Shettima zai wakilci Tinubu a taron G77 a Cuba
Mataimakin shugaban kasar zai bar Abuja a ranar Laraba.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima zai wakilci Shugaban Tinubu a taron shugabannin kasashen G77 a Havana, babban birnin kasar Cuba.
Kakakin ofishin mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola, ya sanar cewa a yayin taron, Shettima zai hadu da sauran shugabannin kasashen duniya, ciki har da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres a wajen taron inda za su tattauna kan ci gaban kasashen kungiyar.
- Faransa ta roki Morocco kan ta karbi tallafin da ta ke so ta ba ta
- ’Yan Najeriya 936 sun rasu a hatsarin kwalekwale a shekara 3
Taron dai zai lalubo hanyoyin magance kalubalen da ke fuskantar cigaban kasashen kungiyar ta hanyar amfani da kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire don bunkasa zamantakewa da tattalin arziki.
Abiola ya kara da cewa, Shettima zai gana da wasu shugabannin duniya domin inganta huldar kasuwanci da zuba jari a Najeriya daidai da tsarin gwamnatin Tinubu na bunkasa tattalin arziki.
Shugaban kasar Cuba Miguel Díaz-Canel ne, zai karbi bakuncin taron na Havana a matsayinsa na shugaban kungiyar G77 da kasar Sin.
Ƙungiyar, wadda hadin gwiwar kasashe masu tasowa 134 tare da kashi 80 na yawan jama’ar duniya ce, na da burin inganta manufofin tattalin arziki na mambobin kungiyar.