Shigar Najeriya kawancen yaki da ta’addanci ta tayar da kura
Harkar tsaro ce ba ta addini ba – kungiyar JNI Shugaban Jama’atu Nasril Islam na Jahar Kaduna Malam Ja’afaru Makarfi ya nuna goyan bayansa ga bayanin da babban Sakataren kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) Dokta Khalid Abubakar Aliyu ya yi a kan batun shigar Najeriya cikin hadakar kasashen musulmi masu yaki da ta’addanci, inda ya […]

Harkar tsaro ce ba ta addini ba – kungiyar JNI
Shugaban Jama’atu Nasril Islam na Jahar Kaduna Malam Ja’afaru Makarfi ya nuna goyan bayansa ga bayanin da babban Sakataren kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) Dokta Khalid Abubakar Aliyu ya yi a kan batun shigar Najeriya cikin hadakar kasashen musulmi masu yaki da ta’addanci, inda ya nuna cewa a hakikanin gaskiya babu wani abin damuwa ko tsaro dangane da shiga kawance da kasashen larabawa domin yaki da ta’addanci.
“Ni a gaskiya ina goyan bayan jawabin da babban Sakatarenmu ya yi, don haka ban ga dalilin da zai sai su kiristoci su rika dari-dari da duk wani abu da ya shafi musulunci ba. Babu wani dalili da za su rika yin dar-dar da wannan kawance, domin abu ne da ya shafi kowa da kowa.’’
“Kuma ai mu musulmi ba mu taba nuna damuwa mu a kan cewa kiristocin kasar nan suna da wakilci a batican ba, amma idan abu ya shafi musulmi sai su ce wai su ba su yarda ba. Kuma gashi wannan zance na ta’addanci kowane bangare ya shafa. Misali, dubi wannan batu na takaita wa’azi da gwamnatin jahar Kaduna ta fito da shi ko take kokarin fito da shi, mu musulmi da dadewa muna da wannan dokar, wanda har an taba yi mata garanbawul, inda dokar ke hana suka da zagi wajen yin wa’azi.
“Game da wannan kawancen, ai a shekarun baya mun sha fadin cewa Boko Haram ba musulunci ba ne, amma ai ba su yarda da hakan ba, sai da suka ga cewa suna kashe musulmi da kiristoci sannan suka yarda da abun da muke fada masu. Saboda haka ne muka kara jan hankalinsu da su sani cewa shi wannan zance na kawance da shugaban kasa ya shiga ai batu ne na tsaro da ya shafi kowa da kowa a kasar nan. Kuma ai su wanda suke takama da su a duniya ai kasar Amurka ce, kuma Saudiya ai ba ta da wata kawa a duniya da ta wuce kasar Amurka. Kuma kasashen Amurka da na turai ai sun dade suna shiga kawance domin yaki da ta’addanci a kasashe. Saboda haka mu a wajenmu wannan kawance zaman lafiya zai kawo wa kasar nan kuma muna goyan bayansa. Ina kuma ganin akwai bukatar su ma su goyi bayan wannan mataki da musulmi suka dauka domin samar da zaman lafiya a kasar nan.’’
Ja’afaru Makarfi ya kara da cewa, “Wannan mataki da aka dauka na tabbata musulmi na yinsa ne da tsoron Allah ba tare da wani manufa ba. Kamata ya yi shugabanninsu su rika fada wa jama’arsu gaskiya a kan abubuwa da ke faruwa ba tare da son rai ba.’’
Game da ko za su nemi zama da kungiyar ta CAN domin wayar masu da kai, sai ya ce, “Eh toh, za mu yi kokari mu zauna da su domin tattauna batun da kuma nuna masu amfanun da ke tattare da shiga kawancen,” inji shi.
Ba mu gamsu da kawancen ba
– kungiyar CAN
Shi kuwa Sakataren kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna Rebrend Sunday Ibrahim, cewa ya yi, ‘’Abin da ya faru shi ne, ka san da farko shugaban kasa ya nuna kamar ziyarar da ya kai shi can kasar ba na shiga ko hada hannu da kasashen larabawa ba ne domin yakar ta’addanci. Amma daga baya sai labari ya zo inda ya shiga wannan kawance da su, wanda hakan ya janyo rashin yarda da shakku a zukatan mutane, musamman kiristoci.’’
