Shekarau ya zama Minista
Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim shekarau a matsayin Minista a zamanta na shekaranjiya Laraba.An wanke Malam Shekarau ne tare da sauran wadanda aka mika sunayensu ga majalisar don nada su a matsayin sababbin ministoci, a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan da suka hada da Abdul Bulama daga Jihar Yobe da […]

Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim shekarau a matsayin Minista a zamanta na shekaranjiya Laraba.
An wanke Malam Shekarau ne tare da sauran wadanda aka mika sunayensu ga majalisar don nada su a matsayin sababbin ministoci, a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan da suka hada da Abdul Bulama daga Jihar Yobe da Adedayo Adeyeye daga Jihar Ekiti da kuma Stephen Oruh daga Jihar Delta.
Mistta Oruh shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP a shiyyar Kudu maso Kudu, yayin da Adedayo Adeyeye shi ne jagoran jam’iyyar a Ekiti.
Sababbin Ministocin za su maye gurabun ministocin da suka yi murabus da suka hada da Yerima Ngama, tsohon Minista a Ma’aikatar Kudi da Caleb Olubolade, tsohon Ministan Harkokinh ’Yan sanda da kuma Godsday Orubebe, tsohon Ministan Harkokin Neja-Delta.
Malam Shekarau, wanda jigo ne wajen kafa Jam’iyyar APC, wadda ita ce babbar jam’iyyar adawa ya koma PDP ne bayan da aka mika jagorancin APC ga babban abokin adawarsa Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya fice daga PDP zuwa APC a karshen bara.
Shugaban kasa ne zai rantsar da sababbin ministocin tare da ba su ma’aikatun da za su jagoranta.