Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya? 4
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Babu ci gaba a kasa – Sulaiman Yakubu Sulaiman […]
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Babu ci gaba a kasa – Sulaiman Yakubu
Sulaiman Yakubu, dan jarida a Kaduna: “Babu ci gaba a cikin shekaru 15 na demokuradiyya saboda ya kamata a ce an fita daga cikin wahalhalun da muke ciki a yanzu a kasar nan. Yanzu manyan suna nan ne su cika aljihunsu da kudi suna kuma baza wa talakawa kura. ’Yan siyasarmu kamata ya yi a ce suna yi wa talakawa abin da ya kamata amma a kullum sai zagin su ake yi. Don haka shekaru 15 na demokuradiyya, babu wani amfani da ’yan siyasa suka kawo.”