“Gaskiyar zance a nan shi ne, idan ka dubi yadda abubuwa ke tafiya a kasar nan dole ne ka yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, idan aka lura da cewa an samu nasarori, musamman ta fannin yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram. Wannan ya sa jama’a ke ganin da a ce an yi amfani da irin wannan dagewa da tuni an gama da wannan matsala ta Boko Haram a kasar nan tun a shekarun baya. Amma da yake akwai cuta da rashin gaskiya da cin rashawa wanda ya yi katutu a zukatan wasu daga cikin manyan kasar nan, wanda hakan ya sa duk da kasancewar makudan kudaden da aka bayar domin sayen makamai saboda yaki da Boko Haram amma sai suka kwashe kudin suka je suna sayen gidaje da motoci a maimakon bada kudin wajen sayen makamai ga sojoji da sauran jami’an tsaro.Wannan mugun hali nasu yasa aka yi ta kashe mutane da sauran jama’a masu yawan gaske. Amma gwamnati ta yanzu ta yi matukar rawar gani wajen yaki da ‘yan ta’addan kasar nan.’’
“Saboda haka ne wasu daga cikin manyan shugabannin kirista suke ganin a maimakon a mayar da hankali wajen shiga kawance da wasu kasashe, kamata ya yi a mayar da hankali wajen cigaba da samun nasara a kan yaki da ta’addanci a cikin kasar nan. Wannan ina ganin shi ne dalilin da ya sa shugabanin kirista suka nuna shakku a kan kawancen.’’
Da aka tambaye shi, baya ganin kungiyoyi kamar su ISIS da sauransu a kasashen musulmi ake samunsu, sannan kuma ai ‘yan Boko Haram sun taba cewa sun hade da ISIS, sai ya ce. “ Ai da farko an sha fada mana cewa ‘yan Boko Haram ba musulmai ba ne, don me kuma a yanzu za a dawo a ce da mu wai akasarinsu musulmi ne? Wannan mu a gare mu wani zance ne da nake ganin akwai bukatar mu rika fada wa juna gaskiya.’’
Yaki da ta’addanci sai da taron dangi – Gwamnatin tarayya
Adam Umar, Abuja
Aminiya ta tuntubi Babban mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Malam Garba Shehu domin jin dalilin shigar Najeriya kawancen kasashen musulmi da za su yaki taaddanci inda ya yi bayani kamar haka:
Aminiya: mene ne dalilin shigar Najeriya kawancen kasashen musulmi da za su yaki ta’addanci?
Garba Shehu: Shi yaki da ta’addanci ya zama al’amari ne na duniya baki daya da ke bukatar hadin kai na gaba daya, babu wata kasa a duniya da za ta ware kanta a yanzu ta ce za ta yaki lamarin ita kadai komi karfinta sai dai ta hanyar taron dangi, saboda su ’yan ta’addan nan kodayaushe cewa suke yi ta’addancinsu bai san shinge a tsakanin kasa da kasa ba, suna kulla zumunci a tsakaninsu. Kuma bayanin da a kullum ake yadawa a duniya a yanzu, wanda ba lallai ba ne ya zama gaskiya, shi ne, ’yan ta’addan nan daga kasashen musulmi ne suke tasowa ko kuma suke da jagorori. To idan su ’yan ta’adda za su yi hulda a tsakaninsu, wane dalili ne gwamnatocin kasashensu ba za su yi hulda wajen yakarsu ba.? kuma kada a manta, su kungiyar Boko Haram da muke fama da su a kasar nan, su ne suka bude bakinsu suka ce sun kulla dangantaka da kungiyar ISIS da ke ta’addanci a Iraki da Siriya, wadanda ko a kwana biyu da suka gabata ‘yan ISIS din nan sun ce su ne suka kai hari a kasar Belgium da ke yankin Turai, inda aka rasa rayuka da dama. Kuma kafin Najeriya ta shiga cikin rukunin wadannan kasashe kowa ya san irin kokarin da shugaban kasa ya yi wajen kulla dangantaka a kan wannan fuska da kasashe makwabta don dakile zirga-zirgar wadannan mutane, to a yanzu idan aka fadada al’amarin ya kunshi hada gwiwa da wuraren da ake kyautata zaton ta can ne suke samun wasu daga cikin makamansu ko kuma kudade, ashe tamkar an shiga wani karin mataki ne bayan shiga na farko. Magana ta biyu ita ce, shi wannan al’amari na ta’addanci an daina dangantashi da kwaminisanci ko wata wariya ta jinsi, an koma ana danganta shi da musulunci ta ko’ina, ya shafi kasashen da ke da rinjayen musulmi, ya sahafi kasashen da musulmi ba su da yawa, kamar Turai ko’ina fama ake yi da shi, kuma duk inda ka ji bama-baman nan sun tashi sai ka ji an danganta shi da musulunci, gaskiya ne ko ba gaskiya ba. kasar Saudiyya wadda ke jagorancin wannan al’amari ita ta gayyaci Najeriya don a hada kai wajen bada bayanai, taimakon kudi, ko na makamai ga juna, ba lalle yaki na gaba da gaba kamar yadda wani zai yi tinani ba.
