Shekaru 50, bayan ba Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato

Gaba ta wuce, baya ad da saura,yanzu ku nemo wani kamatai,Wannan wakar na cikin wani bangare na wakar ta`aziyyar rasuwar Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato,  kuma Firimiyan Jihar Arewa na farko kuma na karshe (1954 zuwa 1966), da shahararren mawakin kasar Hausar nan Alhaji Musa dankwairo Maradun, ya yi yau shekaru 50, bayan da […]

Shekaru 50, bayan ba Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato
Shekaru 50, bayan ba Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato

Gaba ta wuce, baya ad da saura,yanzu ku nemo wani kamatai,
Wannan wakar na cikin wani bangare na wakar ta`aziyyar rasuwar Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato,  kuma Firimiyan Jihar Arewa na farko kuma na karshe (1954 zuwa 1966), da shahararren mawakin kasar Hausar nan Alhaji Musa dankwairo Maradun, ya yi yau shekaru 50, bayan da wasu kananan hafsoshin sojoji `yan kabilar Ibo a karkashin jagorancin Manjo Chukwuma Kaduna Nzegu, suka yi juyin mulkin farko a kasar nan, suka kuma kashe Firimiya Ahmadu Bello da wasu Ministocin tarayyar kasar nan a irin wannan rana ta 15 ga watan Janairun 1966, yau shekaru 50 cif-cif.
A wancan rana ina da kwanaki 15, da barin garinmu Kankiya, na shiga aji na daya a karamar Sakandare ta koyon sana`a ta Mashi a cikin Jihar Katsina ta yau. Kasancewar ina dan shekaru kusan 16, da haihuwa, ban iya cewa takamaimai na shiga wata matsananciyar damuwa ta me zai zama makomar karatuna, bare ta shugabannina, amma dai mun shiga jimami da dimauta a kan abin da muka ji da tunanin ko ya Kaduna wadda a lokacin ta ke Hedkwatar Jihar Arewa da Legas Hedkwatar kasa, suke ciki, yaki ake ko zaune ake lafiya, wa ya karbi mulki? Jin an ce sojojisun kwace mulki, sun kuma kashe Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwto.
Akan waccan waka ta sama kuwa, ga `yan adawa da wasu `yan Arewa da ba su yi hangen nesa ba tun a wancan lokaci, sun dauke ta tamfar zuga ce irin ta maroki, a kan yau shi ne don an kasha Sardauna da a lokacin wasu Talakawa suke ganin gwamnatinsa azaba ce gare su da iyalensu, yanzu kuma suna hasashen tun da dai an kawar da mulki irin na Sarakuna, soja ya zo, to sabuwar rayuwa, ta a sha zuma da madara za ta samu, ba sauran dauri irin na siyasa da sa dimbin haraji da jangali, ba re kuma wasu ayyukan tursasawa da suke ganin masu mulki suna yi musu, musamman hana su  zaben wanda suke so. Allah jikan Sakataren yada labarai na rusashshiyar jam`iyyar NPN reshen Jihar Kano, a jamhuriya ta biyu, Alhaji Namadobi Ya`u, da ya kan ce, “Idan daba don jam`iyyar NPC, ta su Sa Anmadu Bello, ta mike tsaye,tun farko, wajen wayar da kan jama`a ta samu nasararar kafa gwamnatin a cikin hadakarta da jam`iyyar NCNC, ta Cif Nnamdi Azikwe, shugaban kasar nan na farko, a zabubbukan 1954, da taSain da `yan Arewa ke da shi a yau a cikin harkokin gudanar da mulkin kasa bisa kamanta gaskiya da adalci bai samu ba, bare a yi maganar sun iya mulkin tsakankanin sauran manyan kabilun kasar nan.
Idan ka ce dukkan ayyukan ci gaba irin na tafiyar da mulki da na tattalin arzikin kasa da na zamantakewa da na fannin ilimi da kiwon lafiya da noma da kiwo da makamantansu da jihohin Arewa 19, su ke tinkaho da su a yau, sun dauko asali ne daga irin harsashin da Gwamnatin Sa Ahmadu Bello ta kafa ne, ba wanda zai ce ka yi karya. Ta fannin siyasa ko gudanar da mulkin kasa, kowa yana ganin irin rawar da `yan Arewa suke takawa, tun wancan lokaci zuwa yau. Haka labarin yake a kan fannin ilimi, Gwamnatin Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ce ta kakkafa wasu makarantun horon Malamai na maza da na `yan mata, ita ta kafa Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic) da Jami`ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da asibitin koyarwa na jami`ar. Haka ta fannin tsaro, Sardauna ya kafa Kwalejin `yan sanda ta Kaduna. Duk ci gaban kasa da Arewa ta samu, sun samu ne daga irin yadda gwamnatin ta himmatu wajen ganin ingantuwar harkokin noma da kiwo da kuma kudin haraji da jangali. Gwamnatin Sardauna ce ta kara karfafa kafuwar Hukumar sayen amfanin gona ta Arewa, wato NNMB, a Kano. Hukumar da ta rinka sayen amfanin gona irin su gyada da auduga da kwara da makamantansu, a kan kari, kuma a kan farashi mai inganci.
