Shettima ya dawo Najeriya bayan halartar taro a Guinea da Switzerland
Najeriya na ci gaba da tallata kanta a wajen masu zuba zari na ƙasashen waje.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Abuja bayan shafe mako guda yana ziyarar aiki a ƙasashen Guinea da Switzerland.
Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da Shugaban Ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya.
- HOTUNA: Sarkin Zuru ya gana da Ministan tsaro kan matsalar tsaro a Jihar Kebbi
- ’Yan Boko Haram sun kashe Fasto da mafarauta biyu a Borno
Daga nan kuma ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron Tattalin Arziƙin Duniya (WEF) karo na 56 da aka gudanar a birnin Davos na ƙasar Switzerland.
Bayan dawowa gida, Shettima ya ce Najeriya ta samu matsayi a tattaunawar siyasa da tattalin arziƙi a duniya.
A Guinea, ziyararsa ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa rawar jagorancin Najeriya a Yammacin Afirka da kuma bunƙasa haɗin gwiwa a ɓangarorin noma da masana’antu.
A Davos kuwa, ya jagoranci tattaunawa da masu zuba jari, tare da ƙaddamar da ginin ‘Nigeria House Davos’, cibiyar da za ta riƙa tallata damar zuba jari a harkokin noma, albarkatun ƙasa da tattalin arziƙin zamani.
Shettima, ya kuma bayyana cewa tattalin arziƙin Najeriya na samun tagomashi, inda ake sa ran samun bunƙasar tattalin arziƙi a shekarar 2026.
Har ila yau, ana sa ran samun ragin hauhawar farashi, bunƙasa tsaron abinci, da kuma shirin ƙasar na zama babbar mai fitar da man fetur da aka tace.