Shekau ya sake bayyana a sabon bidiyo
kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon faifan bidiyo wanda ke nuna shugabanta, Abubakar Shekau yana raye.Sashin Hausa na gidan rediyon BBC Landan ya ce bidiyon wanda ya kai tsawon kusan minti takwas ya nuna shugaban kungiyar Abubakar Shekau a wani yananyi na rashin kuzari, idan aka kwatanta da sauran faya-fayen bidiyon da ya […]
kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon faifan bidiyo wanda ke nuna shugabanta, Abubakar Shekau yana raye.
Sashin Hausa na gidan rediyon BBC Landan ya ce bidiyon wanda ya kai tsawon kusan minti takwas ya nuna shugaban kungiyar Abubakar Shekau a wani yananyi na rashin kuzari, idan aka kwatanta da sauran faya-fayen bidiyon da ya rika fitarwa a baya.
Abubakar Shekau ya bayyana a faifan bidiyon yana zaune da kayan sojoji a jikinsa kuma akwai bindiga a jingine a kafadarsa ta hagu.
A bidiyon, Abubakar Shekau yi magana da harshen Larabci da Hausa, inda ya nuna cewa kungiyar tana cikin wani hali.
Ya mika gaisuwa ga mayakansa tare da shaida musu cewa ya fitar da sabon bidiyon ne saboda ya tabbatar musu cewa yana raye. Abubakr Shekau ya jima bai fito a bidiyon kungiyar ba, tun bayan da kungiyar ta yi mubayi’a ga kungiyar ISIS a bara.