Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji
Tawagar ta ce ba za ta goyi bayan ƙudirin rabon harajin ba.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da tawagarsa, sun yi watsi da sabon tsarin rabon haraji da ake shirin aiwatarwa a Najeriya.
Tawagar ta ce rashin fayyace cikakkiyar ma’anar tsarin rabon zai iya ƙara haifar da rashin daidaito a tsakanin yankuna.
Da yake magana a ranar Lahadi, mai magana da yawun tawagar, Dokta Ladan Salihu, ya bayyana cewa ya kamata a fayyace yadda tsarin zai gudana don guje wa ruɗani.
Tawagar ta ce tsarin bayar da kashi 30 bisa zai fi amfanar wasu yankuna kaɗai, musamman Jihar Legas, tare da cutar da Arewacin Najeriya.
Tawagar ta yaba wa Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), bisa amincewarta da sabon tsarin raba kuɗin VAT da sauran haraji.
Duk da haka, sun bayyana cewa dole ne a tabbatar da adalci ta hanyar danganta rabon kuɗaɗen da ainihin ayyukan tattalin arziƙi.
Tawagar ta ce ba za ta bayar da cikakken goyon baya ga gyare-gyaren ba har sai an biya buƙatunsu.
Sun roƙi Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya da Kwamitin Gyaran Haraji na Shugaban Ƙasa da su yi gyare-gyaren da suka dace don tabbatar da adalci a tsakanin kowa a Najeriya.