Shekaru biyu na Gwamna Yari: Wace riba talakan Zamfara zai karar?
A yayin da muke bikin cikar dimokradiyya shekara 14 a Najeriya, dan jarida mai zaman kansa, Malam Yusuf Abubakar, Lamba 32A Zamfara Plaza, Gusau 08035877331; ya aiko mana da wannan tsokaci:Alhaji Sani Ahmad Gwamna, dan kasuwa ne kuma shahararren dan siyasa a Jihar Zamfara, wanda ya sha gwagwarmaya na ganin dorewar jam’iyyarsa ta ANPP a […]
A yayin da muke bikin cikar dimokradiyya shekara 14 a Najeriya, dan jarida mai zaman kansa, Malam Yusuf Abubakar, Lamba 32A Zamfara Plaza, Gusau 08035877331; ya aiko mana da wannan tsokaci:
Alhaji Sani Ahmad Gwamna, dan kasuwa ne kuma shahararren dan siyasa a Jihar Zamfara, wanda ya sha gwagwarmaya na ganin dorewar jam’iyyarsa ta ANPP a bisa karagar mulki tun a farkon 1999; lokacin da jam’iyyar ta tsayar da shi domin yi mata takarar gwamna tare da Alhaji M. Z. Anka na jam’iyyar PDP.
A cewar Sani Gwamna da kusan duk wani mai son ci gaban Jihar Zamfara, hakika wannan lokacin, wannan zangon, wannan yanayi sun sha banban sosai ga al’umma dangane da tsarin siyasar ci gaba, domin kuwa Gwamna Abdul-Azeez Yari Abubakar ya sake fasalin alkiblar gudanarwa na siyasar al’ummar Zamfarawa. Jihar ta shiga yanayin canji na samun shugaba wanda yake da hankoron sake fasalta rayuwar al’ummar karkara da na birni tare da son gaskiya, ci gaba da rikon amana. Wannan shi ne Alhaji Abdul-Azeez Yari Abubakar, Gwamnan Jihar Zamfara na hudu a jerin gwamnonin da suka yi mulki kuma na ukku a jerin gwamnonin siyasa a tarihin jihar.
A tun hawansa bisa karagar mulki shekaru biyu da suka gabata, Gwamna Abdul-Azeez ya mayar da hankalinsa ne ga aiwatar da ayyukan raya kasa da ci gaban karkara, ayyuka wadanda suke da muhimmanci ga al’umma da jihar take kamfarsu. Muhimmin abu shi ne irin yadda ya fito da tsarinsa na son ci gaba ba tare da fadanci ko neman suna ba na ‘addininmu, al’ummarmu’ domin kawo nasara da habaka rayuwar al’ummar Zamfarawa, wadanda suka ba shi kuri’unsu, kamar yadda masu lura da al’amuran siyasa a jihar suke bayyanawa.
Hakika da hawansa a bisa karagar mulkin jihar, muhimmin kalubalen da ya fuskanta ga lamarin gudanarwa shi ne kokarin kakkabe fadanci da neman kusanto da wasu ’yan a-bi-yarima-a-sha-kida ke son yi masa domin lalata masa tafiya. Ya yi kokarin tabbatar da adalci bisa gaskiya da janyo kusan kowa a jiki, ta yadda ya bayyana cewar, tun bayan zabensa yanzu ya zama Gwamnan al’ummar Jihar Zamfara, ba na wata jam’iyya ko magoya bayanta ba.
Wannna matakin mai zafi na gyaran siyasar Jihar Zamfara da Gwamna ya dauka, ya sanya ya samu karbuwa sosai ga kawancen jam’iyyun adawa, tun ma kamin zabe. Haka ma ya kara masa kwarjini da bunkasa ko a cikin ’yan adawarsa a wannan jihar. Kamar yadda wani mutumin Gusau, Malam Suleiman dan Musa ya fada.
Gwamna Yari ya samu kyakkywan tarbo da amincewa ga al’umma jihar, inda ya fito fili ya bayyana wa magoya bayan jam’iyyarsa ta ANPP, wadda ya hau mulki a kanta cewa tsarin tafiyarsa tsari ne mai dauke da canji da kuma sabuwar alkibla na ‘Domin al’ummar jiharmu’ ba domin jam’iyyarmu ba.’
Ya fara da janyo ’yan adawa cikin gwamnatinsa, wadanda suka taimaka masa kafa gwamnati. Ina nufin jam’iyyu irinsu ACN, CPC, APGA da wasu sauran jam’iyyu domin tafiya tare. Kodayake daga farko wasu daga cikin jam’iyyun sun karba goron gayyatarsa, yayin da wasu suka ki, sai bayan da suka fuskanci kamun ludayinsa, abin da ya janyo suka amince da cewar hakika da gaske yake yi.
