Shekara uku bayan rasuwar Rashidi Yekini iyalansa suna takaddama a kan rabon gado -Lauya Jubril Olanrewaju Mohammed
Shahararren dan kwallon Najeriya Rashidi Yekini wanda ya rasu kimanin shekara uku da suka gabata yana daga cikin ’yan kwallon Najeriya da ba za a taba manta wa da shi ba. Tun bayan rasuwarsa kimanin shekara uku da suka gabata amma iyalansa sun kasa raba dukiyar da ya bari ga magadansa. Sai dai Lauyansa mai […]

Shahararren dan kwallon Najeriya Rashidi Yekini wanda ya rasu kimanin shekara uku da suka gabata yana daga cikin ’yan kwallon Najeriya da ba za a taba manta wa da shi ba. Tun bayan rasuwarsa kimanin shekara uku da suka gabata amma iyalansa sun kasa raba dukiyar da ya bari ga magadansa. Sai dai Lauyansa mai suna Jubril Olanrewanju Mohammed ya ce a wasiyyar da Yekini ya bar masa ya nuna yadda mamacin ya umarce shi ya raba dukiyar tasa a tsakanin ’ya’yansa mata biyu da ya bari watau Yemimi ’yar shekara 20 da kuma Mariam ’yar kimanin 15 amma wasu daga cikin ’yan uwansa suke neman kawo cikas ga yin haka. A tattaunawar da Lauyan ya yi da manema labarai ya tabo batutuwa da dama. Wakilin Aminiya ya yi kicibis da tattaunawar da aka yi da Lauyan a Turanci a yanar gizo kuma ya fassarawa masu karatunmu kamar haka:
Fassarar Ahmed Garba Mohammed
Tambaya: Za mu so ka gabatar mana da kanka?
Lauya: Sunana Jubril Olanrewaju Mohammed. Ni ne Lauyan marigayi Rasheed Yekini kuma mai kula da daukacin dukiyarsa.
Tambaya: Yaya kake fama da gwagwarmayar kula da dukiyar mamacin kawo yanzu?
Lauya: Gaskiya ba abu ne mai sauki ba. Tun lokacin da mamacin ya bar mini amanar kula da dukiyoyinsa inda ya umarce ni in ya rasu in raba wa ’ya’yansa biyu mata watau Yemisi ’yar kimanin shekara 20 da kuma kanwarta mai suna Maryam mai kimanin shekara 15 da kuma mahaifiyarsa daukacin dukiyarsa nake ta kokarin yin haka. Amma abin mamaki wasu daga cikin ’yan uwansa sun ki yarda da batun raba gado ga ’ya’yansa da kuma mahaifiyarsa kadai, sun nemi su ma a raba gadon tare da su da hakan ta sa yanzu haka ake ta takaddama kuma na tsaya kai da fata sai an bi umarnin da mamacin ya bayar na ’ya’yansa biyu mata ne kawai da kuma mahaifiyarsa suke da alhali a rabon gadon.
Tambaya: Akwai rade-radin da ake bazawa cewa marigayi Yekini ya taba haihuwa da wata mata da ke zaune a kasar Togo, ko za ka yi mana karin bayani a kan wannan batu?
Lauya: Eh kwanaki takwas bayan rasuwar Yekini, an samu wata mata da ta taso tun daga kasar Togo zuwa Najeriya tare da wata yarinyar mai kimanin shekara uku da ta nuna marigayi Yekini shi ne mahaifinta. Da ma Yekini ya taba fada wa mahaifiyarsa da sauran ’yan uwansa cewa ya taba yin soyayya da wata mata a Togo amma ba su dade ba suka rabu. Don haka kafin rasuwarsa ta zo Najeriya inda ta shaida wa mahaifiyar Yekini tana dauke da cikinsa amma dan kwallon ya ki amincewa da haka inda ya nuna sam cikin ba nasa ba ne. Sai dai mahaifiyarsa a wancan lokaci ta amince da batun da matar ta kawo na cewa cikin na Yekini ne da hakan ya sa suka samu sabani a tsakanin Yekini a mahaifiyar tasa a wancan lokaci. Sai dai abin da ya daure wa iyalan kai shi ne yadda matar ba ta bayyana ba sai bayan ya rasu da kimanin kwanaki takwas tare da yarinyar ’yar kimanin shekara 3 inda take neman a raba gadon da ita. Hakan ta sa Lauyan tare da iyalan suka umarci da a ziyarci asibiti don yin gwajin tabbatar da ’yar ko ta marigayi Rashidi Yekini ce ko a’a ta hanyar yin gwajin jini watau (DNA) amma har yanzun da nake wannan hira matar da asibitin ba su gabatar da sakamakon binciken ba. Wannan na daya daga cikin abin da ya kawo tsaiko a wajen rabon gadon.
Tambaya: Mene ne cikakken bayani a game da dukiyar da Rashidi Yekini ya bari?
