Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya? 2
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Kwaliyya ba ta biya kudin sabulu ba – Ali […]
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Kwaliyya ba ta biya kudin sabulu ba – Ali Warure
Alhaji Ali Warure, Kasuwar Wuse Abuja: “A gaskiya ba ta biya ba, kuma in haka demokuradiyyar take a duniya to ba ma fatan ci gabanta a kasar nan. Hanzarin da ake bayarwa a kullum shi ne, ita jaririya ce amma tana girma abun sai kara muni yake yi. Idan ka yi la’akari da jama’ar da ake kashewa a kullum a kasar nan, sannan magance shi kamar yana neman ya gagari mahukunta. To, ai ba yadda za ka yi fatan ya dore. Saboda haka ni a ra’ayina, dimokuradiyya koma baya ta kawo mana, musamman a matakin Tarayya, sai dai tubarkalla akwai dan bambanci a matakin jihohi, saboda wasu wuraren an samu ci gaba an fito da kauyuka da dama zuwa matsayin maraya.”