Tsige Sarkin Musulmi: Shettima ya gargadi Gwamnan Sakkwato

Sarkin Musulmi ba abin wasa ba ne, in ji Shettima ga Gwamantin Sakkwato

Tsige Sarkin Musulmi: Shettima ya gargadi Gwamnan Sakkwato

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar. (Hoto: Twitter.com/officialEFCC).

Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya gargadi Gwamnan Jihar Sakkwato kan yunkurinsa na tsige Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.

Shettima ya bayyana cewa darajar kujerar Sarkin Musulmi ta wuce iya Jihar Sakkwato, don haka ba abar was ba ce, kuma wajibi ne a ba shi kowace irin kariya da girmamawa.

Shettima ya bayyana haka ne a yayin da ake rade-radin Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu na shirin tube rawanin Sarkin Musulmi.

“Sakona ga Mataimakin Gwamnan Sakkwato (wanda ke wakiltar gwamnansa a nan) mai sauki ne: hakika Sultan na Sakkwato a karkashin Jihar Sakkwato yake, amma tabbas darajarsa ta wuce iya nan.

“Sarkin Musulmi wani bango ne da dukkanmu a wannan kasar ke bukatar mu mutunta tare da ba shi kariya da goyon baya mu kuma adana,” in ji mataimakin shugaban kasar.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron tsaro da zaman lafiya na yankin Arewa maso Yamma a ranar Litinin a Kastina.

Mataimakin Gwamnan Sakkwato ne ya wakilci Gwamna Ahmad Aliyu a taron.

Aminiya ta ruwaito Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi (MURIC) ta zargi Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu da yunkurin tsige Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.

Babban-Daraktan MURIC, Farfesa Isiaq Akintola, ya bayyana takaici bisa abin da ya kira shirin gwamnan na fakewa da dalilinsa na tsige wasu sarakunan gargajiya 15 a matsayin hujjar tube Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.

Sarkin Musulmi shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya da kuma Kungiyar Musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI).

A watan Afrilu ne gwamnan ya Aliyu ya tube wasu sarakunan gargajiya 15 kan laifukan da suka danganci rashin tsaro da kuma rikicin filaye a jihar.

Ya ci gaba da cewa, “a kowane lokaci gwamnan na iya far wa kujerar Sarkin Musulmi da dalilin da ya bayar na tube wadancan sarakuna 15 a kwanakin baya.”

Amma ya jaddada cewa Musulmin Najeriya za su tsaya kai da fata su yaki duk wani yunkuri na tsige Sarkin Musulmi.

Abin da Gwamnatin ta ce

Tuni bangaren zartaswa na Jihar Sakkwato ta mika wa majalisar dokokin jihar kudurin yin gyaran fuska ga dokar masarautun jihar domin dacewa da yanayin jihar.

Dokar masarautum jihar ta yanzu ta damka ikon nada hakiman da dagattai a hannun Majalisar Fadar Sarki.

Amma duk da haka a zahiri shawara kawai fadar take ba wa bangaren gwamnatin, inda a karshe gwamnan jihar ke nada masu sarautun.

Amma da yake karin bayani kan sabuwar dokar, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Sakkwato, Nasir Binji, ya bayyana ce za a yi gyare-gyaren ne nomin ganin tsarin aarautar gargajiya ta yi daidai da tsarin shari’a.

Nasir Binji, ya sanar da manema labarai cewa sabuwar dokar da ake shirin yi ta ba wa Majalisar Sarkin Musulmi ikon mika sunayen mutanen na za a ba wa saraut, amma ta ba wa gwamna ikon yin nadin.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda