Shettima ya halarci jana’izar Kwamishinan Borno

Kwamishinan ya rasu da sanyin safiyar ranar Litinin a gidansa da ke Maiduguri.

Shettima ya halarci jana’izar Kwamishinan Borno

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya halarci jana’izar, Kwamishinan kuɗi da ci gaban tattalin arziƙi na Jihar Borno, Alhaji Ahmed Ali Ahmed, tare da Gwamna Babagana Umara Zulum.

Jana’izar ta gudana ne a ranar Litinin a Maiduguri.

Babban limamin Borno, Imam Laisu Ibrahim ne, ya jagoranci sallar jana’iza.

Ahmed, ya rasu a gidansa da ke Maiduguri, kuma yana da shekara 42 a duniya.

Ya bar mata da yara biyu, da ’yan uwa da dama.

Kafin rasuwarsa, shi ne kwamishinan kuɗi da ci gaban tattalin arziƙi na Jihar Borno.

Ya yi aiki da bankin Zenith Bank sama da shekara 17, inda ya kai matsayin Mataimakin Manaja kafin shiga siyasa.

Jama’ar da suka halarci jana’izar sun haɗa da Mataimakin Shugaban APC, Ali Bukar Dalori, Sanata Kaka Shehu Lawan, ’Yan Majalisar Wakilai, Shugaban APC na Jihar Borno, Bello Ayuba, da ’Yan Majalisar Dokoki na Jihar.

Shehun Borno, Abubakar Umar Garbai Elkanemi, da sauran mambobin Kwamitin Sarakunan Borno sun halarci jana’izar.

Har wa yau, mambobin Kwamitin Zartarwa na Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Bukar Tijani, da sauran ’yan siyasa da jami’an gwamnati sun halarci jana’izar.

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur