Shema ya yi katobara
Gwamnan Jihar Katsina Baristsa Ibrahim Shehu Shema ya samu kansa a tsaka mai wuya bayan da ya bayyana ’yan jam’iyyar adawa da kyankyasai kuma ya bukaci magoya bayan jam’iyyarsu ta PDP su buge duk wani dan adawa da ya tsaya a hanyarsu. Gwamnan wanda ke jawabi ga wani taron magoya bayan Jam’iyyar PDP a Katsina […]
Gwamnan Jihar Katsina Baristsa Ibrahim Shehu Shema ya samu kansa a tsaka mai wuya bayan da ya bayyana ’yan jam’iyyar adawa da kyankyasai kuma ya bukaci magoya bayan jam’iyyarsu ta PDP su buge duk wani dan adawa da ya tsaya a hanyarsu.
Gwamnan wanda ke jawabi ga wani taron magoya bayan Jam’iyyar PDP a Katsina ya kwatanta ’yan adawar ne da “kyankyasai,” inda wasu daga cikin magoya bayansa suka ce babu abin da ya cancanta da su illa kisa.
Ya ce, “Siyasar da muka yi a da, an yi wa mutanen PDP rashin kunya, an yi musu wulakanci, an ci musu fuska, mun ce a yi hakuri, to yanzu duk wanda duk ya ja ku, ku maida masa; inji ni, babu sassauci.”
Gwamna Ibarhim Shema ya ci gaba da cewa: “Kuma kada ku damu da kyankyasan siyasa. Kyankyaso ko a gida a masai ake samunsa,” sai ya tambayi magoya bayansa cewa “Idan ka ga kyankyaso a gidanka mai kake masa?” Sai magoya bayan jam’iyyar tasa suka ce “Kashe shi ake yi.” Shi kuma Gwamnan ya ce, “To ku buge su!”
Wadannan kalamai dai sun harzuka ’yan hamayya, musamman magoya bayan babbar jam’iyyar adawa ta APC da jagoranta kuma na sahun gaba a masu neman tsaya mata takarar Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari daga Jihar Katsina yake.
Magoya bayan Jam’iyyar APC sun bayyana kalaman na Gwamna Shema da magoya bayansa a matsayin wani yunkuri na tayar da tarzoma, musamman ganin Gwamnan masanin shari’a ne, amma sai ga shi yana magana irin wadda ta saba fitowa daga ’yan bangar siyasa masu karancin ilimi.
Fiye da kashi biyu bisa uku na zababbun ’yan siyasar Jihar Katsina sun fito ne daga Jam’iyyar APC wadda take da sanatoci uku da wakilan Majalisar Tarayya sama da 10.
Sun kara da cewa bai kamata mutum mai matsayi irin na Gwamna ya yi irin wadannan kalamai ba.
A lokutan baya ma tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya taba bayyanawa a lokacin da yake mulki cewa, zaben da za a gudanar irin na “a mutu ko a yi rai ne,’’ kalaman da ake ganin ba su dace su fito daga bakin Shugaban kasa ba. Haka shi ma Shugaba Jonathan akwai lokacin da aka taba tambayarsa dalilin da ya sa ya ki bayyana kaddarorin da ya mallaka, kamar yadda marigayi Shugaba Umaru ’Yar’aduwa ya yi, sai ya ce, “babu abin da ya dame ni.” Da wadannan kalaman ne ake danganta shi duk lokacin da ya yi wani abu da ake ganin bai dace ba.
Sau da yawa ’yan siyasa kan yi subul-da-baka a lokutan da suke yin jawabi a gaban magoya bayansu, sai daga baya kuma abin ya dame su.