Shettima ya dawo Najeriya bayan halartar taron MDD

A yayin taron ya bayyana buƙatar yadda za a yi sauye-sauye kan ci gaban ƙasashen duniya.

Shettima ya dawo Najeriya bayan halartar taron MDD

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Abuja bayan wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 da aka gudanar a birnin New York da ke Amurka.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi.

A lokacin taron, Shettima ya gabatar da jawabi, inda ya buƙaci shugabannin duniya da su sake fasalin kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ya jaddada buƙatar Najeriya da sauran ƙasashen Afrika su samu kujerun dindindin, inda ya ce cewa canji ya zama dole domin Majalisar Ɗinkin Duniya ta ci gaba da yin tasiri a wannan zamani.

Ya ce wasu daga cikin mambobin kwamitin tsaro na dindindin sun nuna goyon baya kan batun sake fasalin, inda ya buƙaci a gaggauta yin hakan.

Shettima, ya jaddada cewa ya kamata a ƙara yawan mambobin dindindin da waɗanda ba na dindindin ba, domin su wakilci bambance-bambancen duniya.

Ya kuma nuna goyon baya ga ƙoƙarin Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, kan wannan batun.

Shettima, ya tunatar da shugabannin cewa Majalisar Ɗinkin Duniya tana wakiltar haɗin kai, kuma tana mai da hankali kan zaman lafiya, ci gaba mai ɗorewa, da kare haƙƙin bil’adama.

Ya nuna damuwarsa kan matsalolin duniya da suka haɗa da ta’addanci, talauci, rashin daidaito, da sauyin yanayi, inda ya ce waɗannan matsaloli suna nuna yadda duniya ta gaza.

Ya kuma nuna damuwarsa kan juyin mulkin soja da ya faru a wasu ƙasashen Afrika, wanda ya yi gargaɗin cewa dimokuraɗiyya na cikin hatsari idan ba tare da ci gaban tattalin arziƙi da zaman lafiya ba.

A lokacin da yake a birnin New York, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yi taruka da dama tare da halartar wasu muhimman abubuwan da aka gudanar a wajen taron.

Nkwocha ya ƙara da cewa Shettima zai haɗa kai da Shugaba Tinubu don halartar wasu taruka da aka shirya domin bikin cika shekara 64 da samun ‘yancin kan Najeriya.