Shekara hudu ta yi kadan wajen gyara wutar lantarki a kasar nan – Fashola
Ministan Wutar Lantarki da Ayyuka da Samar da Gidaje, Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa ‘shekara hudu ta yi kadan don a gyara wutar lantarkin kasar nan,’ inda duk da matsalolin da suke fuskanta a yanzu an samar da megawat 7001. Ministan ya fadi hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi yayin taro […]
Ministan Wutar Lantarki da Ayyuka da Samar da Gidaje, Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa ‘shekara hudu ta yi kadan don a gyara wutar lantarkin kasar nan,’ inda duk da matsalolin da suke fuskanta a yanzu an samar da megawat 7001.
Ministan ya fadi hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi yayin taro kan inganta wutar lantarki a otal din Crest Hotel da ke Jos.
Ya ce ga masu cewa ya kamata a soke batun sayar da kamfanin wutar lantarki da gwamnati ta yi, to su sani shi bai goyi baya ba.
Ya ce, “Na san har yanzu akwai matsaloli da suka sha kan batun wutar lantarki duk da sayarwar da aka yi, ina so su sani cewa wutar lantarki ba za ta gyaru a shekara hudu ba, wadannan shekaru na gyara ne, dole akwai ayyukan da suka kamata mu yi kafin mu ce hakar sayar da wutar lantarki ta cimma ruwa. Shekaru hudu sun yi kadan, domin mun shafe fiye da shekara 60 wajen gyara wutar lantarki.”
Ya ce, “Bari in kara tuna mana batun sayar da kamfanin wutar lantarki, abin da ya rage a hannun gwamnati kadan ne, idan aka kwatanta wanda yake hannun masu zaman kansu, mu dai rawar da za mu taka a matsayinmu na gwamnati a matakin ta tarayya da jihohi, ita ce mu dauki kyawawan matakai don tabbatar da an bi dokar da wutar lantarki za ta inganta. Kuma wadannan dokoki tuni suna cikin dokar wutar lantarki lokacin da aka kai ga batun sayar da kamfanin wutar lantarki na kasa.”
Ya ce, wadansu sun ce a soke batun sayarwar, to shi bai yarda da hakan ba, inda yake da dalilai masu yawa a kan hakan, “amma dai a yanzu abin da zan ce, shi ne, ina so dukkanmu mu tuna cewa bayan an sayar da kamfanin wutar lantarki, gwamnati ta karbi kudi daga wurin wadanda suka saya, wannan kudi kuwa a Dala ta karba, a lokacin da kowace Dala take kimanin Naira 165, kuma abin da gwamnati ta yi da kudin shi ne, ta biya ma’aikatan kamfanin lantarki, kuma na sani yawancin ma’aikatan sun samu kudadensu, wadansu miliyoyi, inda zuwa yanzu kadan daga cikinsu ne ba su samu ba.”
Ya ce yanzu idan gwamnati ta amince ta soke batun sayarwar, abin da za ta yi shi ne, ta mayar da kudin da aka ba ta, “tun da a Dala ne, dole sai mun nemo Dala mun biya su, inda yanzu kuma Dala ta nunka. Ya kamata mu yi tunanin hakan. Kada mu manta mun sayar da matatar mai a shekarar 2006 a kan kudi Dala miliyan 700, inda muka soke ta, sannan muka biya kudin, inda har zuwa yau muna kan shigowa da mai kasar nan.”
Ya bayyana cewa a yanzu sun fito da wani shiri da yake dauke da tsare-tsare da matakai da hanyoyin da za a inganta wutar lantarki a kasar nan, wadanda suka kunshi rarraba wutar lantarki, batun mitoci, batun sace-sace kayan wutar lantarki da sauransu.
“Inda a yanzu mun samar da wutar lantarki a kasar nan da ya kai megawat 7001, wannan alkalamin mun dauke shi a ranar 12 ga Satumba, 2017 ke nan, inda aka rarraba megawat 6700, duk da haka ba za mu ce ya isa ba.” Inji shi.
Ya ce a yanzu haka gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da kwangilar tashar samar da wutar lantarki ta Mambila wadda za ta samar da megawat 3050 a kan kudi Naira Tiriliyan 1 da miliyan 400, inda aka fara aikinta tun shekara 40 da suka wuce.