Shekaru 52 bayan kashe su Sardauna
A makon nan ne aka cika shekaru 52 da yi wa su Sardauna kisan gilla a wani juyin mulki da sojoji ‘yan kabilar Ibo suka jagoranta.Wannan mummunan juyin mulki da ake yi wa lakabi da juyin mulkin ‘’yan kabilar Ibo, ya gudana ne a talatainin daren 15 ga watan Janairun 1966.Yana da muhimmanci a irin […]
A makon nan ne aka cika shekaru 52 da yi wa su Sardauna kisan gilla a wani juyin mulki da sojoji ‘yan kabilar Ibo suka jagoranta.Wannan mummunan juyin mulki da ake yi wa lakabi da juyin mulkin ‘’yan kabilar Ibo, ya gudana ne a talatainin daren 15 ga watan Janairun 1966.Yana da muhimmanci a irin wannan lokaci mu dinga bita da nanata zaluncin da aka aikata a wannan dare. Ko ba domin kiyaye tarihin magabata ba, domin fito da karairayi da kokarin sauya tarihin abin da ya wakana a wannan dare da wasu mutane ke ta yi tun lokacin da abin ya faru. .Kuma ai ko ba komai, juyin mulkin ya haddasa yakin basasa na watanni 30 da ya sauya alkiblar kasar.Tun lokacin da aka yi juyin mulkin, marubuta da masu sharhi suka fara kokarin sauya abin da ya faru.Wasu na kokarin nuna cewa ma kisan da aka aikata a daren daidai ne. Wasu ma juyin juya hali suka yi wa kisan lakabi da shi. Haka tarihi ya gada, in kaki rubuta tarihinka, to wani zai rubuta maka, kuma zai rubuta abin da ya gadama.
Baya ga batun kokarin boye gaskiyar juyin mulkin, da manufar sojojin da suka aiwatar da shi, akwai masu kokarin nuna shugabannin farko irin su Sa Ahmadu Bello Sardauna, Sa Abubakar Tafawa balewa, cif Samuel Ladoke Akintola da sauran su a matsayin mutanen banza wadanda ba su yi wani abin kwarai ba. A kodayaushe mutum na da makiya, ko da kuwa bayan babu shi.
Komai wasu za su ce, ko za su rubuta a kan juyin mulkin, ko game da mulkin shugabannin farko, ba wanda ya isa ya halasta kisan gillar. Kuma juyin mulkin, ba wani abu ba ne, illa ta’asa ta makasa.Ku bi mutane tsakiyar dare, ku karkashe su, me za a kira ku? ‘Yan juyin juya hali ko-kuwa makasa?
Domin kara tunatar da mu ta’asar daren 15 ga Janairu,1966, bari mu fadi wani abu kadan.’yan boko da ‘yan siyasar Kudancin Najeriya, wadanda su ne ke da ‘yan boko, kuma su ne ma ke da jaridu a wancan lokaci, sun fito da niyyar ko ta halin kaka sai sun murkushe Arewacin kasar nan. Kadan daga cikin yunkurin murkushe mu, shi ne, muhawarar da aka tafka a farfajiyar majalisar dokokin Najeriya, a shekarar 1953. Kamar yadda ya ruwaito a littafinsa mai suna rayuwata (My Life) Firimiyan farko na Arewacin Nijeriya, Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, ya ce “Mun je majalisar tarayya da ke Legas, kawai muka wayi gari da wani kudiri, wanda bai cikin kudirorin da ya kamata ai muhawara a kansu a ranar”.
