Shekaru 50 na Mai martaba Sarkin Kano Kowa ya yarda da Allah. . .
“Ba ni da wani abu mai yawa da zance da ya wuce in gode wa Allah da Ya rayar da ni, har na ga wadannan shekaru akan karagar mulki, a matsayin Sarki da ya yi dogon mulki.” “Ina neman mutanen da muka sabamawa da su yafe mana. Daga bangarenmu ba wanda ya saba mana. Idan […]
“Ba ni da wani abu mai yawa da zance da ya wuce in gode wa Allah da Ya rayar da ni, har na ga wadannan shekaru akan karagar mulki, a matsayin Sarki da ya yi dogon mulki.” “Ina neman mutanen da muka sabamawa da su yafe mana. Daga bangarenmu ba wanda ya saba mana. Idan akwai wanda ya saba mana mu mun yafe masa. ”
Wadannan kalamai na sama na cikin irin kalaman da aka rika jin Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero yana yawan furtawa a duk inda ya samu damar yin jawabi a cikin bukukuwan kwanaki uku da aka gudanar a Kano a zaman cikarsa shekaru 50, akan karagar mulkin Kano, da kuma kasancewar ya cika shekaru 83, da haihuwa.
Alhaji Ado Bayero shine Sarkin Kano na 13, a mulkin Daular Fulani, na 56, a cikin Sarakunan da suka mulki Kano, yau sama da shekaru 1,000. Tarihi ya tabbatar da cewa Alhaji Ado Bayero shi ne da na 12, kuma na farko da aka fara sawa makarantar boko a cikin `ya`yan Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero, Sarkin Kano na 10, (1926 zuwa 1953) a Daular mulkin Fulani, kuma da na biyu ga Hajiya Hasiya da aka fi sa ni da mai Babban daki.
An nada Alhaji Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano a ranar 11 ga watan Oktoban 1963, (shi kansa wannan biki an hada biyu ne aka matso da bikin cika shekaru 50, din zuwa lokacin haihuwa), a lokacin yana Jakadan kasar nan a kasar Senegal, amma kafin ya kai ga wannan mukami tarihinsa ya tabbatar da ya yi aiki Banki, ya kuma aiki da En`en Kano a mukamai daban-daban. Kuma ya tafi Majalisar Dokoki ta Arewa, a Kaduna, daga can ya komo Kano a matsayin Wakilin Doka, mukamin da yake rike da shi aka yi masa Jakadan kasar nan a kasar Senegal.
Zamaninsa ya riski burbishin dimbin ikon da Sarakunan gargajiya suke da shi, na kasancewa suke da Alkalai da `Yan doka da gidajen Kurkuku, wato dai ma`ana suke da cikakken ikon tafiyar da kasashensu ta kowane fanni, da wannan dalili ake masu lakabi da Sarkunan yanka, abin da ya sanya koda Turawan mulkin mallaka suka shigo kasar nan a shekarar 1904, suka ci gaba da mulki a karkashin tsarin da suka tarar da Sarakunan Arewa a kai. Na san da yawa mutane sun sa ni ko sun ji labarin irin yadda akasarin Sarakunan Arewa suka rika gallaza wa talakawa akan bambance-bambancen siyasa a wancan lokacin, wato neman mulkin da akai tsakanin jam`iyyar NPC (mai mulkin Arewa da gwamnatin kasa baki daya) da `yan jam `iyyar NEPU ta `yan adawa.
A irin wancan hali, Alhaji Ado Bayero ya hau kan karagar mulkin Kano, kuma ba da dadewa ba, sai ga guguwar canji ta zo daga sojojin da suka fara yin juyin mulki a kasar nan a ranar 15 ga Janairun 1966, wadanda suka fara bullo da canje-canjen raba Sarakuna da madafun ikon da suke da su, kamar yin shari`a da iko da gidajen Yari da Baitalmalin En`e, tare da taka masu burki cikin gudanar da wasu aikace-aikacen da suka gada iyaye da kakanni.
Abubuwa sun kara rincabe wa Sarakuna a lokacin da sojoji suka mayar da mulki hannun farar hula a shekarar 1979, lokacin da wasu gwamnonin jihohi suka rika ganin Sarakuna karkashinsu suke, ko sun ki ko sun so, bisa ga zugar jami`ansu da magoya baya. A irin wannan hali ne a watan Yulin shekarar 1981, Gwamna Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya ba mai Martaba Alhaji Ado Bayero takardar tuhuma akan ya fita zuwa kasashen waje ba tare da ya samu amincewar gwamnatinsa ba. Wannan takardar tuhuma ita ta haddasa kazamar zanga-zanga a Kano, da ta haddasa salwantar rayuka da dukiyoyin al`umma.
Ita ma gwamnatin soja ta Janar Muhammadu Buhari da ta hambarar da gwamnatin farar hula ta jamhuriya ta biyu, a shekarar 1983, ta dakatar da Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da babban amininsa Oni na Ife Oba Okunade Sujuade, har tsawon watanni shida, bisa ga sun kai ziyara kasar Isra`ila an masu gagarumar tarba, alhali a lokacin kasar nan tana zaman doya da man ja da kasar ta Isra`ila.
Bayan rikicin addini na Muhammadu Marwa Maitatsine da Kano ta yi fama da shi a watan Disamban 1980, wanda ya haddasa asarar rayukan daruruwan al`umma da dukiyoyinsu, Mai martaba Sarki ya sha haduwa da bijirewar `yan kungiyoyin addini irin na Izalatul Bid`a Wa`ikamatus Sunnah da Shi`a, bayan a can baya ya sha ta `yan darikar Tijjani da kadiriiya.
A baya-bayan nan ma yana ta samun takala da farmaki iri-iri daga `yan siyasa da `yan kungiyoyi wala Allah da sunan siyasa ko addini. Alal misali a ranar 19 ga watan Janairun da ya gabata a unguwar Hausawa ta Masallacin Murtala da ke kewayen birnin Kano wasu `yan bindiga da ake zargin `yan kungiyar Jama`tu Ahlis Sunnah Lid Da`await Wal Jihad ne da ake ma lakabi da Boko Haram, suka kai wa Mai maitaba Sarkin na Kano hari, inda suka kashe mutane shidda ciki kuwa har da na kusa da Sarkin su uku, sannan suka jikkata wasu da suka hada da `ya`yansa biyu.
Tabbas Alhaji Ado Bayero Sarki ne da ya ratso cikin guguwar sauye-sauyen zamani walau na zamantakewa, tattalin arziki, siyasa da addini, amma kuma ya yi iyakacin bakin kokarinsa matuka wajen karbar wadannan canje-canje ba tare da tayar da hankalinsa ba, ba tare da la`akari da irin mulkin da Kano ta gada ba. Haka kuwa duk sun samu ne bisa yarda da ya yi akan babu mai zamani ban da Allah, kuma shi ya yarda da Allah. Tumbin Giwa na taya Maimartaba Sarki Barka da arzikin ganin wadannan shekaru da magabatansa ba su gani akan karagar mulkin Kano ba, tare da addu`ar Allah Ya kara wa Sarki lafiya, Ya kuma dubi bayansa.