A farkon shekararsa bisa karagar mulki, ya yi kokarin gyara da neman sake tayar da komadar tattalin arzikin jihar, wanda ya maido da darajar wasu muhimman ababe da al’ummar jiharsa suke da kamfarsa. Wadannan kuwa sun kunshi gyara da sake samar da issasun ruwan sha, fuskantar matsalar ilmi da nemo hanyar magance ta, matsalar kiwon lafiya, gyara da bunkasa hanyoyin mota. Sauran sun kunshi inganta tsaro da kuma fadada aikin noma na rani da damina.
Bayan gyara da kuma sake fadada gidan ruwa na garin Gusau, Gwamna Abdul-Azeez ya mayar da hankalinsa wajen inganta lamarin samar da ruwan sha ga wasu garuruwa da suka kunshi kaurar Namoda, Maru, Talata Mafara da kuma Gummi.
Farkon aikinsa da ya hau karagar mulki, shi ne kafa kwamiti na musamman karkashin jagorancin Sanata Sa’idu dansadau, domin gano ayyuka na gaskiya wadanda aka gada da kuma tantance masu muhimmanci, wadanda za su amfani al’umma daga cikinsu.
Kwamitin ya yi aiki, inda ya gano kusan ayyuka har guda 480, wadanda gwamnatocin da suka gabata suka kirkiro ga al’ummar Jihar Zamfara. Wasu daga cikin ayyukan an kai kusan kashi 20 ko 30, yayin da wasu ba a ko fara aiwatar da komi a kansu ba.
Kwamitin a shawarar da ya bai wa gwamna ya nemi da ya mayar da hankalinsa ga ayyuka masu muhimmanci, wadanda suka kunshi Gidan Ruwan Gusau da ke bukatar kusan Naira biliyan daya da kuma Asibitin Yariman Bakura na Gusau. Sauran sun kunshi sabon gidan rediyo da kuma ginin Babbar Kotun Shari’a da ke Gusau da Hukumar Kula da Shari’a da Babban Ofishin Hukumar Ma’aikata ta jiha da sauransu.
Haka kuwa aka yi, nan take Gwamna Yari ya fara aiki tare da karbar shawarar kwamitin inda cikin taimakon Allah ya samu nasarar tabbatar da kammala wadannan ayyukan a cikin shekara daya na farkon hawansa bisa karagar mulki.
Daga nan kuma sai ya koma ga ayyukan hanya, wadanda ya lura da cewa suna janyo matsala mai yawa ga al’ummar Jihar Zamfara, mussaman manyan hanyoyin Gwamnatin Tarayya, inda ya samar da makudan kudi ga aiwatar da aikin hanyoyin, irinsu Mayanci, Anka zuwa daki Takwas da kuma kaurar Namoda, Zurmi zuwa Gidan Jaja. Dukkanin wadannan hanyoyin an kammala su kuma tare da tunanin Gwamnatin Tarayya za ta biya gwamnatin jiha wadanan kudaden ayyukan da ta aiwatar.
Wani abin sha’awa shi ne, irin yadda Gwamna Yari a cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa ya yi kokarin iyar da wasu ayyuka wadanda ya gada domin fadada ci gaban jihar.
Musamman ya kammala babbar hanyar ‘Bye Pass’ ta Gusau wadda ya sake tsarawa tare da biyan kudinta, haka ma ya gina wasu sababbin hanyoyi da kuma gidaje domin amfanin al’umma. Hanyoyin cikin gari na Gidan Dawa da na Damba duk sun samu kulawa na taimaka musu wajen rage matsalar sufuri da kuma yi wa birnin kwalliya, wanda aka yi domin amfanin al’umma mazaunan wadanan wuraren.
Bayan kamalla wannan aikin hanyoyin sai kuma ya tsunduma ga lamarin samar da hanyoyin mota na zamani ga al’ummar jihar, inda yanzu haka cikin shekaru biyu bisa mulki yake kokarin gina hanyoyi na kilomita har 467 domin amfanin al’umma.
Wasu daga cikin wadanan hanyoyin wadanda kuma ya kammala domin amfanin jama’a sun kunshi Magami, dangulbi, dankurmi zuwa Sabon Birnin Bagega zuwa Anka. Haka ma akwai Wanke-Bawa Ganga, danjibga, kuncin Kalgo zuwa Kwaren Ganuwa har Bilibis zuwa Kucheri da sauransu. Hakika Gwamna Yari ya mayar da hankali sosai domin ganin cewar an samar da ci gaban al’umma domin bunkasa musu rayuwa.