Shekarar 2013 mai cike da rudanin siyasa a kasar nan
Allah a cikin ikonSa da kudirarSa Ya sanya ga shi shekarar2013, Miladiya ta kare a ranar Talatar da ta gabata, har ma an samu kwanaki uku cif-cif a cikin shekarr 2014, a yau din nan, sai ka ji kamar gobe ana cewa ita ma ta 2014,za ta wuce, Allah ke nan! Allah Ya sa mu […]
Allah a cikin ikonSa da kudirarSa Ya sanya ga shi shekarar2013, Miladiya ta kare a ranar Talatar da ta gabata, har ma an samu kwanaki uku cif-cif a cikin shekarr 2014, a yau din nan, sai ka ji kamar gobe ana cewa ita ma ta 2014,za ta wuce, Allah ke nan! Allah Ya sa mu cika da imani Ya ba mu jinkiri mai albarka. Shekarar ta bana tana da muhimmancin gaskea cikin tarihin gwagwarmayar kasar, don ko koda ba don kasancewarta shekarar jajibirin zabubbukan 2015, ba, ita ce kuma shekarar da kasar nan ta cika shekaru 100, cif-cif daTurawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya suka hade Arewa da Kudanci, sannan suka rada mata suna Najeriya, hadewar da aka yi a cikin irin wannan watan na Janairun shekarar 1914. Turawan kuma suka ci gaba da mulkinta, har zuwa ranar 1 ga watan Oktoban 1960, da suka kakkabe hannuwansu a cikin mulkinta.
Ko kusa ba aniyar makalarmu ta yau ba ce ta yi nazari akan bikin tunawa da cikar kasar nan shekaru 100, da hadawa ba, illah dai don yin matashiya ga masu karatu. Don haka na bar wannan batu, sai an fara mai karatu ka ji cikakken bayani ta kafofi daban-daban akan me ya sa Turawan mulkin mallakar suka yi wannan hadi, da alfanun ko rashin alfanun hadin zuwa yanzu, da sauran bayanai da suka kunshi tarihin shekara 100, na haduwar kasar da a yau ba sai gobe ba, a nahiyar Afirka , ba kasar da ta fita yawan al`umma da albarkatun kasa. Aniyar makalar tawa ta yau ba ta wuce in yi nazarin irin rudanin siyasar da kasar nan ta shiga a shekarar da ta gabata ba, sannan kuma in yi hashen duk don me rudanin ya zafafa? Kasancewa kamar yadda na fadi tun farko ita cewa ita ce shekarar jajibirin babban zaben kasar nan in Allah Ya kaimu.
Mai karatu, mai yiwuwa baka manta ba da irin balahira iri na batuwan harkokin siyasa da tafiyar da mulki da suka faru a shekarar 2013 ba, musamman na harkokin siyasa, wadanda wala-Allah ka karantasu a wannan fili, ko ka ji su a wata kafar yada labarai, ko sauran hanyoyin sadarwa. Alal misali, hadewar manyan jam`iyyun siyasar nan hudu wato ANPP da ACN da CPC da APGA, hadewar da a ranar 31-07-13, Hukumar zabe mai zaman kanta, wato INEC, ta tabbatar masu da rijistar jam`iyyar APC. Wannan haduwar jam`iyyun adawar, da aniyar su karbi mulki daga jam`iyyar siyasa da ke kan mulki ita ce ta farko irinta a cikin tarihin siyasar kasar nan tun da ta samu`yancin kai a shekarar 1960. Don haka ka ce ma an kai an kawo,cikin yin kulle-kulle da aniyar tadiye neman hakan, daga ciki da wajen gungun sabuwar jam`iyyar ta APC.
