Shekarau ya zama Ministan Ilimi
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya rantsar da sababbin ministoci hudu a fadarsa da ke Abuja a shekaranjiya Laraba inda yya nada tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau a matsayin Ministan Ilimi.Malam Ibrahim Shekarau yana cikin mutum hudu da Majalisar Dattawa ta tattance a makon jiya, don nada su a mukaman ministoci.Sauran wadanda aka […]

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya rantsar da sababbin ministoci hudu a fadarsa da ke Abuja a shekaranjiya Laraba inda yya nada tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau a matsayin Ministan Ilimi.
Malam Ibrahim Shekarau yana cikin mutum hudu da Majalisar Dattawa ta tattance a makon jiya, don nada su a mukaman ministoci.
Sauran wadanda aka nada sun hada da Mista Stephen Oru, Ministan Ma’aikatar Harkokin Neja- Delta da Abdul Bulama, Ministan Kimiyya da kere-kere, sai kuma Clement Adebayo Adeyeye, Minista a Ma’aikatar Ayyuka.
Shugaba Jonathan kuma ya maida Alhaji Bashir Yuguda a matsayin Ministan Tsare-Tsare na kasa kuma Minista a Ma’aikatar Kudi don cike gurbin da sallamar Minista Yarima Ngama ta haifar a ma’aikatar.
A jawabin Shugaba Jonathan ya umarci ministocin su yi aiki tukuru ba don burge shi, shi kadai ba, har ma da ’yan Najeriya ganin sun zo ne a matsayin cikon lokaci, abin da ke nuni da karatowar zaben badi.