Shema ka tabbatar da dorewar tallafin ilimin’ya’ya mata
Daga Kabir Saulawa ’Ya’yan da suka rasa dammar neman ilimi a da, yanzu ana damawa da su, musamman ’ya’ya mata, wadanda matsalar zamantakewa da tattalin arziki da al’adu da addinai suka kange su, sun kasance abin damuwa a wajen Gwamna Ibrahim Shehu Shema na Jihar Katsina, tun sa’adda ya kama ragamar mulki a shekarar 2007. […]
Daga Kabir Saulawa
’Ya’yan da suka rasa dammar neman ilimi a da, yanzu ana damawa da su, musamman ’ya’ya mata, wadanda matsalar zamantakewa da tattalin arziki da al’adu da addinai suka kange su, sun kasance abin damuwa a wajen Gwamna Ibrahim Shehu Shema na Jihar Katsina, tun sa’adda ya kama ragamar mulki a shekarar 2007. Don haka ko wata tantama babu shi yasa Gwamnatin Shema ta bullo da bayar da tallafin kudi ga iyaye mata da suka kyale ’ya’yansu su tafi neman ilimi, suka kuma karfafa musu gwiwa.
Irin wannan tallafi ya yi matukar tasiri wajen bunkasa ilimin ’ya’ya mata, amma bai kamata ya tsaya a kan kudi kadai ba. Wasu masanan na ganin ya kamata Gwmana Shema ya hada bunkasa sana’o’in mutanen karkara, ta yadda idan iyaye mata na da abin dogaro, ko gwamnati ta ba su tallafin dubu biyar ko ba ta bayar ba, a kashin kansu za su tura ’ya’yansu makarantun ilimin addini da na zamani. Kodayake uwargidan gwamna Shema na da shirin horar da mata a kan sana’o’in hannu, to a akwai bukatar a bunkasa shirin ta yadda zai shiga manhajar makarantun Firamare da na Islamiyya da ke fadin Jihar Katsina.
Matakin farko da gwamnatin shema ta dauka na ganin cewa ana samar da ingantaccen ilimi, ta hanayar horar da malamai da samar da kayan aikin koyarwa. An kuma yi wannan hobbasa ne don a cike gibin da ke tsakanin jinsi wajen samun ilimi mai alfanu. Saboda a cimma wannan manufa aka jajirce wajen ganin cewa mutanen karkara da na birnin duk sun smau dammar halartar makarantu don koyon ilimin zamani.
Hakika mutanen Jihar Katsina sun yaba da shirin nan na tallafa wa iyaye mata da suka bar ’ya’yansu suka shiga makaranta don kyon ilimin zamani, inda aka riba ba su Naira dubu biyar. Ba ma wannan kadai ba, har ma da bai wa sashen ilimi kaso mai tsoka a kasafin kudi. Wannan namijin kokari ya sanya aka cimma shigar da kananan yara sama da miliyan guda mkarantun Firamaren da yawansu ya kai dubu biyu da 203; an kuma horar da malamai sama da dubu biyar. Hasali ma dai Gwamnatin tarayya da kanta ta tabbatar da cewa, a tsarin Ilimin Bai daya na UBE, Jihar Katsina ta sha gaban sauran jihohi, a tsakanin shekarun 2005 zuwa 2008. Kuma wannan martaba da Jihar Katsina ta samu, an hado lambar yabon da motar Hilud da tsabar kudi Naira miliyan 700. Hakika wannan kyauta ta kara wa jiharmu karsashin ci gaba da managartan ayyukan bunkasa ilimi.
Sanin kowa ne Jiharmu na da isassun malamai da ke koyarwa a makarantun Firamare, wadanda suka jajirce wajen bayar da ilimi ingantacce. Kuma ana bayar da tallafin karatu a kowane amtaki na ilimi, ind aa halin yanzu dalibai da dama sun samu guraben karatu a nahiyoyin Afirka da Amurka da Turai da Asiya. Sannan gwamnati na kokarin biyan kudin tallafin karatu a kan kari.
Tun daga shekarar 2008, Jihar Katsina ce kawai t ayi kokarin bunkasa ilimin mata, inda a kalla kimanin kasha 70 cikin 100 na wannan rukuni ke cin gajiyar tallafin hadin gwiwa na miliyoyin Naira da Asusun raya ilimin kananan yara na Majalisar dinkin Duniya da Hukumar tallafa wa ci gaban al’ummomi a kasashen duniya ta DFID suka fito d ashi, inda ‘’ya’ya mata kimanin dubu 600 suka shiga makarantun zamani.
Babu kasar da za ta ci gaba, ta samu makoma mai kyau, sai ta zuba dimbin jari a fannin ilimi, musamman ma ganin cewa, wannan manufa tana cikin kudurorin majalisar dinkin Duniya da Muradun karni don kyautata rayuwar al’umma. Ganin cewa ci gaban al’umma ya dogara kacokam wajen ilimi, watakila shi yasa Gwamna Shema ya kara matsa kaimi, wajen bai wa fannin ilimi fifiko tun daga shekarar 2007, ta hanyar bunkasa ilimin ’ya’ya mata.
Masu nazari kan harkokin ilimi a Jihar Katsina da ma kasa baki daya za su iya tabbbatar da cewa, tallafin da ake bai wa iyaye mata ya yi matukar tasiri wajen bunkasa ilimin ’ya’ya mata a wannan jiha, amma babbar matsalar ita ce yaya za a yi wannan shiri ya dore ko da Gwamna Shema na mulki ko wnainsa? Wannan tambayar ita ce abin da ya kamata a bijiro da ita ga daukacin wadanda ke hankoron samun mukaman siyasa a wannan jiha. Al’umma Jihar Katsina dole ne mu tabbatar ana tallafa wa iyalai masu rauni, musamman iyaye mata don kada su zabi tallace-tallace a kan ilimi. Lallai akwai bukatar tsari mai dorewa, musamman ganin cewa idan aka ilimantar da mace, gajiyarta ta fi a ilimantar da da namiji a wani yanayin. Uwa-uba, kannan yara daga iyaye mata suke fara samun ilimin zamantakewa.