Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya? 1

A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: An samu ci gaba – Muhammad Kabiru Malam  Muhammad […]

Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya? 1
Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya? 1

A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

An samu ci gaba – Muhammad Kabiru

Malam  Muhammad Kabiru Audu Zamfara: “Ni a ganina akwai ci gaban da aka samu duk da cewa bai taka kara ya karya ba amma ya bambanta da mulkin kama karya na sojoji da ya gabata, domin ko ba komai akwai ’yancin fadin albarkacin baki a cikin wannan mulki na dimokuradiyya da biyan bukatun mutane na kusa da gwamnatin kasa; musamman ga ’ya’yan jam’iyyar mai mulkin kasa kuma an samu yawaitar ababen hawa da babu irin hakan a can baya kuma wasu cikin matasa wasu an koyar da su sana o’i daban-daban na dogaro da kai, ga kuma wayar sadarwa ta hannu birni da kauye.
Amma duk da wadannan, akwai wurare kuma da mulkin Dimokuradiyyar ya yi kasa a gwiwa.