Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya?
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Babu wani ci gaba – Alhaji Ibrahim Alhaji Ibrahim […]
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Babu wani ci gaba – Alhaji Ibrahim
Alhaji Ibrahim Muhammad Suma’ila: “A matsayina na dan Najeriya, abin da na gani da abin da ni na fahimta game da wannan mulkin dimokuradiyya, tun a lokacin da kasar nan aka maido da ita, a 1999 ya zuwa bana da muke ciki a halin yanzu; a gaskiya babu wani ci gaba na a zo a gani da za a buga kirji a ce an samu, ko wani amfani da aka samar wa al’ummar kasar nan; illa kawai ci gaba irin na mai tonon rijiya.
“Dalilina kuwa, domin idan ana batun maganar ci gaba ko samun wani amfani sai an fara duba batun tsaron kasa da zaman lafiyar jama’a, ita ce shinfida ta farko kafin komai. Sai batun kawar da talauci da samar wa ’yan kasa ayyukan dogaro da kai.