Yaƙin Gaza: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 41,000 ta sa 2.5m gudun hijira a shekara guda

Ɓarnar da aka yi a Zirin Gaza cikin shekara guda na yaƙin ƙungiyar Hamas da ƙasar Isra’ila

Yaƙin Gaza: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 41,000 ta sa 2.5m gudun hijira a shekara guda

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa sama da 41,000 a Zirin Gaza a shekara guda, daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Hare-haren bom ɗin da tankoki da jiragen yaƙin Isra’ila suka kai Zirin Gaza sun raba Palasɗinawa sama da miliyan biyu da dubu ɗari huɗu da muhallansu.

Ma’aikatar Lafiyar Falsɗinawa a Zirin Gaza ta ce, kananan yara da mata da tsofaffi ne mafi yawan mutanen da sojin Isra’ila suka kashe a munanan hare-haren da suka kai ta kasa da kuma ta jiragen yaƙi ta sama da kuma ta ruwa.

A yayin hare-haren na sojojin Isra’ila, asibitoci da wuraren ibada da tantuna da sansanonin ’yan gudun hijira da makarantun da fararen hula suke zaman mafaka da sauran wuraren taruwar jama’a da abubuwan more rayuwa da ba su tsira ba.

Shekara guda da fara yaƙin Isra’ila da ƙungiyar Hamas, lamarin na neman mamaye yankin Gabas ta Tsakiya gaba ɗaya.

A halin yanzu dai yaƙin ya ɗauki sabon salo, inda saura ƙiris a fara musayar wuta kai-tsaye tsakanin Isra’ila da ƙasar Iran, babbar mai goyon Hamas.

Tuni dama ƙungiyar Hizbullah da ke ƙasar Lebanon da mayaƙan Houthi na ƙasar Yaman waɗanda dukkansu ke samun goyon bayan Iran suka shigar wa Hamas a yaƙin.

A yayin wannan yaƙi da aka faro ranar 7 ga Oktoban shekarar 2023 ke cika shekara guda, ana gudanar da maci a sassan duniya da kiraye-kirayen kawo ƙarshen zubar da jini a Gaza.

Hamas a Gaza

Hamas dai na rike da yankin Gaza tare da gudanar da cibiyoyinta tun shekara ta 2007, kuma  ta lashe zaɓen majalisar dokoki shekara guda da ta gabata tare da murƙushe abokiyar hamayyarta, Fatah.

Yanzu, yawancin cibiyoyin Gaza ko dai sun lalace ko kuma sun lalace.

Isra’ila na zargin Hamas da amfani da makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya da sauran kayayyakin more rayuwa na farar hula wajen gudanar da ayyukan soji, zargin da Hamas ta musanta.

Illar Rikicin

Yakin bai bar wani yanki na Gaza da ya tsira daga harin bam ba.

Dubban ɗaruruwan yara ne ba su je makaranta ba kusan shekara guda, yayin da jami’o’i da na’urorin samar da wutar lantarki da tashoshin ruwa da kuma ofisoshin ’yan sanda suka daina aiki.

A tsakiyar shekara ta 2024, tattalin arzikin Gaza ya ragu zuwa “kasa da kashi shida na matakin 2022,” in ji wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya.

Rahoton ya nuna za a ɗauki “shekaru goma kafin a dawo da Gaza” zuwa yadda take kafin Oktoba 7, 2023.

A ranar 24 ga Nuwamba, an tsagaita wuta na mako guda tsakanin Isra’ila da Hamas.

Kungiyar Hamas ta saki Isra’ilawa 80 da ta yi garkuwa da su a a yayin da Isra’ila ta sako Falasdinawa 240 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila.

Haka kuma an kuɓutar da wasu mutane 25 da aka yi garkuwa da su, galibinsu ma’aikatan gona ne na kasar Thailand.

Muhimman lokuta 10

A yayin da wannan yaƙi ke cika shekara guda, ga jerin wasu muhimman abubuwa:

1- Harin 7 ga Oktoba

Da asubahin ranar 7 ga Oktoba, 2023 daruruwan mayakan Hamas suka kutsa cikin Isra’ila a wani wa mai hari da Isra’ila ba ta gani ba, suka hallaka mutane 1,205, akasarinsu fararen hula suka kuma yi awon gaba da wasu 251 zuwa Zirin.

