Shigar Atiku APC: Banza ba ta kai zomo kasuwa

An dai ce zabuwa ba ta goge zanen jikinta, kamar yadda mai hali bai barin halinsa. Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar Turakin Adamawa ya sake  ficewa daga jam’iyyar PDP, a karo na biyu, ya koma jam’iyyar APC wacce yake ganin ita ce za ta  magance masa dukkan matsalolinsa na siyasa da suke sa […]

Shigar Atiku APC: Banza ba ta kai zomo kasuwa
Shigar Atiku APC: Banza ba ta kai zomo kasuwa

An dai ce zabuwa ba ta goge zanen jikinta, kamar yadda mai hali bai barin halinsa. Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar Turakin Adamawa ya sake  ficewa daga jam’iyyar PDP, a karo na biyu, ya koma jam’iyyar APC wacce yake ganin ita ce za ta  magance masa dukkan matsalolinsa na siyasa da suke sa shi tsilla-tsilla da tsilli-gudidi.
Turaki Atiku dai jigo ne a jam’iyyar PDP, kuma tare da shi aka yi hakilon kafa ta, yana kuma kan gaba wajen habaka ta da kuma tarairayar ta har sai da ta kama kasa. Duk da cewa  jam’iyyar PDP ta muzanta shi, ta ki tsayar da shi takarar shugabancin kasar  nan a shekarar 2003, Turaki Atiku bai fice daga jam’iyyar ba, haka nan ya yi ta zaman tammahan-wa-rabbuka a cikinta har ya zuwa 2007, inda a wannan lokacin ma aka nuna mar iyakarsa, yana ji, yana gani zama cikin jam’iyyar ya fi karfinsa har sai da ya tattara ‘yan komatsansa ya koma jam’iyyar AC a  shekarar 2006, inda aka share mar hawayensa na kukan rashin tsayar da shi takara a jam’iyyar PDP.
Ko a wancan lokacin ma hakar Atiku ta mulkin kasar nan ba ta cimma ruwa ba, bai kuma hakura da hankoron zama shugaban kasa ba. Sai ya sake komawa inda aka makanta shi don a ja masa gora, watau jam’iyyar PDP, ya kasa, ya tsare, da fatan zai cimma burinsa. To amma Turaki Atiku ya tarar da shukar da ya yi a jam’iyyar PDP ta girma, wadanda ya bari a cikinta sun girbe, sun zuba a rumbunsa don su mayar masa da aniyarsa. Haka nan dai ya zama dan bora a jam’iyyar da ya taimaka wajen kafuwarta, kuma daga karshe da ya ga ba ta da sauran mamora a gare shi, sa’annan kuma burinsa a cikin jam’iyyar ya zame wutsiyar rakumi a gare shi, sai ya rungumi kaddara, ya nemi sake sheka ko wani ramin da zai kutsa, domin ya rigaya ya zame maciji wanda bai ramin kansa.  Shi ya sa ya tunkari jam’iyyar APC  domin ya fi ganin ta a can, kuma mai yiwu ne ya tsinci dami a kala.
To da ma wai shin Turaki Atiku da biyu ne ya koma jam’iyyar APC don ya huta da kawazuccin shugabancin kasa da yake ganin ta yi masa nisa a jam’iyyar PDP, ko kuwa don ya sabunta kokarinsa ne na kai wa ga biyan wannan bukatar a APC?  A, to, ai sanin gaibu sai Allah. Amma ai dukkan aiki na dogara ne bisa niyyar da aka yi don aiwatyarwa. A dukkan lokutan da Atiku ya yi walle-walle zuwa wata jam’iyya  sai ka tarar cewa sabuwa ce fil da aka samar bayan hadin gwiwar wasu jam’iyyu. Da farko dai bayan ta kwabe wa su Sanata Ahmed Bola Tinubu a jam’iyyar Alliance for Democracy, AD ne sai suka kafa jam’iyyar Action Congress  AC, daga baya suka hadu da wani bangare na AD, suka kafa Action Congress  of Nigeria, AC wacce daga baya Turaki Atiku ya lalaba cikinta don ya yi takarar shugabancin da bai samu nasara ba. To bayar sun fatattake shi ne daga cikin jam’iyyar sai suka canja sunanta zuwa ACN. A yanzu ma ga shi nan ya sake dumfarar wata jam’iyyar gamin gambiza, kuma ana kyautata zaton cewa kulafucin shugabancin kasa ne ya hankada shi cikinta.
Haka nan ma a zaben 2011 Turaki Atiku ya sake amayar da maitarsa don kame kurwar kujerar shugaban kasa, yayin da wasu wadanda suka kira kansu shugabannin Arewa, ‘ya’yan jam’iyyar PDP, wadanda suka ce suna tsananin kishinta, suka kadawa talakawan yankin walawala, suka kuma dauki mara cin. A lokacin ne aka ce an fitar da Turaki Atiku a matsayin dan takarar Shugabancin kasa, abin da ya kai jama’an Arewa guna-guni ganin cewa al’amarin bai shafi daukacin mutanen Arewa ba, tsari ne na PDP don a kwashe kafafun  Janar Buhari, dan takarar jam’iyyar CPC  da aka tabbatar Arewa da sauran wasu sassan kasar nan sun fi raja’a a kansa.
To yanzu Turaki Atiku ya ce bayan ya kammala waiwayar wadanda ya kamata ya tuntuba, ciki har da wadancan masu da’awar kishin Arewar da suka yi tabargazar tsayar da shi don a sayar da Arewar, sai ga shi nan suna son sake daurewa karya gindi.  Shigar  Turaki Atiku cikin sabuwar APC ya sanya an ci gaba da yaudarar Arewa ta tsohuwar hanyar da aka saba, domin kuwa ana nan ana ta kulle-kullen toshe kafar fitowar dan takarar da jama’ar Arewa suka kosa su nuna wa karimci mamakon wanda hankalinsu bai kwanta da shi ba.
Kaman yadda aka yaudari jama’a a 2011 da cewa za a tsayar masu da dan takara guda wanda rubabbun kayar Arewa suka gabatar, a wannan karon ma suna ta kokari ne don fitar da dan takarar shugabancin kasa daga shiyyar Arewa-maso-Gabas domin shugaban kasa bai taba fitowa daga yankin ba, ganin yadda yankin Arewa-maso Yamma ya sha fitar da shugabannin kasa, na soja da na farar hula. Ta haka ne ake son a share fagen sake dora Turaki Atiku, daga shiyyar Arewa-maso gabas takara. Ashe ke nan ana iya cewa biri ya yi kama da mutum, domin kuwa haka nan kawai, zikau-mikau, Turaki Atiku ba zai yi kasadar barin PDP ba ya tsunduma cikin jam’iyyar APC. Yana dai na so ne bayan an gama nika ya kwashe garin. Takarar shugabancin kasa yake so ya yi, domin banza  ba ta  kai zomo kasuwa.