Shekara hudu da sace ’yan matan Chibok, shin gwamnati ta yi kokari?
Shugaba Buhari ya yi rawar gani – Muhammad Fayama Daga Abbas dalibi, a Abeokuta Muhammad Fayama Jarimi: “A ra’ayina Shugaba Buhari ya yi rawar gani a yunkurin gwamnatinsa na kubutar da ’yan matan da ’yan ta’addan Boko Haram suka kame dama sauran mutanen da aka yi garkuwar tare da suka, duk da dai yau shekaru hudu […]
Shugaba Buhari ya yi rawar gani – Muhammad Fayama
Daga Abbas dalibi, a Abeokuta
Muhammad Fayama Jarimi: “A ra’ayina Shugaba Buhari ya yi rawar gani a yunkurin gwamnatinsa na kubutar da ’yan matan da ’yan ta’addan Boko Haram suka kame dama sauran mutanen da aka yi garkuwar tare da suka, duk da dai yau shekaru hudu da yin garkuwa da ’yan matan Chibok kuma har yanzu akwai ragowarsu a hannun Boko Haram za mu jinjinawa gwamnatin Buhari bisa kokarin ta na ceto da yawa daga cikin zullumi, dama kudirin sa na ceto ragowar su.”
Buhari ya yi kokari – Alhaji Sulaiman Ismaila Adam Umar, Abuja
Alhaji Sulaiman Ismaila Ajingi: “Gwamnati musamman ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda gadon matsalar ta yi, ta yi kokari matuka ta fuskar jami’an tsaro da kuma difilomasiyya wajen gano wadannan ’yan mata. Kowa ya san yadda shugaban kasa ya zagaya kasashen da ke makota da mu da hawansa mulki don toshe kafofin da ’yan ta’addan nan ke samun makamai, sannan a gefe guda ya rungumi tafarkin sasantawa da su don ganin wadannan ’yan mata sun komo ga iyayensu lafiya, inda a sakamakon hakan sun sako sama da ’yan matan Chibok 100 sannan wasu kamar sittin sun samu damar tserewa.”
Gwamnati ta tabuka – Alhaji Umaru Namashaya
Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi.
Alha Umaru Namashaya Diggi: “A nawa ra’ayin gwamnatin APC ta yi abin a zo a gani wajen dawo wa ’yan matan chibok, wanda wannan ya nuna cewa gwamnatin Muhammadu Buhari da gaske take yi wajen mai do da duk wadanda Boko Haram ta sace, ba ma wai kawai ‘yan matan chibok kadai ba. Amma gwamnatin da ta shude ba da gaske ta yi ba, illa dai kawai ta fidda kudaden al’umma ne don amfanin kansu, ba wai don yaki da Boko Haram ba ko don su kwato ’yan matan chibok. Domin har gwamnatin Jonathan da ta wuce ba su kwato yarinya ko guda ba, sai da gwamnatin Buhari ta zo ne suka fara maido da ’yan matan Chibok, ka ga wannan ba karamar nasara ba ce gwamnatin APC da kuma iyayen ’yan matan Chibok.”
Ta yi kokari sosai – Malam Rabi’u Yunusa
Daga Abbas dalibi, a Legas
Malam Rabiu Yunus Kura: “Alal hakika Shugaba Buhari ya yi kokri sossai ba ma ga kubutar da ’yan matan Chibok kawai ba hatta yakin da wannan gwamnati ta yi da ’yan Boko Haram a shekarun uku na mulkin ta dole ne a yaba mata duba da nasarorin da ta samu cikin kankanin lokaci, duk dai har yanzu akwai ragowar ’yan matan Chibok a wajen ’yan Boko Haram shekaru hudu da yin garkuwa da su, hakan ba zai sa aki yaba masa domin ya da aniyar ceto ragowar ’yan matan.”
Gwamnati ba ta yi kokari ba – Malam Ibrahim Tanimu Adam Umar, Abuja
Mallam Ibrahim Tanimu: “A gaskiya gwamnati ta gaza idan aka yi la’akari da tsawon lokaci da lamarin ya dauka da kuma adadin wadanda ta samu nasarar kubutarwa daga hannun ’yan ta’adda. Duk da dai ba a zamanin wannan gwamnatin ne a ka sace ’yan matan ba, sai dai irin burin da ’yan Najeriya ke cike da shi a kan gwamnatin na magance matsalar tsaro wanda shi ne babban dalilin da ya sa a ka zabeta, to wajibi ne ta kara zage dantse a kan daukacin lamarin tsaron ba ma a kan na ’yan matan Chibok ba, sannan Jagororin tsaro na gwamnatin su hada kansu wajen yakar matsalar a maimakon gasa a tsakaninsu ko rashin taimakawa juna da bayanai da kuma kawo dauki.”
Gwamnati ta yi kokari kwarai – Alhaji Bilya Doya Zauro
Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi.
Alhaji Bilya Doya Zauro: “Ya zama wajibi a yaba wa wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari wajen dawo da wadansu daga cikin ’yan matan Chibok da wannan gwamnati ta yi, domin kuwa a lokacin da aka sace ’yan matan a lokacin wancan gwamnatin Jonathan ba ta iya tsinana komai ba. Ya kamata a ce wancan gwamnatin c eta ceto ’yan matan, amma in banda sharholiya da kudin makamai babu abin da ta tsinana a kan Boko Haram saboda haka wannan gwamnati ta yi abin a yaba mata.”