Mayakan Hamas sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya kan kisan gilla da cin zali da kwace filaye da yankunan Palasdinawa da gwamnatin Isra’ila ta shafe sama da shekaru 40 tana yi a Zirin Gaza.

Hukumomin Isra’ila sun ce daga cikin mamatan har da wadanda suka mutu a hannun Hamas, sannan har da gawarwaki a cikin mutane 251 da kungiyar ta yi garkuwa da su a Gaza.

Zuwa wannan lokaci dai mutum 70 daga cikin fursunonin yakin sun mutu, Hamas ta sako 117 a yayin da take ci gaba da rike ragowar, 64.

Tun a wancan lokaci Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya lashi takobin kawar da kungiyar Hamas daga ban-kasa.

2- Ƙaddamar da Hare-haren Isra’ila ta Kasa

Sojojin kasan Isra’ila sun kaddamar da hare-haren bom da mummunan samame a Gaza, inda a ranar 13 ga Oktoba, 2023 suka umarci fararen hula da ke Arewacin Gaza su koma Kudanci.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan mataki ya mayar da Falasɗinawa miliyan biyu da dubu 400 ’yan gudun hijira.

A ranar 27 ga watan sojojin Isra’ila suka kaddamar da hare-hare ta kasa, inda a ranar 15 ga watan Nuwamba suka kai hari a asibiti mafi girma a Gaza, wato Asibitin Al-Shifa, bisa zargin Hamas na amfani da asibitin a matsayin cibiyar gudanarwar harkokin soji, zargin da kungiyar ta musa.

3- Tattaunawa da musayar fursunoni

Ranar 24 Nuwamba, 2023 yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda tsakanin Isra’ila da Isra’ila ta fara aiki.

A lokacin ne kungiyar ta sako mutane 80 da ta yi garkuwa da su, Isra’ila kuma ta sako Falasdinawa 240 da take tare da su a kurkuku.

Isra’ila ta kuma sako wasu ma’aikatan Palasdinawa 25 da ta yi garkuwa da su, wadanda galibinsu ma’aikata ne a wani gidan gona.

Sannan ta ba da karin damar shigo da kayan jinƙai Gaza, ta kasar Masar

Amma duk da haka, akwai tsananin bukatar kayan jinkai a Gaza.

Bayan kwarewar yarjejeniyar, Isra’ila ta fadada hare-harenta zuwa Kudancin Gaza, yankin a baya ta umarci fararen hula su koma.

4- Tsaikon Kayan Agaji

A ranar 29 ga Fabrairu, 2024, Ma’aikatar Lafiyar yankin Gaza ta sanar cewa sojojin Isra’ila sun harbe Falasdinawa 120 har lahira a Arewacin Gaza, a lokacin da fararen hulan suka nufi wata babbar motar kayan agaji domin su karbi abincin tallafi.

Amma Isra’ila ta bayyana cewa sojojinta sun ga masu zuwa karbar agajin ne a matsayin ‘barazana’ a garesu.

A farkon watan Maris kasashen duniya da dama suka jefa kayan jinkai ta jiragen sama Gaza.

A ranar 15 ga watan jirgin ruwan kayan agaji na farko daga kasar Cyprus ya iso.

A ranar 1 ga Afrilu, 2024 harin Isra’ila ya kashe wasu ma’aikata bakwai na kungiyar jinkai bakwai kasar Amurka, mai suna World Central Kitchen.

Sojojin Isra’ila sun bayyana harin a matsayin ‘kuskure mai ban takaici’.

5- Rikicin Isra’ila da Iran

Ranar 13 ga Afrilu jirage marasa matukan Iran suka yi wa Isra’ila ruwan bama-bamai, a matsayin raguwar gayya kan harin da aka kai wa ofishin jakadancinta da da ke birnin Damascus na ƙasar Syria, wanda take zargin Isra’ila.

Sai dai Isra’ila ta yi ikirarin kakkabo mafi yawan bama-baman.

6- Hare-haren Kudancin Gaza

Ranar 7 ga watan Mayu Isra’ila ta kaddamar da hare-hare ta kasa a yankin Rafah a Kudancin Gaza, inda yawancin Palasdinawa suke zaman mafaka.

Sun kuma kwace ikon mashigar kasar Masar daga Gaza tare da hana shigo da kayan agaji zuwa Gaza.

Haka kuma sun kai hare-hare a sansanonin ’yan gudun hijira da tantuna da makarantu Palasdinawa ke zaman mafaka.

