Shettima ya kaddamar da aikin Abba a gidan gwamnatin Kano

Shettima ya kaddamar da ginin ofishin Gwamnan Kano da Abba Kabir Yusuf ya yi wa kwaskwarima

Shettima ya kaddamar da aikin Abba a gidan gwamnatin Kano

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya kaddamar da katafaren ginin ofishin Gwamnan Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa kwaskwarima a cikin gidan gwamnatin jihar.

Ginin, mai dauke da bangaren majalisar zartarwa, dakin taro, da masaukin baki na alfarma na zamani, Gwamnan Kano a zamanin mulkin soja, Marigayi Kwamishinan ’Yan Sanda Audu Bako ne ya gina shi a shekarar 1967.

Shettima ya yaba da jajircewar Gwamnan Abba wajen ganin an kammala aikin a kan lokaci.

“Ina taya Gwamna Abba Kabir Yusuf da ’yan majalisar zartarwa murna kan wannan nagartaccen aiki,” in ji Mataimakin Shugaban Kasan.

Ya ce gyaran ofishin da na’urorin zamanin da aka sanya za su samar da kyakkyawan yanayin aiki ga gwamnan da ma’aikata don yu aiki yadda ya kamata domin kawo cigaba mai ma’ana.

Shettima ya samu rakiyar Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, da Sanata Kawu Sumaila, da Mataimakin Gwamnan Jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Mataimakin Shugaban Kasa da tawagarsu sun je Kano ne a ranar Laraba domin ta‘aziyyar marigayi Right Hon. Ghali Umar Na’abba wanda ya rasu a safiyar ranar.