Ta fannin kasuwanci da zuba jari da kafa masana`antu, gwamnatin Sa Ahmadun ce ta kafa Kamfanin ci gaban Arewa, da na zuba jari, wato NNDC da NNIL, dukkansu a Kaduna da Bankin Arewa, wato Bank of the North da yanzu hadakar Bankuna ta sa ya narke a cikin Bankin hadin kai, wato Unity Bank. Hakazalika, Gwamnatin Arewa ta farko ita ta kafa Masakar Arewa a Kaduna da ta Zamfara a Gusau, da Kamfanin suminti na Sakkwato, baya ga zuba idanu da ta yi wajen tabbatar da cewa `yan kasuwar jihar, ana yi da su yadda ya kamata, al`amarin da ya sa har Alhaji Abacha suke da shi a zaman wakilinsu a Majalisar Dokoki ta Arewa. Ta fannin yada labarai gwamnatin arewar ce ta kafa gidan Radiyo da Telebijin na Kaduna a shekarar 1962, sannan ta kafa Kamfanin buga jaridun New Nigerian a dai Kadunan a farkon shekarar 1966, wadda kwanaki 15, da kafuwarta aka kashe Sardauna. A kan batun ayyukan gwamnatoci, tun daga ta Arewa, zuwa ta tarayya, Sa Ahmabu Bello ya tabbatar da cewa, yadda Arewa take habaka a kan samun masu ilimin zamani, haka ake kara cusa su cikin ma`aikatu da Hukumomin gwamnatocin, kuma ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba, bare jinsin da mutum ya fito, muddin dai dan Arewa ne kai, to, an gama. Haka Marigayi Sardaunan Sakkwato ya gudanar da ayyukansa na Firimiyan Jihar Arewa na tsawon shekaru 12, don ci gaban Arewa da al`ummarta, ayyukan alherin da kullum ake ambatansa da aikatawa.
Wani mutum mai suna Alhaji Ma`aji a Maiduguri wajejen shekarun 1980, ya taba gaya mini irin karamci da alheri da rashin hadama irin na Sardauna da ya sa ni ya kuma gani a aikace. Ya ce “A duk shekara Sardauna ya kai rangadi lardin Barnon, ya kan sa Ma`ajin Baitalmalin En-en (N.A) lardin da ya kawo dukkan kudin da En-en ta mallaka, kudin da jami`an En-en, kan dan boye wani abu da tunanin Sardaunan zai tafi da wasu, amma idan an kawo sai ya tambaya, an fitar da wadanda za a biya albashi da alawus-alawus na wannan watan, idan an ce eee…, sai ya sa hannu ya fara raba kudin yana mai ba da umurnin wannan kason a ba malamai, wannan kason a ba fakirai, wannan kason a ba nakasassu da sauran mabukata su yi mana addu`a, Allah Ya zaunar da mu lafiya, tare da kara kawo daukaka ga Arewa da mutanenta da ma kasa baki daya.” Alhaji Ma`aji ya ce tun ba su fahimci cewa, Sardauna ba ya daukar ko sisin kwabo daga cikin kudin, har suka gane.
A kullum sai ambaton kyawawan halayen kirki na shugabanci nagari na Marigayi Sardauna muke yi, amma mun  kasa samun ko da kwatankwacin irinsu daga shugabannin da suka biyo bayansa. Ko me ya sa? A wata tattaunawa da na taba yi da Alhaji Yusuf Maitama Sule dan Masanin Kano, kuma tsohon Ministan tarayya a jamhuriya ta daya, cewa ya yi, “Samun Sardaunan ya yi matukar wuya ne, kasancewar, a da ana batun Sardauna shi kadai, duk inda ya sa gabansa can za a yi a Arewa, amma a yau kana maganar gwamnoni 19, gwamnonin da kowa da inda ya sa gabansa, gwamnonin da ko da zama a cikin jam`iyyar siyasa daya bai sanyawa su yi abu iri daya.” Wannan kadai in ji shi, ya isa ya sa a ga an kasa samun magajin Sardauna a yau. Ina ga dai kamar yadda marigayi dankwairo ya fadi a waccan wakar, har yanzu muna kanta. Allah Ya jikan Sardaunan Sakkwato da mukarrabansa da dukkan shugabannin da suke koyi da su akan ayyukan alheri ga jama`arsu da kasarsu.