Shekarar 2020: Muhimman ayyukan da Buhari zai mayar da hankali
Jawabin Shugaba Buhari na sabuwar shekarar 2020 tare da Muhimman ayyukan da ya ce zai mayar da hankali a kai Shugaba Muhammadu Buhari ya fara da yi wa ‘yan Najeriya godiya kan zabensa da suka sake yi a watan Fabrairun 2019. Sannan ya yaba wa abokan hamayyarsa da suka yi takara tare kuma suka dauki […]
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Jawabin Shugaba Buhari na sabuwar shekarar 2020 tare da Muhimman ayyukan da ya ce zai mayar da hankali a kai
Shugaba Muhammadu Buhari ya fara da yi wa ‘yan Najeriya godiya kan zabensa da suka sake yi a watan Fabrairun 2019.
Sannan ya yaba wa abokan hamayyarsa da suka yi takara tare kuma suka dauki kaddara.
Shugaban ya kara da cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a 2023 ba, amma kuma ya sha alwashin inganta harkar zaben kasar a nan gaba.
Muhimman ayyukan da Buhari ya ce zai mayar da hankali a kai:
- Tituna 47 da za a yi a tsakanin 2020/21 da suka hada da hanyoyin da suka dangana ga tashoshin ruwa.
- Manyan gadoji musamman gadar Second Niger Bridge.
- Kammala ayyukan rukunin gidaje 13 karkashin tsarin samar da gidaje na kasa.
- Kaddamar da filayen jirgin Lagos da Kano da Maiduguri da Enugu a 2020.
- Kaddamar da shirin aikin gona a karkara a kananan hukumomi 700 a tsawon shekaru uku.
- Kaddamar da shirin gandun kiwon dabbobi a Gombe.
- Horas da ma’aikata 50,000 domin taimaka wa malaman gona 7,000 da ake da su.
- Kaddamar da titin jirgin kasa na Lagos zuwa Ibadan da Itakpe zuwa Warri a watanni ukun farkon 2020.
- Fara aikin hanyar jirgin kasa da za ta tashi daga Ibadan zuwa Abuja da kuma Kano zuwa Kaduna a farkon watannin ukun 2020.
- Kara sakar wa harkar wutar lantarki mara domin bai wa masu sanya hannun jari damar samo da sayar da wutar lantarki.
- Fara aikin ginin tashar wutar lantarki ta Mambilla a watannin shidan farkon 2020.
- Fara aikin jan bututun iskar gas AKK gas pipeline, da OB3 gas pipeline da kuma fadada bututun iskar gas din na Escravos zuwa Lagos a watanni ukun farko na 2020.