Aminiya: Fargabar masu korafin nan shi ne hakan na nunaa cewa Najeriya kasar Musulunci ne ke nan?
Garba Shehu: Ina ganin masu yawancin wannan kushe sun jahilci wannan al’amari, akwai kasashen da adadin musulmi a wajen bai da yawa, amma sun shiga wannan kungiya gabanin Najeriya ta shiga, misali shi ne makwabciyarmu jamhoriyar Benin ta shiga wannan kungiya gabanin Najeriya ta shiga, saboda sun ga amfanin hakan. Kuma gabanin shugaban kasa ya je kasar Saudiyya, ai ya amsa gayyayatar kungiyar kasashe 7 masu karfin arzikin masana’antu, inda suka nemi jin bukatun Najeriya tare da alkawarin tallafa mata a kai, wadannan kasashe dukkansu kasashe ne ba na musulmi ba. Idan Shugaban kasa bai kyamace su ba, wane dalili zai sa ya kyamaci wadannan kasashe wadanda ake danganta tushen al’amarin ta’addanci da yankunansu, bayan kuma su ne suka nemi wannan kawancen? kuma idan karbar taimako daga wajensu bai juya addininmu ba meye dalilin da yanzu za a ce na yanzu zai iya juyawa?
Aminiya: Akwai kuma masu fargabar hakan na iya karo wa Najeriya karin makiya, ma’amana dai kamar an tsokalo wani tsuliyar dodo ne?
Garba Shehu: karin karfi ne aka yi, kuma kar mu takaita wannan al’amari a kan fuskar tsaro kawai, alakar ya shafi sauran bangarori da ke da nasaba da tattalin arziki, wadannan kasashe irin su Saudiyya da katar da Hadaddiyar Daular Larabawa, wato inda Dubai take, kowa ya san matsayin da suka kai a duniya a yanzu, kasashe ne da ke da tarin dukiya a jibge wadda ba a amfani da ita, kuma a kullum neman wurare da za su zuba jari suke yi, mu kuma a gefe guda muna bukatar zuba jari da kuma tallafi, idan ka koma bangaren illar da ta’addancin nan ta yi mana kadai, muna bukatar sake tsugunar da al’ummarmu da suka rasa matsugunansu, wadanda ko a bayanin da shugaban kasa ya yi a kwanan nan adadinsu ya kai miliyan biyu, muna bukatar taimako daga duk ta inda zai zo, matukar bai saba ka’ida ba.
Babu laifi shiga kawancen yaki da ta’addanci -Jakada Sulaiman
Ibraheem Hamza Muhammad a Abuja
Jakada Sulaiman dahiru (OFR) tsohon Jakadan Najeriya ne a kasashen Brazil da Angola da Poland da Ibory Coast da Austireliya da Sudan da Pakistan. Ya ce ba laifi ba ne a shiga kawance don yaki da ta’adanci da kasashen musulmi ko na kirista.Kamar yadda ya bayyana wa Aminiya a wannan hirar:
Aminiya: Mene ne alfanun shigar Najeriya kawancen yaki da ta’adanci da kasar Saudiyya ke jagoranta?