Ranar 13 ga Yuli Isra’ila ta yi ikirarin kashe shugaban bangaren sojin kungiyar Hamas, Mohammed Deif, a Kudancin Gaza.

7- Yamusti a Gabas ta Tsakiya

Mayaƙan Houthi na kasar Yaman, wadanda ke samun goyon bayan Iran, sun yi ta kai jiragen ruwa hare-hare a Tekun Bahar Maliya da Aden domin nuna goyon bayansu ga Palasdinawa.

20 ga watan Yuli Isra’ila ta kai musu harin ramuwar gayya kan harin jirage marasa matukan Houthi suka kai wa birnin Tel Abib, babban birnin Isra’ila.

A kan iyakar Isra’ila da kasar Lebanon kuma, musayar wuta s ake yi kusan kullum tsakanin dakarun Isra’ila da mayakan Hizbullah da ke da goyon bayan kasar Iran, ta tsananta.

Ranar 27 ga watan Yuli harin rokoki ya kashe kananan yara 12 a yankin Tuddan Golan da ke karkashin ikon Isra’ila; Hizbullah ta nesanta kanta da harin.

An kashe babban kwamandan Hizbullah, Fu’ad Shukr a wani harin ramuwar gayya da Isra’ila ta kai birnin Beirut na kasar Lebanon.

Washegari aka kashe Shugaban Siyasar Hamas, Ismail Haniyeh, a wani hari a birnin Tehran na kasar Iran, inda ya je halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar. Iran ta zargi Isra’ila da kai harin.

Daga bisani Hamas ta nada Yahya Sinwar a matsayin magajin Ismail Haniyeh.

8- Tattaunawar Zaman Lafiya

Amurka ta gabatar da sabon tayin yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 16 ga watan Agusta, amma nan take Hamas yi farali da shi. A ranar 22 ga watan kuma aka ci gaba da tattaunawar da kasar ta fara jagoranta kafin kasar Katar.

Ranar 25 ga watan Agustan kuma Isra’ila ta yi ikirarin dauke wani gagarumin harin Hizbullah, da hare-haren da ta kai ta sama zuwa cikin kasar Lebanon.

Hamas kuma ta ce ta yi nasarar harba daruruwan rokoki zuwa cikin Isra’ila.

9 – Here-haren Yammacin Kogin Jordan

28 ga watan  Agusta 28, Isra’ila ta kaddamar da wani babban harin soji kan mayakan Palasdinawa a yankin Yammacin Kogin Jordan West Bank.

Amma Majalisar Dinkin Duniya ta nemi Isra’ila ta dakatar da hare-haren nan take.

Bayan sojojin Isra’ila sun gano gawarwakin shida daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da suna Gaza,  a ranar 31 ga watan  Agusta gwamnatin kasar ta fuskanci matsin lamba cewa ta kubutar da ragowar wadanda Hamas ta yi garkuwa da su. Amma duk da haka shuagaban kasar Benjamin Netanyahu bai mayar da hankali kan sulhu ba.

10- Hare-haren Lebanon

Rabar 17 da 18 ga Satumba wayoyyin daruruwan mayakan Hizbullah suka yi ta yin bindiga  tare da sanadin mutuwar mutane 39 da jikkata wasu kimanin 3,000 a Lebanon,.

Isra’ila ta sanar cewa za ta fadada yakinta a Gaza domin kwace yankin Arewaci da ke makwabtaka da Lebanon. Sai kuma ba ta dauki alhakin abin da ya faru a Lebanon ba.

A yayin da take ci gaba da hare-hare kan Hizbullah, a ranar 27 ga Satumba Isra’ila ta kashe shugaban kungiyar, Sayyid Hassan Nasrallah tare da wabi Janar din Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran a birnin Beirut.

Shugaban Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya sha alwashin cewa jina Nasrallah ‘ba zai tafi a banza ba’.

Ranar 1 ga watan Oktoba Rundunar Juyin Juya Halin Musuluncin Iran ta yi wa Isra’ila ruwan makamai masu linzami a matsayin ramuwar gayya kan kisan Ismail Haniyeh da Hassan Nasrallah.

Rundunar ta harba makaman ne a ranar da Isra’ila ta sanar da kai wasu hare-hare kan Hizbullah a Kudancin Lebanon.

An kashe da mutane 1,900 a Lebanon daga lokacin da Hizbullah da Isra’ila suka fara musayar wuta da Isra’ila a watan Oktoban shekarar 2023.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya