Shettima ya gana da Ministan Man Fetur da Shugaban NNPCL

‘Yan Najeriya ke yin tattaki mai nisa zuwa wuraren bukata.

Shettima ya gana da Ministan Man Fetur da Shugaban NNPCL

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gayyaci Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, zuwa fadar shugaban ƙasa ta  Aso Rock.

Shi ma mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya halarci taron wanda ba zai rasa nasaba da ƙarin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan ba.

Haka kuma a taron akwai wasu jami’an gwamnati daga ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

Ƙarin farashin man fetur na baya-bayan nan ya sa kara tsadar kurin sufuri da fiye da kashi 50 a manyan biranen Najeriya.

Sabon ƙarin farashin, wanda ‘yan kasuwa da ke hulɗa da Kamfanin Dillancin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) suka  aiwatar, ya tashi daga Naira 855 zuwa N897 kowace lita, inda ake samun ’yan bambance-banbamce, ya danganta da shiyyar sassan ƙasar.

‘Yan kasuwa masu zaman kansu sun kayyade farashin duk litar man fetur daya a tsakanin N930 zuwa N1,200.

Ƙarin farashin dai ya yi tasiri matuƙa, inda wasu ‘yan Najeriya ke yin tattaki mai nisa zuwa wuraren bukata, yayin da wasu kuma sun rasa aikin yi saboda tsadar sufuri.

Farashin ya ƙaru kwanaki biyu bayan da Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPC, Olufemi Soneye, ya sanar da cewa kamfanin na fuskantar matsalar kuɗi da hakan ke barazana ga ɗorewar wadatuwar man a kasar.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi