Shekaru 15 da Dimokuradiyya a Najeriya: Ci gaba ko baya? 5
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Ci gaban rabi da rabi ne – Jummai Usman […]
A makon jiya ne Najeriya ta cika shekara 15 da mulkin Dimokuradiyya. Abin tambaya a nan shi ne, a tsawon shekarun nan, shin an samu ci gaba ne ko kuwa ci baya, ko tsaka-tsaki? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Ci gaban rabi da rabi ne – Jummai Usman
Malama Jummai Usman: “Gaskiya abin ya kasu kashi biyu ne, ta wani bangaren zan ce an ci gaba ta wani bangaren kuma ba a ci gaba ba. Rashin ci gaban kasar nan a cikin shekaru 15 na demokuradiyya na da alaka da rashin shugabanni masu kishi. Domin maganar gaskiya ya kamata a ce ci gaban Najeriya ya fi inda muke a yanzu. Misali, rashin aiki karuwa yake yi, tabarbarewar ilmi, ga rashin tsaro da sauran matsaloli da suka dabaibaye kasar nan.”