Shell ya tallafawa ‘yan gudun hijira sama da 50,000 a Arewa maso Gabas
Sama da ‘yan gudun hijira dubu 50 a sansanin garin Dikwa na jihar Borno suka samu tallafin kamfanin tace man fetur na Shell (SPDC) a wani shirin kamfanin na bayar da tallafi a harkar lafiya, tsaro, samar da ruwan sha da tsaftace muhalli da samar da ingantaccen abinci da aka fara shekara daya ya wuce. […]
Sama da ‘yan gudun hijira dubu 50 a sansanin garin Dikwa na jihar Borno suka samu tallafin kamfanin tace man fetur na Shell (SPDC) a wani shirin kamfanin na bayar da tallafi a harkar lafiya, tsaro, samar da ruwan sha da tsaftace muhalli da samar da ingantaccen abinci da aka fara shekara daya ya wuce.
Kamfanin tace man fetur na Shell tare da sauran ma’aikatan reshen kamfanonin a Najeriya sun bayar da tallafin kudi dala miliyan 1.1 akan fannin kiwon lafiyan iyali a shekara.