Ba kowane kudiri ba ne, Sardauna ke magana in ban da kudirin nan da jam’iyyar AG, ta Yarbawa ta dauki nauyi, kuma ta gabatar, wanda Anthony Enahoro, dan jam’iyyar AG ya gabatar a zauren majalisa. Wannan kudiri yana magana ne, a kan a bai wa Najeriya ‘yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka a shekarar 1957. Hikimar bai wa Najeriya ‘yanci a wannan lokaci, shi ne, mutanen Kudu wadanda ke da masu ilimi, su ne za su mamaye komai, kama daga aikin gwamnati, kwangila, siyasa da komai. Domin a wancan lokaci ‘yan bokon Arewa ba su wuce a kirga ba. Hangen nesan shugabaninmu da ke waccan majalisar kamar shi Sa Amadu Bello, Makaman Bidda, Muhammadu Ribadu da sauran su, ya sa suka ki amincewa da wancan kudiri, domin sun riga sun hango tarkon da aka nada mana. Rashin amincewa da wannan kudiri, ya sa ‘yan jaridar Kudu, da ‘yan siyasarsu, musamman na jam’iyyar AG suka dinga rubuce-rubucen batanci, suna zagin wakilan Arewa, cewa su ‘yan koren Turawan Yamma ne, wai ba su son a samu ‘yanci cikin lokaci. Kai har ma sai da ta kai an sanya ‘yan bangar jam’iyyar AG da NCNC suka yi wa shugabannin mu a ture, suna zagin su da gaya musu maganganu mara sa dadi. A cikin littafin da ya rubuta mai suna My Life (Rayuwata) Sardauna, ya bayyana yadda tun daga Legas har Kaduna duk garin da suka wuce, sai ka ga ‘yan bangar AG ko na NCNC na yi musu eho, saboda kamar yadda na yi bayani a baya, Nnamdi Azikwe, wanda shi ne shugaban jam’iyyar NCNC ya mallaki jaridarsa, wadda ake bugawa kuma tana zuwa har Kano da Kaduna, don haka hatta mutanen Kudu mazauna manyan biranen Arewacin Najeriya suna samun jaridar. Abin da ya faru a majalisar tarayya ne, ya sa wakilan Arewa da suka dawo Kaduna suka yi zama a majalisar dokokin shiyyar Arewa, inda suka gabatar da kudirori takwas, wadanda martani ne ga abin da ya faru a Legas. Cikin wadannan kudirori har da batun yiwuyar Arewa ta janye daga tarayyar Najeriya. Ana cikin wannan sabatta juyata, wai sai kuma jam’iyyar AG ta Yarbawa, ta turo wata tawaga zuwa Kano, domin su zo su wayar da kawunan mutanen Arewa game da muhimmanci Najeriya ta samu gashin kai a shekarar 1957. Wannan abin bai yi wa ‘yan siyasarmu da mutanenmu dadi ba, abin da ya haifar da tarzomar da ake kira tarzomar Kano ta shekarar 1953. An yi kone-kone da kashe-kashe a Sabon-gari da sauran wuraren da ke akwai al’ummar Kudu.
Za mu iya cewa tarzomar Kano ta shekarar 1953, ita ce , tarzomar kabilanci ta farko a Nijeriya.
Dole a nan mui jinjinan ga Sardauna da sauran shugabannin Arewa bisa jajircewa da sukai a wancan zamani wajen kare martabar Arewa. Tsayin daka da sukai da jajircewar ce, ta sa daga karshe da aka rasa yadda za a yi da su, aka kashe su. An gudanar da zaben farko, kuma NPC wadda ita ce jam’iyyar Mutanen Arewa ta samu gaggarumar nasara, inda tai hadin guiwa da NCNC tasu Zik(Nnamdi Azikwe) suka kafa gwamnatin Tsakiya. Ita kuma AG (Action Group) karkashin cif Obafemi Awolowo ta zama ‘yar adawa a majalisa. Yarbawa ba su ji dadin yadda suka zama ‘yan adawa ba. Kazalika, su kan su ’yan kabilar Ibo babu yadda za su yi dole tasa suka shiga gwamnatin gambiza da NPC. Saboda haka, baki dayan jamhuriya ta farko, ba a barta ta zauna lafiya ba. Daga rikicin kidaya a shekarar 1962 zuwa rikice-rikicen zabubukan 1964 da 1965 abin da ya tilasta wa Firayiminista Sa Abubakar Tafawa balewa sanya dokar ta-baci a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya.
Wani abin da ya kamata mu sani shi ne juyin mulkin, wanda aka yi a daren 15 ga watan Janairu, 1966, an dade ana tsara shi, kuma hatta su kan su shugabannin da aka tsara za a kashe sun samu rahotan asiri cewa za a kashe su. ‘Yan siyasa, musamman jam’iyyar Yarbawa ta AG ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kawo karshen jamhuriya ta farko.
Wasu abubuwa da za a fahimta shi ne, baki dayan sojojin da suka tsara da aiwatar da juyin mulkin, ’yan kabilar Ibo ne. Kazalika, babu Ibo daya da aka kashe lokacin juyin mulkin. Amma a Arewa an kashe Firimiya,an kashe Firayinminista Tafawa balewa, ta bangaren soja, an kashe Zakari Maimalari da Kur Mohammed, wadanda duk ‘Yan Arewa ne. Sannan an kashe Cif Akintola, wanda Bayarabe ne, an kashe Okotie Eboh da sauran su, ciki har da manyan hafsoshin soja. .Amma ba a kashe Zik ba, wanda an tsara ba ya kasar lokacin juyin mulkin, kuma ba a kashe Makel Okpara ba,wanda shi ne Firimiya na bangaren Ibo, ba a kashe Aguyi Ironsi ba. Wannan duk suna nuna manufar wadanda suka aikata juyin mulkin domin duk wadannan mutane da na zana cewa ba a kashe su ba, da su ake gwamnatin.
Shin ko Shugaban kasa Nnamdi Azikwe (Zik) na da hannu a wannan juyin mulki? Wace rawa ya taka a yakin basasa? Shin da gaske Janar Hassan Usman Katsina ya goyi bayan juyin mulkin? Da sauran batutuwan da suka shafi juyin mulki na biyu da ya biyo baya, da yakin basasa da irin gudunmuwar da shugabannin wancan zamani suka bayar, al’amura ne abin bibiya.
Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina
Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka ta kasa 08165270879 Muryar talaka <[email protected]>