Lauya: Gaskiya wasu daga cikin iyalansa sun sha kirana a waya suna umartar na sayar da wasu daga cikin kadarorin da marigayin ya bari don a raba musu dukiyar. Ni kuma a matsayin Lauyan mamacin wanda ya bar wa wasiyyar cewa na raba dukiyar ce kawai ga ’ya’yansa mata biyu da kuma mahaifiyarsa sai na yi biris da wannan umarni. Don na san ko a shari’ar Musulunci bai dace a sayar da daukacin kadarorin da mamacin ya bari ba kuma a raba kudin a tsakanin daukacin iyalansa alhali yana da ’ya’ya da kuma mahaifiya a raye. Hasalima Rashidi Yekini tun yana raye ya mallaka wa mahaifiyarsa wasu daga cikin gidajensa don haka ba daidai ba ne a ce na nemi kwace su daga wajenta a yanzu bayan ya rasu. Haka kuma sauran gine-ginen da suka rage a wasu wurare, mamacin bai yi takamaiman bayanin yadda ya kamata a raba su ba bayan wasiyyar da yaa yi. Ya mallaki wasu rukunin gidaje (mansion) da ya bari a Ibadan, kuma tuni muka mika su ga wadansu kamfanoni wadanda suka kware wajen kula da kadarori kuma daga cikin kudin ne ake kula da dawainiyar yau da kullum ta iyalansa da kuma na ’ya’yansa. Sannan wasu rukunin gidajen da mamacin ya mallakawa mafaiyarsa kuma ita ce take karbar kudin shigar kai tsaye don haka ba ni da ikon cewa wani abu a kan haka. Sannan Yeki ya mallaki wasu rukunin gidaje har guda uku a Ijagbo da ke Legas. A halin da ake ciki ’ya’yan mamacin ba su samun ko kwabo daga kudin da ake samu daga rukunin gidajen. Mahaifiyarsa ce take rike kudin da ake samu daga wadansu gidajen daban da aka bayar da hayarsu. Don haka lokacin da wasu daga cikin iyalan suka nemi ina rika ba su wani kaso daga cikin kudin da ake samu a rukunin gidajen da ke Ijagbo sai na ki, don mamacin bai ambaci na ba su ko kwabo daga ciki ba a wasiyyar da ya bari. A takaice zan iya cewa mamacin ya mallaki rukuni gidaje masu yawa a Ibadan da kuma Legas.
Tambaya: Ka nuna shakku a kan yanayin da Rashidi Yrkini ya rasu a wancan lokaci, ko za ka yi mana karin bayani?
Lauya: Eh har yanzu ina kan baka ta na cewa ina tababar akan yanayin da aka ce Rashidi Yekini ya rasu. A bayanin da kanwar marigayin ta yi mini jim kadan da rasuwarsa, wacce ita ma ta rasu bayan wadansu kwanaki da rasuwarsa, ya nuna wasu daga cikin ’yan uwansa ne suka daure shi a cikin wani daki na tsawon kwanaki da nufin kada ya gudu saboda ya samu lalurar tabin hankali. Kuma a ranar 4 ga Mayu, watau a ranar da marigayin zai rasu, sai ya nemi a ba shi shayi don yana jin yunwa. Bashi shayin ke da wuya sai aka ga ya fadi kasa yana kakarin mutuwa, inda aka garzaya da shi wani asibii mai zaman kansa mai suna Al-Amin Hospital da ke yankin Apere a Ibadan amma Likitan a wani bincike da ya yi ya tabbatar da mutuwarsa tun ma kafin a isa da shi asibitin. Don haka a lokacin na nemi a gudanar da bincike a gawar mamacin don a tabbatar da ainihin abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa sai wasu daga cikin iyalansa suka ki, kuma suka yi gaggawar binne shi. Wannan ta sa akwai ayar tambaya a kan yadda mamacin ya rasu. Na san ko a Amurka an gudanar da bincike a kan gawar marigayi shaharren mawaki Micheal Jackson a lokacin da ake zargin wani likita ya kashe shi ne ta hanyar yi masa allura. Da na nemi yi wa matasan da suka garzaya da shi asibiti wadanda aka yi al’amarin akan idonsu, ban samu wani kwakkaran bayani ba, kuma hakan ce ta sa na shiga shakkun cewa akwai rina a kaba akan yanayin da mamacin ya rasu. Don haka har yanzu ina tabbatar yadda marigayin aka ce ya rasu jim kadan bayan an ba shi shayi, wannan ya nuna akwai lauje cikin nadi. Amma da yake iyalan sun ki amincewa a gudanar da bincike a kan gawar tasa, sai na hakura, na bar komai a wajen Allah.
Tambaya: Kawo yanzu yaya ’ya’yan Rashidi Yekini suke gudanar da rayuwa?
Lauya: Babbar ’yarsa mai suna Yemisi ta cika shekara 20 yayin da kanwarta mai suna Maryam ta cika shekara 15. A halin yanzu Yemisi tana kararu ne a Jami’ar Leicester da ke Ingila inda take karatu a bangaren wasan kwaikwayo (performin arts). Ita kuma kanwar tana kararu ne a makarantar sakandare mai zaman kanta da ke garin Osogbo da ke Ibadan, kuma yanzu haka tana ajin karatun karshe ne.
An haifi marigayi Rashidi Yekini ne a ranar 23 ga watan Oktoban 1963 a garin Kaduna kuma ya rasu ne a ranar 4 ga Mayun, shekarar 2012