Shigar Najeriya kawancen kasashen musulmi don yaki da ta’adanci ya dace matuka, sannan surutun da ake yi abu ne wanda bai dace ba. Don komai a Najeriya ana danganta shi da kabilanci ko addini, wanda ko kadan bai dace ba. Don kawai an ce an shiga kawance da kasashen musulmi ke jagoranta sai kawai mahawara ta barke? ai ba a ce lallai sai mutanene kasar sun zama musulmi ba. A sani cewa kasar Najeriya kasa ce da ba ta bin wani addini guda, sai dai an yarda da addinai biyu, watau addinin Musulunci da na Kirista. Na goyi bayan duk wani shiri da za a yi don dakile ta’addanci, shirin ko na musulunci ne ko kuma na kirista.
Aminiya: Shigar na ganin dama ne ko na tilastawa?
Wannan kawance ne na ganin dama, ba irin na Amurka ba wanda ta tilasta wa kasashe. Domin lokacin da Amurka ta shirya domin kai wa Iraki hari, Shugaban kasar na lokacin George Bush, ya ce “Ko kana tare da mu (Amurka) ko kuma kana tare da su (masu kai hari).”
Aminiya: Mene ne babban alfanunu wannan kawance ga Najeriya?
Wannan tsari na kasar Saudiyya na ganin dama ne. Najeriya ta shiga ne domin tana fama da ta’adanci. Ban ga wani abin damuwa ba da shigar Najeriya wannan hadaka. Ya kamata ne kungiyar kasashe rainon Ingila su yi jagorancin haka, amma kasashen da Faransa ta raina sun shiga hadakar, kamar Kamaru da kuma Mozambik wacce Potugal ta mulka, don neman ci gaban kasashensu. To haka ake yi a duniya, don kowa na neman abokai don a gudu tare a tsira tare.
Bai kamata a kawo bambancin harshe ko wani abu ga abin da zai amfani zaman lafiya a kasa ba. In da Najeriya ba za ta karu da shigan hadakar ba, ai da ba a shiga ba. Ta’adanci matsale ce da ta addabi kasashen duniya, don haka kasashen duniya ne za su hadu su yi maganin matsalar. Ko kasashen musulmi ne suka hada kai ko kuma kashashen kiristoci. kasar Ingila da Amurka ma sun nemi a taimaka musu a yakin duniya. A kasar Siriya, kasashen yamma ne, wanda yawancinsu kiristoci ne, suke yaki da kungiyar ISIS, amma kuma suna son kawar da mulkin Bashar Al-Assad ne. Wannan ba zai sa muce don su kirostoci ne sun fito ne don yaki da musulmi ko addinin Islama ba. A ganina duk abin da za a yi domin maganin ta’adanci ya dace. Maganganun da ake yi a Najeriya kan shiga wannan hadaka duk soki-burutsu ne. Shigar kasar ne bai maida kasar nan ta musulunci ba ko kadan. Idan Najeriay ta samu hadakar Musulmi ko na Kirista don magance wannan annoba za ta shiga. Su kuma wadannan ‘yan ta’adda ko wa suka yi karo da shi ko musulmi ko kirista ko mara addini, suna kashe kowa su lalata wurin addini da wurin sana’o’i da kasuwanni da sauransu.
Aminiya: ta fuskar diflomasiyya hakan ya dace?
Bai kamata ana surutu ba, domin a fannin diflomasiya wannan ya dace. Najeriya a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta sauya manufar Najeriya tun da aka samu ‘yancin mulkin kai, inda aka yarda a mara wa duk wata kasa da ake gallaza wa ba gaira-ba-sabar a duniya, amma Jonathan yace kar a jefa wa Palasdinu kuri’a domin Benyamin Natanyahu ya yi masa waya, haba wannan abin takaici ne matuka. Matsayin Najeriya na hulda da kasashen waje bai kamata ya sauya ba don wani mutum guda, domin Najeriay ta fi wani mutum guda ko wane ne shi.