Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya? 3

A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Ba ta biya kudin sabulu ba – Ibrahim Yakubu […]

Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya? 3
Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya? 3

A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Ba ta biya kudin sabulu ba – Ibrahim Yakubu

Malam Ibrahim Yakubu dandushe: “Kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba a mafi yawan al’amura. Saboda an ce mulkin dimokuradiyya ita ce: “Gwamnatin da jama’a suka zaba, wadda jama’a suke gudanarwa, don amfanin jama’a.” To a yadda nake ji nake ganin yadda al’amura ke wakana a kasar nan, akasin haka ne. Wanda jama’ar ke so ba shi ake tsayarwa takara ba, bare har a bari a zabe shi, sannan ya amfani jama’ar. Wannan ya nuna ba dimokuradiyyar ake aiwatarwa ba. Abu mafi sauki a demokuradiyya shi ne ’yancin fadin albarkacin baki, to yau idan mutum wanda ya kai ya kawo ne ya fade ta, sai an yi masa bita da kulli an nakasa shi.”