Shettima ga Jonathan: Tilas a shawo kan matsalar Boko Haram
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya shaida wa Shugaban kasa Goodluck Jontahan cewa “ba zai yiwu a ci nasara kan Boko Haram ba” matukar ba a kara yawan sojoji da kayan yaki zuwa yankunan da ake tashin hankali ba.Gwamnan ya bayyana haka ne ga manema labarai bayan ya gana da Shugaban kasara ranar Litinin […]
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya shaida wa Shugaban kasa Goodluck Jontahan cewa “ba zai yiwu a ci nasara kan Boko Haram ba” matukar ba a kara yawan sojoji da kayan yaki zuwa yankunan da ake tashin hankali ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne ga manema labarai bayan ya gana da Shugaban kasara ranar Litinin da ta gabata a Abuja, inda ya ce mayakan da ke kai hare-hare sun fi sojojin kayan yaki da karfin hali.
Shettima yana Fadar Shugaban kasar ne domin yi masa bayani kan hare-haren bayan nan da suka salwantar da rayukan daruruwan mutane a cikin mako daya.
A ranar Asabar da ta gabata ce mayakan da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai hari kauyen Izge da ke kusa da iyakar jihar da Adamawa inda suka halaka mutum 106 nan take. Kuma zuwa ranar Litinin din an ce wadanda suka mutu a harin sun kai mutum 133.
Kwana daya kafin harin na ranar Asabar, an kashe sojoji tara a garin, yayin da fiye da mutum 50 suka rasa rayukansu a garin Konduga a wani harin na daban kwana biyu baya.
Shettima ya yi bayani ga Shugaban kasar ne a gaban hafsoshin bangarorin soja wadanda suke ganawa da shi a daidai lokacin.
Shettima ya fadi cikin sassanyar murya kamar zai yi kuka cewa: “A takaice abin da ke fuskantarmu shi ne muna wani yanayi na yaki. Kuma shi ne abin da na zo shaida wa hugaban kasa. Hanzarta daina rikon sakainar kashi ga lamarin da mikewa don fuskantar kalubalen halin da ake ciki da yin amfani da albarkatu wajen magance matsalar Boko Haram ne kawai zai haifar mana da alheri dukkanmu. Hakikan lamarin muna bukatar karin kudi da sojoji a kasa.”
Gwamnan ya ce sojoji da ’yan sanda na kokarinsu lura da halin da suka samu kansu a ciki, sai dai gaskiyar lamari Boko Haram sun fi su makamai. Ya ce yana da tabbaci kamar yadda ya sha fadi lura da halin da ake ciki, zai yi wahala a murkushe Boko Haram. “Na shaida wa Shugaban kasa balo-balo cewa Boko Haram sun fi sojojinmu makamai da karfin hali,” inji shi.
Gwamna Shettima ya ce “Duk mai lura da al’amuran da ke gudana a kasar nan, zai ga cewa suna gudanar da ayyukansu a tsanake suna murkushe garuruwa da kashe jama’a. Shin mun samu nasarar wargaza daya daga cikin shirye-shiryensu?”
Ya kara da cewa: “Sun je Konduga sun yi abin da suka ga dama. Sun zauna na tsawon awa biyar kafin su bar garin. Sun je Kawuri da Izge, ba na zargin sojojin Najeriya. Gaskiya mu shugabanni ne za a dora wa laifi kan gazawarmu.”
Ya ce Shugaban kasar ya ba shi tabbacin zai yi kokari domin ganin an kawo karshen auka wa kauyuka da yayyanka mutanen da ba su san hawa ko sauka bad a Boko Haram ke yi.
Game da yana ganin zai yiwu a gudanar da zabe a Jihar Borno a badi, ganin rashin tsaron da ake fama da shi, ya ce wauta ce ga wani ya yi maganar zabe a lokacin da rayukan jama’a suke cikin hadari. Ya ce abin da ya fi damunsa a samu zaman lafiya a Borno da Arewa maso Gabas, don haka jama’a su daina sanya siyasa a cikin lamarin.
A wani labarin kuma Hedikwatar Tsaro ta kasa ta ce an kara tura sojoji zuwa yankunan da ake kai hare-haren inda ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa a kauyukan Jihar Borno da ke jawo asarar rayukar fararen hula masu yawa.
Sanarwa da hedkwatar tsaron ta fitar dauke da sanya hannun kakakinta Manjo Janar Chris Olukolade ta bukaci jama’ar yankunan da lamarin ya shafa su gaggauta sanar da jami’an tsaro da zarar sun ga wani abu.
Ta ce hare-haren da ’yan kungiyar Boko Haram suka kai a ’yan kwanakin nan, ba zai sa guiwar su ta yi sanyi ba a kokarin da suke yi na magance ayyukan ta’addanci a kasar. Ta ce a yanzu haka dakarunta sun zage dantse wajen farautar masu tada kayar baya da suka addabi jama’a a wasu yankunan Jihar Borno da Yobe da Adamawa.