Ita kanta jam`iyyar PDP, a shekarar ta 2013, ta shiga mummunan rikicin cikin gida da a tarihin siyasar kasar nan shi ma, ba a taba ganinsa ba, lokacin da rikici ya yi rikici akan zargin shugaba kasa Dokta Goodluck Jonathan da shugaban jam`iyyar na kasa Alhaji Bamanga Tukur suna tafiyar da harkokin jam`iyyar ta hanyar gudanar da shugabancin kama-karya, zargin da Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa da gwamnonin jam`iyyar bakwai suka yi. Gwamnonin bakwai masu wancan zargi su ne Gwamna Alhaji Sule Lamido na Jihar Jigawa da Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako na Sakkwato da Alhaji Abdulfatai Ahmed na Jihar Kwara da Dokta Mu`azu Babangida Aliyu na Neja da Alhaji Murtala Nyako na Adamawa da Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso na Jihar Kano da Cif Rotimi Amaechi na Jihar Ribas. Duk da kokarin da shugaban kasa da shugabancin jam`iyyar suka yi ta yi don kawo karshen wancan rikici, kokarin ya ci tura, inda a ranar 26-11-13, biyar daga cikin wadancan gwamnoni bakwai, in ban da gwamnonin jihohin Neja da Jigawa, suka canja sheka daga jam`iyyarsu ta PDP suka koma APC.
Ba nan kadai wannan rigima ta PDP ta tsaya ba, don kuwa a ranar 18-12-13 `yan Majalisar Wakilai na Tarayya 37, na PDP, sun bi gwamnoninsu biyar zuwa APC, wanda haka ya sanya yanzu jam`iyyar APC, ita ke da rinjaye a Majalisar da Wakilai 175, ya yin da PDP ke da 171. Akwai kuma zato mai karfi da ake kyautatawa cewa wasu daga cikin gwamnonin da ’yan Majalisun Dokoki na kasa na jam`iyyar PDP, zasu komajam`iyyar adawa ta APC a cikin wannan shekarar.
Wata babbar rigima da ta afka wa jam`iyyar PDP a bara, ita ce ta cacar baki da ta bayyana, tsakanin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo (ubangidan siyasa na shugaba Jonathan) da shugaba Jonathan din. A takardar tsohon shugaban kasar, mai shafuffuka 18, tsohon shugaban kasar ya zargi shugaba Jonathan da daure wa cin hanci da rashawa gindi da kasa tabuka kome akan tabarbarewar tsaro da kafa kungiyar `yan ina-da-kisa har mutane 1,000, da ya yi zargin shugaba Jonathan zai yi amfani da su don cimma aniyarsa ta ci gaba da mulki a shekarar2015.
A nasa martanin ga Cif Obasanjo, mai kalmomi 4984, na ranar20-12-13, shugaba Jonathan ya bayyana Cif Onasanjo da cewar so kawai yake ya damalmala matakan tsaron kasar nan, sannan kuma a gefe daya ya zuga talakkawan kasar nan, don kuwa wai a zaman Cif Obasanjo tsohon shugaban kasa da ya yi mulki kasar nan kusan shekaru 12, ya kamata ya san irin maganar da zai fadi.
A gefe daya kuma rahotanni sun tabbatar da cewa tuni sojojin bakan shugaba Jonathan suka shirya jerin sunayen `yan Arewa 151, da za su tuntuba don samun nasarar sake zabensa (shi shugaba Jonathan)a shekarar 2015, al`amarin da ya zuwa yanzu wasu `yan kalilan daga cikin jerin sunayen mutanen da aka ambata suka nisanta kansu da cewa koda an tuntubesu ba za su bada goyon bayan ba.
Da wadannan rudani da na iya ambata faruwarsu a fagen siyasar kasar nan a shekarar 2013, da wadanda rashin fili ya sa ban iya kawo su ba, mai karatu zai iya fahimtar cewar `yan siyasar kasar nan suna kitsa wadannan rudu ne don zabubbukan shekarar 2015, kuma hakan suna manuniya da irin rudanin da za a kara shiga a wannan shekarar ta 2014, wadda ita ce shekarar jajibirin shekarar zaben mai zuwa. Ma`ana dai duk abin da suke yi, sai don samun nasarar zabubbukan ko ta halin kaka. Don haka ba abin da ya rage wa `yan kasa da ya wuce su ci gaba da dukufa cikin rokon Allah SWT, akan Allah Ya sa a yi zabubbukan lami lafiya, Ya ba mu ikon zaben shugabannin nagari tun daga sama har kasa, wadanda za su taimaka cikin ganin ingantuwar rayuwar`yan kasa, amin summa amin .