun yaran da aka shigo da su suna kanana wadanda shugaba Obama ya ba su damar ci gaba da zama, shi ma ya mika batun ga majalisa yana bukatar ta dakatar da wannan tsarin. Sai kuma batun sasantawa da gwamnatin  Obama ta yi da kasar Iran a kan batun sarrafa makaman nukiliya, shi ma ya sa kafa ya yi  fatali  da shi.

Misali, Maria Liasson ta ce mutum ne wanda  ba ya komai sai haifar da rudani  ga mutanen da yake shugabanta. Ta ce shugaban kasar Amurka tun daga shekarar  1940 zuwa  shekarar  2017 ana kallonsa ne tamkar shugaban duniya, ba  wai  domin yawan makamai ba, a’a sai dai  domin karamci, da dattakon shugaban.

Amma wani masanin tarihi ya ce shugaban na Amurka na yuanzu akasin wadannan halayyar yake da su.

Doglas Brinkley wani marubuci da  ya rubuta littafi akan shugabannin da suka hada da Gerald Ford, John F.Kenedy, da kuma Jimmy Carter, ya ce kusan ko wane shugaba yana sukan lamirin ‘yan jarida,  amma ba kamar yadda Trump ya yi ko  kuma yake yi ba.

Brinkley ya ce shugaba Richard Nidon ya dauki lokaci suna takon saka da ‘yan jarida, amma bai zake ba tare da fitowa fili yana sa-in-sa da ‘yan jarida kamar yadda Shugaba Trump ke y. Ya ce shugaba Trump shi da kansa ke bai wa ‘yan jarida amsar duk wani bayani da yaji wanda bai ji dadinsa ba, sabanin wadanda  suka gabace shi.

Shi ko William Inboden, malami a Jam’iar Tedas, cewa ya yi, Shugaba Trump  ya  kauce daga tsarin shugabannin da suka gabace na mikawa shugabannin jam’iyyar wasu daga cikin manufofinsa a kaikaice, yadda za su samu tsallakewa  idan  sun isa  fadar  majilisa  domin muhawara. 

Wasu mutane sun ce maimakon ace ya zama uba wanda ‘yaya za su yi koyi da shi, sai ya zama kiri-kiri yake fitowa yana fada wa mutane.To sai dai da yake ba zai iya  sauya tsarin da ya yi tasiri shekara da shekaru ba, shi ya sa hakan bai taba cimma nasara ba.